Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/12/2024

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe Litinin - idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Dole Rasha ta amince da alhakin hatsarin jirgin saman Kazakhstan'

    Shugaban Azerbaijan ya ce dole Rasha ta amince tana da hakki a hatsatin jirgin saman ƙasar a Kazakhstan a ranar Laraba inda mutum 38 suka mutu.

    Mr Aliyev ya ce dole a hukunta waɗanda ke da hannu tare da biyan diyya ga Azerbaijan.

    Ya ce hujjoji sun tabbatar da girman ɓarnar da jirgin ya yi a cikinsa yayin da ya ratsa ta sararin samaniyar Rasha.

    A ranar Asabar Vladimir Putin ya kira shugaba Aliyeb inda ya nemi afuwarsa, amma bai amsa cewa Rasha ce ta harbo jirgin na fasinja ba.

  3. Hatsarin jirgi: An ayyana zaman makoki na mako ɗaya a Koriya ta Kudu

    Shugaban riko na Koriya Ta Kudu ya sanar da mako ɗaya na zaman makokin waɗanda suka mutu sakamakon hatsarin jirgin sama mafi muni da aka taɓa gani a ƙasar.

    A ranar Lahadi jirgin saman Jegu ɗauke da mutum 181 ya yi hatsari yayin da yake ƙoƙarin sauka inda kuma kusan ɗaukacin mutanen da ke ciki suka mutu.

    An yi nasarar ceto mutum biyu daga tarkacen jirgin.

    Hotunan bidiyo sun nuna yadda jirgin ke matsanancin gudu a titin saukarsa kafin ya daki gini wuta ta kama.

  4. Za a samu raguwar rashin tsaro a arewa maso yamma a 2025 - Sanata Yari

    Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, ya tabbatar da cewa za a samu raguwar rashin tsaro da ya dabaibaye Zamfara da kuma arewa maso yammacin Najeriya zuwa watan Oktoban, 2025.

    Sanata Yari ya bayyana haka ne yayin zantawa da manema labarai a garin mahaifarsa Talata-Mafara kamar yadda gidan talbijin na Channels ta ruwaito, inda ya ce gwamnatin tarayya na iya ƙoƙarinta wajen ganin ta daƙile ayyukan ƴan bindiga.

    Ya ce an tura ƙarin dakaru zuwa yankin domin kakkaɓe ƴan bindiga, musamman ma a jihar Zamfara.

    "A baya-bayan nan an tura sojoji da kuma makamai zuwa arewa maso yammacin Najeriya, saboda ganin cewa yankin na zama matattarar ƴan bindiga da kuma masu aikata laifi. Amma ina tabbatar muku da cewa kafin karshen watan Oktoban shekara mai zuwa, za a rage barazanar ɓata-garin," in ji Yari.

    Ya ce za a samu nasarar yin haka ne ganin irin maƙudan kuɗaɗe da shugaba Bola Tinubu ya ware wa ɓangaren tsaro a kasafin kuɗin baɗi, inda ya ce nan ba da jimawa ba matsalar tsaro za ta zama tarihi.

    Yari ya nuna ƙwarin gwiwar cewa ƙoƙarin da ake yi zai haifar da ɗa mai ido da kuma kawo sauki ga al'ummar Zamfara, musamman manoma waɗanda lamarin ya fi shafa.

    Ya tabbatar da cewa a damina mai zuwa, kowane manomi zai iya zuwa gonarsa ba tare da fargabar cewa za a kai masa hari ba.

    "Idan Allah ya yarda, yawancin manoma za su koma gonakinsu domin yin shuka a daminar baɗi," in ji Sanata Yari.

  5. An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati a Iran

    Rahotanni daga Iran sun ce an gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati kan yadda take tafiyar da tattalin arzikin kasar.

    Bidiyon da aka yaɗa a kafofin sadarwa na intanet wanda BBC ta tabbatar, ya nuna yadda ɗaruruwan ƴan kasuwa ke rufe shagunansu suna shiga zanga-zangar a birnin Bazaar.

    An ji suna yayata cewa ba su ci gaba da kasuwanci ba saboda taɓarɓarewar kuɗin ƙasar.

    Wannan na zuwa kuma bayan gargaɗin da hukumomin Iran suka yi cewa za su murkushe duk wata zanga-zanga.

  6. Gwamnatin Zamfara ta amince da 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta

    Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce daga yanzu ma'aikatan jihar za a fara biyan ma'aikatan jihar da sabon tsarin albashin.

    Ya kuma ce gwamna Dauda Lawal ya amince da ƙarin albashi ko kuma alawus na ƙarin wata ɗaya ga ma'aikata a faɗin jihar.

    "Wannan shi ne irinsa na farko a tarihin Zamfara, wanda kuma gwamna Dauda Lawal ya biya a cikin watan Disamba," in ji sanarwar.

    Kakakin gwamnan ya ce dukkan ma'aikatan jihar, ciki har da waɗanda suka yi ritaya za su samu kashi 30 na alawus.

    Gwamnan Dauda Lawal ya ce ya amince da albashi mafi ƙanƙantan da kuma alawus ne domin taimakawa ma'aikatan jihar a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara da kuma ƙara musu karfin gwiwa wajen aiki tukuru wajen kai jihar gaba.

  7. Zanga-zanga ta ɓarke a Iran don nuna adawa da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki

    Rahotonni daga Tehran, babban birnin Iran na cewa an samu ɓarkewar zanga-zanga a babbar kasuwar birnin domin nuna adawa kan yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arziki.

    Bidiyoyin da aka wallafa a shafukan sada zumunta kuma BBC ta tabbatar da sahihancinsu sun nuna ɗaruruwan 'yan kasuwa na rufe shagunansu domin shiga zanga-zangar a kasuwar - inda gwamnatin ƙasar ke da ƙarfi.

    Masu shagunan na furta wasu kalamai da ke nuna cewa ba za su ci gaba da kasuwanci ba sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar, wanda ya faɗi da kashi 25 cikin 100 a wata uku da suka gabata.

    Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da rundunar juyin-juya halin ƙasar ta fitar da sanarwar cewa a shirye suka su magance da duk wata tarzoma da za ta tashi.

  8. Za a ɗauki shekara uku ana rubuta sabon kundin mulkin Syria - al-Sharaa

    Sabon shugaban riƙo na ƙasar Syria ya ce ƙasar za ta kwashe shekara uku kafin rubuta sabon kundin tsarin mulki, sannan shekara huɗu kafin shirya zaɓe.

    Yayin wata hira da kafofofin yaɗa labaran Larabawa, Ahmad al-Sharaa ya ce za a shafe shekara guda kafin 'yan ƙasar suka ga wani sauyi na zahiri a ƙasar, bayan kifar da gwamnatin Bashar al-Assad.

    Ya ƙara da cewa zai soke ƙungiyarsa ta H-T-S da ta jagorancin kifar da gwamnatin Assad a taron tattaunawa na ƙasa da za a shirya nan gaba.

    Taron shi ne na farko da za a fara auna ko sabuwar gwamnatin za ta cimma alƙawuran da ta ɗaukar wa 'yan ƙasa na haɗa kan al'umma bayan shafe shekara 13 ana yaƙin basasa.

    Mista al-Sharaa ya sha cewa baya ganin kansa a matsayin wanda ya ceci ƙasar, yana haƙƙaƙe cewa 'yan ƙasa ne suka ceci kansu.

  9. Shugaban Azerbaijan ya zargi Rasha da ɓoye gaskiya kan hatsarin jirgi a Kazakhstan

    Shugaban ƙasar Azerbaijan ya zargi jami'an Rasha da ɓoye gaskiya kan abin da ya haifar da hatsarin jirgin saman ƙasar da ya auku ranar Laraba, a ƙasar Kazakhstan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 38.

    Ilham Aliyev ya ce an riƙa bayar da wasu dalilai waɗanda ba su kenan ba.

    Ya ce a bayyane take cewa jirgin ya faɗo ne bayan da aka harbo shi a sararin samaniyar Rasha a lokacin da yake ƙoƙarin sauka a Chechnya.

    A ranar Asabar ne shugaban Rasha, Vladimir Putin ya kira shugaba Aliyev domin neman afuwarsa kan abin da ya kira mummunan iftila'i.

    To amma bai bayyana ɗukar alhakin kakkaɓo jirgin ba.

  10. Labarai da dumi-dumi, Duka fasinjojin jirgin da ma'aikatansa huɗu sun mutu

    Rahotonnin da ke fitowa daga Koriya ta Kudu na cewa mutum 179 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman da ya auku a filin jirgin saman Muan ranar Lahadi da safe.

    Mutum biyu kawai aka samu cetowa daga hatsarin - waɗanda dukkansu ma'aikatan jirgin ne da aka zaƙulo daga cikin baraguzan jirgin.

    Hakan na nufin duka fasinjojin jirgin 175 haɗe da ma'aikatansa hudu sun mutu a hatsarin.

  11. Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ayyana makokin mako guda

    Gwamnatin ƙasar Koriya ta Kudu ayyana makokin kwana bakwai, domin jimamin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin sama.

    Za a sauko da tutocin ƙasar ƙasa-ƙasa, yayin da ma'aikatan gwamnati za su ɗaura baƙin ƙyalle a tufafinsu a tsawon kwanakin.

  12. Shugabannin duniya sun fara aikewa da saƙonnin jaje

    Shugabannin ƙasashen duniya sun soma aikewa da saƙonnin jaje ga gwamnatin Koriya da Kudu bisa hatsari jirgin saman da ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 177.

    Shugaban China, Xi Jinping na daga cikin mutanen da suka fara aikewa da ta'aziyyarsu ga iyalan mamatan.

    Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa a Telegram, Mista Xi ya ce ya kaɗu matuƙa da hatsarin jirgin.

    "A madadin gwamnati da al'ummar China, ina miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan mutanen da suka mutu, tare da fatan samun sauƙi da waɗanda suka samu raunuka'', kamar yadda ya wallafa.

    Shi ma sakataren wajen Birtaniya, David Lammy, ya ce labarin hatsarin jirgin ya tayar masa da hankali.

    Cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Mista Lammy ya jajanta wa mutanen ƙasar da na Thailand.

  13. Tarihin hatsarin jirgin sama a Koriya ta Kudu

    Yayin da muke kawo muku rahotonni kan hatsarin jirgin sama a filin sauka da tashin jirage na Muan, mun yi waiwaye kan tarihi hatsarin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

    • A 2002, wani jirgi ƙirar Boeing 767-200 mallakin kamfanin 'Air China' ya faɗi a wani tsauni da ke kusa da birnin Busan mai tashar jiragen ruwa. Hatsarin ya kashe mutum 129 tare da raunata 37.
    • A watan Satumban 1983, wani jirgin yaƙin Tarayyar Soviet ya harbo wani jirgin saman kamfanin 'Korean Airlines', bayan da ya shiga sararin samaniyar yankin Tarayyar Soviet a tsibirin Sakhalin, inda duka mutane 269 da ke cikin jirgin suka mutu.
    • Haka ma a 1997, wani jirgin sojin ƙasar ya faɗi a tsibirin Guam na yankin Pacific, inda mutum 228 daga cikin fasinjojin jirgin 254 suka mutu.
  14. 'Na'urar kula da filin jirgin ta buƙaci direban ya jinkirta sauka saboda tsuntsaye'

    Jami'an hukumar sufurin Koriya ta Kudu sun bayar da bayanai kan abin da ya faru da jirgin yayin da ya doshin filin sauka.

    • Da farko jirgin ya yi yunƙurin sauka, amma sai na'urar da ke kula da filin jirgin ta aike masa saƙon ya jinkirta sakamakon tsuntsaye da ke shawagi a titin da zai sauka.
    • Minti biyu bayan gargaɗin da aka aike wa jirgin, sai direban ya yi kiran gaggawa ga na'urar kula da filin, wanda ta ba shi damar sauka, amma ta ɗaya gefen.

    Nan take direban ya amince ya kuma sauke jirgin.

    Bidiyon saukar jirgin ya nuna yadda ya sauka ba tare da tayoyi ko wani abu da ke taimaka wa saukar jirgi ba, lamarin da ya sa ya kauce wa hanyar har ya je ya bugi wani gini kafin ya kama da wuta.

    Ma'aikatar sufurin ƙasar ta ce direban jirgin ya jima yana tuƙin jirgin sama tun 2019, yayin da ya shafe fiye da sa'o'i 9,800 yan tuƙa jirgin sama.

  15. An gano na'urar adana bayanin jirgin

    Ma'aikatar sufurin Koriya ta Kudu ta ce an gano na'urar adana bayanan jirgin saman da ya yi hatsari a ƙasar.

    Kawo yanzu dai ba a san musabbabin hatsarin jirgin ba, yayin da ake ci gaba da bincike.

    Adadin mutanen da suka mutu ya zuwa yanzu ya kai 176.

    Bayanan da jami'an hukumar kashe gobara ta ƙasar suka bayar sun ce tsuntsaye ne suka sabbaba hatsarin.

  16. Hatsarin jirgin Koriya ta Kudu: Adadin wadanda suka mutu ya kai 176

    Hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta aƙalla mutum 176 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman ƙasar bayan da wani jirgin saman fasinja ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

  17. Shugabar Georgia mai barin gado ta ƙi sauka daga muƙaminta duk da rantsar da sabo

    An rantsar da sabon shugaban ƙasar Georgia, Mikheil Kavelashvili, a daidai lokacin da ake zanga-zanga a Tbilisi babban birnin ƙasar.

    A wani jawabin nuna rashin amincewa da wadda ya gada - Salome Zourabichvili - ta yi, ta ƙi sauka daga muƙamin, to amm ta fice daga fadar shugaban ƙasar.

    Majalisar dokokin ƙasar - wadda jam'iyyarsa ta fi rinjaye ce ta zaɓi mista Kavelashvili, a matsayin shugaban ƙasar, a kwanakin da suka gabata

    Ms Zourabichvili ta ce zaɓen nasa ya saɓa wa ƙa'ida, kasancewar zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar cikin watan Oktoba na cike da kura-kurai.

    An gudanar da bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, bayan shafe makonni ana zanga-zangar adawa da jam'iyyar Dream Party ta Georgian, wadda 'yan adawa ke ganin ta ƙara samun ƙarfin iko da kuma adawa da EU.

  18. Hotunan iyalai da masu aikin ceto a wurin da lamarin ya faru

    Iyalai da dama sun shiga alhini sakamakon hatsarin jirgin sama da ya rusta da 'yan'uwansu a Koriya ta Kudu.

    Hatsarin - wanda ya auku a fiin jirgin saman Muan - ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 166.

    Ga hotunan wasu iyalai da suka taru a wajen filin jirgin yayin da suke cikin alhinin rashin 'yan'uwansu.

  19. Bidiyon jirgin a lokacin hatsarin

    Jirgin ya sauka ne a filin jirgin kafin ya kauce wa titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.

    Masu aikin ceto na ci gaba da ceto mutanen da lamarin ya rutsa da su.

    Hukumar kashe gobara ta ƙasar ta ce aƙalla mutum 1671 ne suka mutu a hatsarin.

  20. Hatsarin jirgin Koriya ta Kudu: Adadin mutanen da suka mutu ya kai 151

    Hukumar kashe gobara ta Koriya ta Kudu ta aƙalla mutum 151 ne suka mutu a hatsarin jirgin saman ƙasar bayan da wani jirgin saman fasinja ya kauce daga titinsa yayin da yake sauka a filin jirgin sama a Koriya ta Kudu.

    Hukumar kashe gobarar ta ce daga cikin wadanda suka mutu 71 maza ne, mamat 71 , yayain da suka kasa tantance jinsi gawawaki huɗu sakamakon ƙonewar da suka yi.

    Jirgin dai na ɗauke da mutum 181, ciki har da ma'aikatansa shida a lokacin da hatsarin ya auku.

    Jami'an agaji sun ceto ma'aikatan jirgin biyu, bayan faruwar lamarin.

    Jirgin kirar Boeing 7-3-7 ya sauka, bayan dawowa gida daga Bangkok na ƙasar Thailand.

    Saukar tasa ke da wuya ne ya kwace ya saki titinsa ya kutsa ta cikin wani gini, kana ya kama da wuta.

    Shaidu sun ce sun ji karar fashewar wani abu mai karfi bayan faruwar lamarin.