Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Usman Minjibir

  1. Yaƙin Ukraine: Amurka da Rasha za su fara tattaunawa yau a Saudiyya

    Lavrov na Rasha

    Asalin hoton, Reuters

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya sauka a Saudiyya domin jagorantar tattaunawa da tawagar wakilan Rasha a yau Talata.

    Hakan na zuwa ne ƙasa da mako ɗaya da Donald Trump ya yi magana da Shugaba Putin na Rasha ta waya.

    Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, shi ne ke jagorantar tawagar wakilan Rasha.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce tattaunawar ce za ta ba da haske kan ko da gaske Rashar take wajen kawo ƙarshen yaƙinta da Ukraine.

    Wakilin BBC ya ce Shugaba Zelensky ya ce bai san komai kan tattaunawar ba tsakanin Amurka da Rasha, saboda haka Ukraine ba za ta amince da duk wata yarjejeniyar da za a cim ma ba tare da an saka ta ciki ba.

  2. Babu fasinjan da ya mutu bayan jirgin sama ya hantsila a Canada

    Hatsarin jirgi

    Asalin hoton, EPA

    Wani jirgin sama mallakin kamfanin Delta Airlines na Amurka ya yi hatsari tare da kifewa a filin jirgi na Toronto a kasar Canada.

    Hotunan da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda dusar ƙanƙara ta rufe jirgin.

    Wakilin BBC ya ce wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar ta ce dukkan fasinjoji 80 da ke cikin jirgin sun tsira, yayin da mutum uku - ciki har da ƙaramin yaro - ke tsananin jin jiki.

  3. Barka

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a yau Talata.

    Za mu kawo muku rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar, da kuma maƙwabtansu.

    Ni ne Umar Mikail zan jagoranci kawo rahotonnin bisa kulawar Usman Minjibir.

    Mu je zuwa!