Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/01/2025

Taƙaitattu

  • Roma na son Casmero, Napoli da Juventus na son Hojlund
  • ECOWAS za ta ci gaba da ma'amala da ƙasashen sahel da suka fice daga cikinta
  • Amurka ta buƙaci Rwanda da ta tabbatar da tsagaita wuta a Jumhuriyar Congo
  • 'Ba za mu daina ƙera makaman nukiliya ba - Kim Jong Un
  • Boniface na shirin haɗewa da Ronaldo a Al-Nassr
  • Fursunoni sun tsere daga gidan yari a Jumhuriyar Congo
  • An sami hargitsi a taron kwamitin amintattu na jamiyyar PDP
  • Me ya sa El Rufa'i ke jan zare da jam'iyyar APC?
  • Alamu na nuna cewa Rwanda ke goyon bayan mayaƙan M23 - MDD
  • Najeriya ta ciyo bashin dala biliyan 1.1 don samar da wutar lantarki – Tinubu
  • Kamfanin Max Air ya yi bayani kan hatsarin da jinginsa ya yi a Kano

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ibrahim Yusuf Mohammed da Aisha Aliyu Ja'afar

Buɗewa

Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba.

Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.