Rufewa
Masu bin shafin namu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotoonin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa da sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/01/2025
Usman Minjibir da Ibrahim Yusuf Mohammed da Aisha Aliyu Ja'afar
Masu bin shafin namu a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotoonin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa da sabbin labarai.
Amma kafin nan muke cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Bring Them Home Now
Ofishin Firaiministan Isra'ila ya ce Hamas ta tabbatar da cewa Arbel Yehud na cikin mutanen da za ta saki a gobe Alhamis.
Tun ranar Asabar aka yi tsammanin Hamas za ta saki Yehud.
Rashin sakin ta ya sanya Isra'ila ta dakatar da Falasɗinawa komawa Arewacin Gaza.
Sai dai bayan samun tabbacin tana raye cikin ƙoshin lafiya daga Hamas ɗin, ya sanya Isra'ilar ta bai wa dubban Falasɗinawa damar komawa gidajensu.
Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin Isra'ila za su zauna a sansanin 'yan gudun hijira na Jenin da ke Gaɓar Yamma da kogin Jordan bayan kammala farmakin da suke kaiwa a yankin yanzu.
Isra'il Katz na wannan jawabi ne daga sansanin a rana ta takwas da suke aikin tsaro da jirage masu saukar ungulu da tankokin yaƙi da kuma jirage marasa matuƙa.
Jami'an Falasɗinawa sun ce an kashe Falasdinawa 17 tare da an rushe gidaje da dama tare da tilasta wa yawancin fararen hula tserewa.
Kafin farmakin da Isra'ila ta kai, sojojin hukumar Falasɗinawa suna fafatawa da mayaƙan Hamas tsawon makwonni.

Asalin hoton, Ikorodu fc Twitter
Ikorodu City ta doke Kano Pillars 4-1 a wasan mako na 20 a gasar Premier ta Najeriya da suka kara ranar Laraba a Legas.
Ikorodu City ta fara cin ƙwallo a minti na biyu da take leda ta hannun Adelani Shola, sannan ta kara na biyu ta hannun Uzondu Harrison a minti na 27.
Daf da za su je hutu ne Pillars ta zare ɗaya ta hannun Abba Adam, kuma na huɗu da ya zura a raga a kakar nan.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne mai masaukin baƙi ta kara na uku, bayan da Pillars ta ci gida a kwana daga Harrison Austin, sannan Ayomide Cole ya ci na huɗu.
Tun a ranar Talata da sanyin safiya Pillars ta ziyarci Legas a jirgin sama a karon farko da gwamnati ta yi wannan bajintar a kakar nan.
Ta kuma yi haka ne domin ƴan wasa su samu natsuwa da hutun da suke bukata, domin buga wasa da Ikorodu, sannan su koma Kano a kan kari don fuskantar wani kalubale ranar Lahadi.
Ranar 8 ga watan Satumba, Pillars ta caskara Ikorodu City 3-0 a wasan farko na fara kakar bana da suka fafata a filin wasa na Muhammadu Dikko a jihar Katsina.
Ranar Lahadi 2 ga watan Fabrairu, Kano Pillars za ta karɓi bakuncin Bayelsa United, ita kuwa Ikorodu City za ta je Enugu Rangers.

Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Adadin mutanen da suka mutu a wurin turmutsitsin bikin addinin ya kai 30.
Bikin Kumbh Mela, da ake gudanarwa bayan kowace shekara 12 ya kasance babban taron addinin Hindu a faɗin duniya.
Taron bikin - wanda aka kwashe fiye da mako shida ana yi, ya ɗauki hankalin miliyoyin mutanen duniya.
Turmutsitsin ya auku ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na daren ranar Laraba, a lokacin da wani gungun masu ziyarar ibada suka karya shingen da masu ziyarar ke tsayuwa kafin su yi wanka a kududdufi.
Masu ibadar sun yi imanin cewa wanka a kogin kan wanke zunubi tare da samun yafiya.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ƙasar ta fitar, ta ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 30, yayin da wasu 60 suka jikkata.
Duk da da wannan turmutsitsi, wasu masu ibadar sun ce za su ci gaba da bikin ibadar domin ci gaba da wanka a kududdufin.
Aƙalla mutum miliyan 50 ne suka yi wanka a kududdufin a yau Laraba, inda kawo yanzu waɗanda suka yi wanka a kududdufin ya kai mutum miliyan 249.8 tun farkon fara bikin.
Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya aike da saƙon ta'aziyya ga iyalan sojojin ƙasar 13 da aka kashe a DR Kongo.
Cikin wata sanarwa da shugaban ya fitar kan halin da ake ciki a DR Kongo, Mista Ramaphosa ya ce rundunar sojin ƙasar, na aiki don tabbatar da ''samar wa dakarun ƙasar da taimakon da suke buƙata.''
Ya ɗora alhakin mutuwar sojojin kan hare-haren ƙungiyar 'yantawayen M23 da kuma dakarun Rwanda da suke kai wa dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar SADC ta ƙasashen yankin kudancin Afirka.
Hare-haren sun kuma kashe wasu sojojin ƙasashen Malawi da Tanzaniya.
A makon nan ana ci gaba da gwabza fada a birnin Goma na DR Kongo, inda 'yantawayen M23 suka ƙwace mafi yawan sassan birnin.

Asalin hoton, Getty Images
An kama mutum 10 da aka zarga da mallakar wata babbar ƙungiyar da ke fasa-ƙwaurin taba sigari a Turai.
An fara binciken ne bayan wata kwantena cike da taba ta isa Belgium maimakon ta nufi Jamus ɗauke da kayan gini.
Masu binciken laifuka a Belgium da Netherlands da Jamus sun bankaɗo yadda ake amfani da wannan hanya wajen shigar da kwantena sama da 150 cike da sigari cikin Turai.
An yi tabar ne a ƙasashen Turkiyya da Iran kuma ana amfani da tashar jiragen ruwan Tarayyar Turai wajen shigar da tabar ƙasashen ta hanyar amfani da takardun fito na bogi.

Asalin hoton, Max Air
Gwamnatin Najeriya ta hannun Hukumar kula da sufurin jragen sama ta ƙasar (NCAA) ta sanar da dakatar da ayyukan kamfanin jirgin sama na Max Air, bayan jirgin kamfanin ya yi hatsari a daren jiya Talata a jihar Kano.
Daraktan hulɗa da jama'a da kare haƙƙin abokan hulɗa na hukumar, Michael Achimugu - wanda ya fitar da sanarwar - ya ce dakatarwar za ta soma aiki ne a daren 31 ga watan Janairun 2025, domin bai wa hukumomin kamfanin damar tattance ayyukanta a cikin gida da ya haɗa da bincike kan kamfanin, ma'aikatansa, tsarin aikinsa da jiragensa, da kuma tattalin arziƙin kamfanin.
Achimugu ya kuma ce tuni hukumar tabbatar da kariya (NSIB) ta ƙaddamar da bincike kan musabbabin haɗarin na baya-bayan nan.
Jirgin Max Air samfurin B734 mai lambar rijista 5N-MBD, ya yi haɗari ne a yayin sauka a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano bayan tayarsa ta fashe a jiya Talata.
Duk da dai fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun fita lafiya, hukumar kula da filayen jiragen sama ta ƙasar (FAAN) ta rufe filin jirgin na wucin-gadi kafin buɗe shi a safiyar ranar Laraba.
Wannan ne karo na uku da ake samun haɗarin jirgin na Max Air a cikin wata uku.

Asalin hoton, Reuters/Yonhap
Aƙalla mutane 20 ne aka tabbatar sun mutu bayan wani haɗarin jirgin sama a jihar Unity da ke Sudan ta Kudu.
A cewar wani rahoton gidan radio Miraya na tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar, jirgin ya yi haɗarin ne bayan ya tashi daga wata rijiyar mai a Unity a hanyarsa ta zuwa babban birnin ƙasar Juba.
Fasinjoji 21 da ma'aikatan jirgin ne ke ciki a lokacin da yayi haɗarin.
Rahotannin sun tabbatar da cewa matuƙin jirgin saman ya mutu, yayin da wanda ke raye a cikinsu ke cikin mayuwacin hali.

Asalin hoton, PDP
An sami wani hargitsi a babbar sakatariyar jam'iyyar adawa ta PDP da ke Abuja a ranar Laraba lokacin da mabiyan Samuel Anyanwu da na Udeh Okoye waɗanda ke rikici kan matsayin sakataren jamiyyar ta ƙasa, suka yi arangama a yayin taron kwamitin amintattu.
Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa rikicin ya soma ne bayan wasu da ake zargin ƴan daba ne sun tilasta wa Udeh Okoye fita daga cikin taron wanda ya kai ga ce-ce-kuce.
A cewar rahotan tuni aka jibge jami'an tsaro da suka haɗa da ƴan sanda, da sojoji, da jam'ian tsaron farin kaya na DSS, a sakatariyar domin tabbatar da tsaro.
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP wadda ke ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida, ta kira taron kwamitin amintattu a yau domin shawo kan matsalolin da suka raba jami'iyyar gida biyu.
Rikici kan matsayin sakataren Jamiyyar ya soma ne bayan Anyanwu ya bar matsayin domin takara a zaɓen jihar Imo wanda yayi rashin nasara.
Bayan tafiyarsa, masu ruwa da tsaki na jamiyyar a kudu maso gabashin Najeriya suka amince da Ude -Okoye a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Sai dai bayan rashin nasarar nasa, yayi ƙoƙarin dawowa kujerarsa wanda hakan ya ƙara jefa jamiyyar cikin rikici.

Asalin hoton, Onanuga/El Rufa'i/X
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i, a karon farko ya caccaki jam'iyyar APC a bainar jama'a inda ya bayyana jam'iyyar APC mai mulki da wadda ta "sauka daga aƙidun dimkoraɗiyya da aka kafa ta a kai".
El Rufa'i dai ya bayyana hakan yayin gabatar da jawabi a wani taron da aka shirya kan hanyoyin ciyar da dimokraɗiyya gaba a Najeriya, da aka gudanar a Abuja.
Wannan ne kuma ya janyo zazzafar martani daga jam'iyyar APC mai mulki da ma ɓangaren fadar shugaban ƙasa.
Za dai a iya cewa wannan ne karon farko da tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya fara fitowa fili ya soki salon kamun ludayin jam'iyyar APC, tun bayan da majalisar dokokin ƙasar ta gaza tantance shi a matsayin minista a Najeriya.

Asalin hoton, EPA
Masu zanga-zanga a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, na ci gaba da ƙona hotunan shugaban ƙasar Rwanda tare da kekketa tutocin ƙasar a daidai lokacin da ƴan tawayen M23 suka karɓe iko da galibin birnin Goma da ke gabashin ƙasar.
Bacin ransu ya karkata ne kan shugaban ƙasar Rwanda Paul Kagame, wanda suke zargin yana marawa ƴan tawayen baya - zargin da MDD ta dade tana yi.
A zahiri, tawagar ƙwararrun Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da cewa sojojin Rwanda ke kula da ayyukan M23, ta kuma ba da cikakken bayani kan yadda sojojin Rwanda ke horar da ƴan M23 da aka ɗauka da kuma yadda ƙungiyar ke samun goyon bayan manyan makamai daga Rwanda.
Goma, wanda ke kusa da wani dutse mai aman wuta a gefen tafkin Kivu, yana kan iyaka da Rwanda. Shi ne babban birnin lardin Kivu ta Arewa mai arzikin ma'adinai - kuma muhimmin cibiyar kasuwanci ya kuma kasance babbar matattara ta tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD.
Tun lokacin da aka fara rikicin, shugaba Kagame ya sha musanta cewa yana da hannu wajen goyon bayan ƴan tawayen M23, waɗanda suke da kayan aiki da makamai su ke kuma samun ingantaccen horo.

Asalin hoton, Tinubu/X
Najeriya ta karɓo rancen dala biliyan 1.1 daga bankin raya Afirka (AfDB) don samar da wutar lantarki ga mutane miliyan 5 daga yanzu zuwa ƙarshen shekarar 2026.
A cewar Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan a cikin jawabin da Adebayo Adelabu, ministan wutar lantarki, ya gabatar, a taron da aka kammala na kwanaki biyu na inganta ɓangaren makamashi na Afirka a Dar es. Salaam, babban birnin ƙasar Tanzania.
Tinubu ya kuma bayyana cewa za a yi amfani da dala miliyan 200 na AfDB domin samar da wutar lantarki ga mutane 500,000 a ƙarshen shekarar 2025.
"Wannan babban buri ne, amma za mu iya cimma shi tare," in ji Tinubu.
"A matsayina na shugaban Najeriya, na himmatu wajen ba aiwatar da aikin samar da makamashi, kuma mun ba da babban fifiko."
Ya ƙara da cewa “Kamar yadda muka sani, Afirka na da wadatar albarkatun makamashi, amma har yanzu miliyoyin ƴan nahiyar mu ba sa samun ingantaccen makamashi mai araha.''
Shugaba Tinubu kuma jinjinawa Ajay Banga, shugaban bankin duniya, da Akinwunmi Adesina na AfDB saboda hangen nesan su na kawo sauyi, wanda ya ce "zai haskaka da kuma karfafa Afirka."

Asalin hoton, Max Air
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Max Air ya tabbatar a hukumance cewa ɗaya daga cikin jiragensa ya yi hatsari a lokacin da ya zo sauka a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da yammacin ranar Talata.
Wannan lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:57 na dare, bayan da jirgin da ya taso daga Legas ya sami tangarɗa a tayoyinsa na gaba a lokacin da ya ke shirin sauka.
Ba a dai samu rahoton rasa rai ko jikkata a hatsarin ba.
"Muna so mu sanar da jama'a cewa ɗaya daga cikin jiragenmu ya samu matsala yayin da ya ke ƙoƙarin sauka a Kano da yammacin jiya," in ji Max Air a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba.
Kamfanin ya ce titin saukan jirgi na filin jirgin saman Kano zai ci gaba da zama a rufe na wani ɗan lokaci yayin da ake tabbatar da cewa an kawar da duk tarkace, wanda hakan na iya haifar da tsaiko a ayyukan sufurin jirgi a ranar Laraba.
Ya yanzu dai hukumar binciken hatsarin jiragen sama ta Najeriya (NSIB) ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance game da lamarin ba.
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin wata guda da jirgin kamfanin Max Air zai yi saukar gaggawa a ƙasar.

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla mutane 12v ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka sakamakon turmutsitsi a wani gagarumin biki na addinin Hindu a arewacin Indiya.
Hatsarin ya afku ne a bikin Kumbh Mela lokacin da wasu da suka je wanka a cikin ruwa mai tsarki suka tattake mutanen da suke barci a bakin kogi a Prayagraj.
An ga jami’an bayar da agajin gaggawa suna kwashe gawarwaki a kan gadajen ɗaukar maras lafiya.
Firaminista Narendra Modi da ministocin tarayya ciki har da Ministan harkokin cikin gida Amit Shah sun yi ta'aziyya ga waɗanda suka mutu sakamakon turmutsistin.
Sai dai gwamnatin Uttar Pradesh ƙarƙashin jam'iyyar Bharatiya Janata Party (BJP) Yogi Adityanath, ta yi shiru kan adadin waɗanda suka mutu.
Sai dai sun ce mutane da dama sun samu raunuka, har yanzu hukumomin yankin ba su fitar da adadin matattun a hukumance ba.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, ECOWAS
Hedikwatar gudanarwa ta hukumar ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta ce ta yi wani shri da zai saukaka tattaunawa da ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da ke karkashin jagorancin mulkin soji da suka fice daga ƙungiyar a hukumance ranar 29 ga wannan watan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a safiyar ranar Laraba, Hukumar ta ce tana shirin kaucewa ruɗani da hargitsi a cikin rayuwa da kasuwancin mutanen da ke kasashen ECOWAS da kuma waɗanda ke yankin Sahel, a lokacin da ɓangarorin biyu ke raba gari.
"Ficewar Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar daga ECOWAS ya fara aiki daga yau 29 ga watan Janairu 2025. Duk da haka, a cikin mutunta zamantakewa da inganta haɗin kai a yankin da kuma muradun jama'a. Hukumar ECOWAS ta bukaci dukkan hukumomin da abin ya shafa a ciki da wajen ƙasashen ƙungiyar ta ECOWAS da su ƙyale ƴan ƙasashen uku su ci gaba da cin gajiyar ƴancin shige da fice ba tare da buƙatar biza ba, da daman zama a cikin ƙasashe kamar yadda ka’idojin ECOWAS suka tanada na tsawon wani lokaci.” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa ECOWAS za ta ci gaba da amincewa da takardun tafiye-tafiye da katin shaida mai ɗauke da tambarin kungiyar ECOWAS da ke hannun ƴan ƙasashen Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar har sai an sanar da hakan; sannan a ci gaba da mutunta kayayyaki da ayyukan da ke fitowa daga ƙasashen uku bisa tsarin kasuwanci manufofin saka hannun jari na ECOWAS.
Hukumar ta yi nuni da cewa, za a gudanar da wadannan tsare-tsaren har sai majalisar shugabannin ƙasashen ECOWAS ta kammala tantance hanyoyin da za a ci gaba da hulɗa da ƙasashen uku nan gaba.
Kungiyar ECOWAS ta ce ƙasashen na Sahel na da wa’adin watanni shida da zai ƙare a watan Yuli, domin sake duba matsayinsu, ko da za su sauya ra'ayi kan ficewa daga ƙungiyar.

Asalin hoton, Getty Images
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya yi kira ga shugaba Paul Kagame na Rwanda ya tabbatar an gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo. '
Ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, sun kusan kama ikon daukacin birnin kasar Goma.
Ita ma ministar harkokin wajen Congo Theresa Kayikwamba ta yi kira ga kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya taimaka kawo ƙarshen rikicin.
Ta ce miliyoyin mutane sun rasa muhallansu, dubbai sun makale a birnin Goma da aka yi wa kawanya, su na fama da rashin ruwan sha da abinci da kuma tsaro, an kuma kashe daruruwa a ɗan tsakanin nan.

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani.
Kafar yada labaran ƙasar ta rawaito Mr Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matuƙar muhimmanci a tsarin da ƙasar ke yi na ƙarfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk ƙasashen da suka nemi tsoma baki a harkar ƙasarsa.
Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama aiki.
A ɓangare guda kuma Mr Trump ya ce zai sabunta hulɗar da ke tsakaninsa da shugaban na Koriya ta Arewa.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni daga Jamus sun tabbatar da cewa ƙungiyar Al-Nassr ta cimma cikakkiyar yarjejeniya da Bayer Leverkusen domin ɗaukar ɗan wasan Najeriya Victor Boniface.
Rahotannin dai na cewa albashin ɗan wasan mai shekara 24 zai iya kai wa Yuro miliyan 15 a duk kakar wasa.
Tuni dai ɗan wasan ya kammala gwajin duba ƙoshin lafiyarsa a kulob ɗin na Saudi Pro League.
Ɗan wasan ya taka rawar gani a kakar wasan da ta gabata, inda ya taimakawa Leverkusen ta lashe gasar Bundesliga, da kofin Jamus, da kuma Super Cup na Jamus,
A wannan kakar, ya buga wasanni 34, inda ya zura ƙwallaye 21 ya taimaka aka ci 10.
Rashin halartar atisayen Leverkusen da Boniface ya yi a ranar Talata ya kara rura wutar raɗe-raɗin tafiyar tasa.
Da yake magana da manema labarai, kocin Leverkusen Xabi Alonso ya amince da tattaunawar sauya sheƙar ɗan wasan da ke gudana kuma ya tabbatar da cewa shirye-shiryen ƙungiyar na wasan ƙarshe a zagayen rukuni na gasar cin kofin zakarun Turai na ci gaba da gudana ba tare da Boniface ba.

Asalin hoton, AFP
An samu labarin tserewan fursunoni daga wani gidan yari da ke garin Goma a yankin gabashin Jumhuriyar Dimokradiyar Kongo, yayin da rikici ke ƙara ƙamari tsakanin ƴan tawayen M23 da dakarun sojin ƙasar.
Bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna mutanen da ake kyautata zaton fursunoni ne a titunan birnin, sa'o'i kaɗan bayan da mayaƙan ƙungiyar M23 masu ɗauke da makamai da sojojin Rwanda suka shiga babban birnin lardin Kivu ta Arewa.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa an yi tashe-tashen hankula a gidan yari da safiyar ranar Litinin wanda hakan ya yi sanadiyar tserewar fursunonin.
Rahotanni dai na bayyana cewa ƴan tawayen na daf da karɓe iko da Goma da ake cewa sun ƙwace filin saukar jirgin sama.
Gwamnatin Kongo dai ta dage cewa tana samun galaba yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a wasu sassan birnin.
Ana zargin ƙasar Rwanda da marawa ƙungiyar Tutsi ta M23 baya a yayin da take ci gaba kai hare-hare cikin ƴan watannin nan a faɗin yankin mai arzikin ma'adinai.
Rwanda ta sha musanta wannan zargi.