Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 23/10/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai tsaye - 23/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Gwamnatin Najeriya za ta hukunta jihohin da suka ƙi zaɓen ƙananan hukumomi

    Shugaba Bola Ahmed Tinubu

    Asalin hoton, TINUBU X

    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta ɗauki mataki a kan jihohin da suka ƙi gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da zai tabbatar da cin gashin kai na ƙananan hukumomin kamar yadda kotun ƙolin ta zartar.

    Babban lauyin gwamnatin tarayyar Mista Lateef Fagbemi, wanda ya bayyana hakan a jihar Ekiti a jiya Talata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ya ce ba gudu ba ja da baya a kan shirin aiwatar da hukuncin kotun ƙolin kan cin gashin ƙananan hukumomin.

    Mista Fagbemi ya ce gwamnatin za ta yi nazarin dokokin jihohi a kan zaɓen ƙananan hukumomi tare da duba dalilin da ya sa wasu jihohinke jinkirin gudanar da zaɓen.

    Bayanai sun nuna cewa a yanzu sama da ƙananan hukumomi 164 ne a jihohi takwas ba su yi zaben ba.

    Jaridar ta kuma ruwaito cewa, wasu rahotanni na nuna cewa wataƙila Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar da hukuncin kotun ƙolin a kan cin gashin kai na ƙananan hukumomi nan da ƙarshen watan nan na Oktoba.

    Hakan na nufin gwamnatin tarayyar za ta iya riƙe kason kuɗin ƙananan hukumomin da ba a yi zaɓe ba, kamar yadda hukuncin kotun ya ayyana.

    Ƙananan hukumomin da ba a yi zaɓe ba na jihohin Katsina da Zamfara da NasarawaOndo, da Osun da Ogun da Cross Rivers.

    Hukuncin kotun ya nuna cewa, saɓa doka ne gwamnonin jihohi su ci gaba da karɓa ko riƙe kason kuɗaɗen ƙananan hukumomi a ƙarƙashin asusun haɗin gwiwa na jida da ƙananan hukumomi.

    Wasu gwamnonin jihohin ƙasar dai na ganin wallen hukuncin kotun.

    A makon da ya wuce gwamnan jihar Anambra Farfesa Chukuma Soludo, a lokacin sanya hannu kan dokar mulkin ƙananan hukumomi ya yi gargaɗin cewa ba wa ƙananan hukumomin ƙasar 774 cikakken ƴancin cin gashin kai ka iya haifar da abin da ya kira ''gagarumar matsala'' ta yarda za a kasa samar da cigaba mai ɗorewa.

  2. 'Yan cirani biyu sun mutu bayan kifewar jirginsu a ruwan Ingila

    Mutum biyu sun mutu bayan wani jirgin 'yan cirani ya kife a ruwan Ingila da ke kusa da tafkin Calais a yau Laraba.

    Hukumomin kula da gaɓar ruwa na Faransa sun ce an ceto mutum 46 da ransu kuma ana ci gaba da neman wasu.

    Tuni mai shigar da ƙara ya ƙaddamar da bincike.

    Lamarin na faruwa ne bayan wani jariri ya mutu yayin da wani jirgin ya kife lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka ruwan na Ingila ranar Alhamis.

  3. Najeriya ta hana fitar da gas ɗin girki ƙasashen waje

    Gas

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta hana fitar da gas ɗin girki zuwa ƙasashen waje, daga ranar 1 ga watan Nuwamba mai kamawa, a wani mataki da ta ce ta ɗauka domin hana hauhawara farashin gas ɗin.

    Ƙaramin ministan albarkatun mai mai kula da harkokin gas, Ekperikpe Ekpo, ne ya bayyana haka, a cikin irin matakan da ya ce gwamnati ta ɗauka domin tabbatar da saukinsa.

    Ministan ya nuna damuwarsa kan yadda farashin gas ɗin ke ta hauhawa a baya-bayan nan daga tsakanin naira 1,100 da 1,250 zuwa naira 1,500 a kan kilo ɗaya.

    A kan hakan ministan ya yi taro da masu ruwa da tsaki a kan gas ɗin a Abuja ranar Talata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, domin lalubo hanyoyin magance matsalar hauhawara farashin, wadda ke damun 'yan ƙasar.

    A nan ne ministan ya sanar da cewa daga cikin muhimman matakan da aka ɗauka sun haɗa da umartar kamfanin mai na ƙasar NNPCL da masu samar da gas ɗin na cikin ƙasa da su daina fitar da gas ɗin da aka samar a ƙasar zuwa waje.

    Ekpo ya jaddada buƙatar ganin an samar da wani tartibin tsari na tsayar da farashin gas ɗin wanda zai dace da cikin gida.

    A wata sanarwa da kakakin ministan, Louis Ibah, ya fitar ya ce an bai wa hukumomin da ke aikin hakowa da sayar da albarkatun mai na ƙasar da su fitar da wani tartibin tsarin farashin gas ɗin na cikin gida nan da kawana 90.

  4. Sojojin Najeriya biyar sun mutu a haɗarin mota a jihar Filato

    Wajen wani ha

    Asalin hoton, Channels TV

    Wasu sojojin sama na Najeriya biyar na daga cikin matafiya 19 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a Hawan Kibo da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Filato a jiya Talata.

    A wata sanarwa da kakakin rundunar sojin sama ta Najeriya, Olusola Akinboyewa ya fitar, ya ce, sojojin na kan hanyarsu ne ta zuwa wani wasa a Abuja, lokacin da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota.

    Sai dai kuma wani bayani da hukumar kiyaye haɗura ta Najeriya ta fitar ya saɓa da wanda kakakin sojin ya fitar, inda hukumar ta ce motar bas ta sojojin ƙirar Hiace, mai ɗaukar mutum 18 da ta taso daga Yola ta bi yo ta Jos a kan hanyarta ta zuwa Abuja ta ci karo ne da tirela wadda ke tsaye a kan hanya, lamarin da ya janyo mutuwar direban da dukkanin sauran mutanen da ke cikin motar su 18.

    A wata hira da tasahar talabijin ta Channels, kakakin hukumar ta kiyaye haɗura (FRSC) a jihar ta Filato, Peter Longsan, ya ce dukkanin mutanen da ke cikin wannan mota bas da sojojin suke sun mutu.

    Longsan ya danganta munin haɗarin da ya kai ga mutuwar mutanen gaba ɗaya, da gudun da direab bas ke yi inda ya ce a dalilin hakan ne da ta yi karo da tirelar ba wanda ya tsira.

  5. Rasha na ɗaukar fursunoni aikin soji domin yaƙi a Ukraine - BBC

    Andrey Perlov

    Asalin hoton, Novosibirsk courts administration

    Bayanan hoto, An gaya wa fursuna Andrey Perlov, za a iya dakatar da shari'arsa idan zai shiga soja

    Wani bincike da BBC ta gudanar ya gano cewa Rasha ta faɗaɗa yadda take ɗaukar fursunoni domin su yi mata yaƙi a Ukraine.

    Bayan wannan a yanzu ta kuma haɗa da mutanen da ake tsare da su waɗanda ke jiran shari'a.

    BBC ta gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar shafin Intanet mai zaman kansa na Mediazone da ke Rasha.

    Wakilyar BBC ta ce wata sabuwar doka da aka yi wadda kuma ta fara aiki a farkon wannan shekarar ta buƙaci masu shigar da ƙara da lauyoyi da su yi wa kusan duk wanda ake zargi da aikita laifi a Rasha tayin kwantiragin aikin soji.

  6. Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya kai ƙarar jam'iyyar Labour ta Birtaniya

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Kwamitin yaƙin neman zaben Donald Trump ya shigar da ƙara kan jam'iyyar Labour da ke mulki a Birtaniya, inda ya zarge ta da yin katsalandan a zaɓen Amurka.

    Sanarwar da ofishin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar Republican ya fitar ta yi nuni da rahoton da wata jaridar Birtaniya (The Telegraph) ta bayar cewa wasu mutane da ke da alaka da jam’iyyar Labour sun je Amurka don yaƙin neman zabe a madadin ƴar takarar jam'iyyar Democrat, Kamala Harris.

    Bayanai na nuna cewa har yanzu babu wani martani a hukumance daga Jam'iyyar Labour, amma jami’an jam’iyyar sun ce waɗanda suka yi tafiyar ba jam'iyyar labour ce ta ɗauki nauyinsu ba.

  7. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafi na BBC Hausa da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, muna yi muku maraba a wannan safiya ta Laraba 23 ga watan Oktoba, 2024.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da mu a wannan rana kamar kullum.

    Ni ne Muhammad Annur Muhammad, zan kasance da ku daga yanzu har zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Mu fara da wannan karin maganar da ke cewa - Komai gaggawar ungozoma ta bari a haihu.