Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/12/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 04/12/2025.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Umar Mikail

  1. Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatan lafiya a Gaza sun ce hare-hare ta sama da Isra'ila ke kai wa sun kashe mutum biyar a kudancin Zirin, tare da jikkata wasu da dama.

    Waɗanda suka ga harin a sansanin 'yan gudun hijira na al-Mawasi sun ce Isra'ilar ta kai harin ne kan wani tanti.

    Sannan ta biyo baya da wasu hare-haren a kusa da asibitin Kuwait, abin da ya dugunzuma iyalan da ke fake a wajen.

    Hamas ta kira harin da dabbanci - na kan-mai-uwa-da-wabi, wanda kuma ya saɓa da yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da Amurka ta samar- wadda ta fara aiki mako bakwai da ya wuce.

    Rundunar sojin Isra'ilar ta ce ta kai harin ne a matsayin martani bayan da aka farmaki dakarunta.

  2. Amurka, Rasha da China na ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Laliben da ake yi na neman gano bakin zaren kawo karshen yakin Ukraine na kara fadada, inda ake ci gaba da tattaunawa a Florida da Beijin, yayin da shugaba Putin na Rasha ke India, inda yake ƙoƙarin ƙara ƙarfin alaƙarsa da ɗaya daga cikin manyan ƙawayen kasarsa.

    Fadar gwamnatin Amurka - White House ta tabbatar da cewa wakilin musamman na Shugaba Trump Steve Witkoff zai gana da masu shiga tsakani na Ukraine a yau Alhamis, domin tattauna martanin Rasha a kan shirin samar da zaman lafiya da Amurka ke mara wa baya.

    Mista Witkoff zai ba wa Trump bayani a kan tattaunawarsa da Putin a Moscow, inda Putin din ya ce masa Rasha ba za ta yarda da wasu daga cikin tanade-tanaden shirin ba.

    Ita ma Ukraine ta ki yarda ta sallama wa Rasha dukkanin yankunan da rashar ke nema.

  3. Manyan alƙawurra uku da C.G. Musa ya ɗauka game da tsaron Najeriya

    ...

    Asalin hoton, X/Defence Headquarters

    "Bayan shafe shekaru 39 na rayuwata a cikin aikin soja, na ga duk abin da ke faruwa, na fahimci duk abin da ke faruwa kuma na san abin da muke bukata," kamar yadda Janar Christopher Musa mai ritaya ya bayyana lokacin da majalisar dattijan Najeriya ke tantance shi a ranar Laraba.

    Ya kara da cewa "Za mu iya cin nasara a wannan yaki, amma wajibi ne mu yi aiki tare, wajibi ne mu samu taimako da muke bukata.”

    Nadin Christopher Musa - wanda majalisar dattijan Najeriya ta tantance shi a ranar Laraba bayan shugaba Bola Tinubu ya mika sunansa - a matsayin ministan tsaro na zuwa ne yayin da kasar ke cikin wani mawuyacin hali game da tsaro.

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu ci gaba daga inda muka tsaya a jiya na labaran kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a cikin Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.