Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Afcon 2025/26: Najeriya za ta buga kwata fainal karo na 12

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan wasan Najeriya da Mozambique karawar zagaye na biyu gasar kofin nahiyar Afirka 2025/26 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw

  1. Ko Najeriya za ta kai kwata fainal a kan Mozambique?, Afcon Morocco 2025/26

    A yau Litinin ne Najeriya za ta ɓarje gumi da Mozambique a wasan zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta cin kofin Afirka da ake gudanarwa a Morocco.

    Za a fara karawa tsakanin Masar da Benin da karfe biyar na yammaci daidai da agogon Najeriya da Niger, sai a kece raini tsakanin Najeriya da Mozambique da karfe takwas na dare daidai da agogon Najeriya da Niger.

    Super Eagles ta yi ta ɗaya a rukuni na uku da maki tara, ita kuwa Mozambique tana daga cikin huɗun da aka yi wa alfarmar zuwa zagaye na biyun da maki uku daga rukuni na shida da ta yi ta uku.

    Masar ma ita ce ta yi ta ɗaya a rukuni na biyu da maki bakwai, Benin kuwa alfarma aka yi mata daga rukuni na huɗu da maki uku, bayan karewa a mataki na uku.

  2. Salah ya kara ci wa Masar ƙwallo, Masar 3-1 Benin

    Mohamed Salah na Masar ya ci kwallo da kafar hagu daga wajen da'ira zuwa tsakiyar raga.

    Zizo ne ya taimaka masa bayan wata kora da suka kai.

  3. Brahim Diaz ne kan gaba a yawan cin ƙwallaye a Afcon, Waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye a Morocco

    • Brahim Díaz (Morocco) – 4
    • Lassine Sinayoko (Mali) – 3
    • Ayoub El Kaabi (Morocco) – 3
    • Riyad Mahrez (Algeria) – 3

    Waɗanda ke kan gaba a cin ƙwallaye bibiyu a Afcon:

    • Christian Kofane (Cameroon) – 2
    • Pape Gueye (Senegal) – 2
    • Mohamed Salah (Egypt) – 2
    • Lyle Foster (South Africa) – 2
    • Oswin Appollis (South Africa) – 2
    • Ademola Lookman (Nigeria) – 2
    • Elias Achouri (Tunisia) – 2
    • Raphael Onyedika (Nigeria) – 2
    • Gaël Kakuta (DR Congo) – 2
    • Chérif Ndiaye (Senegal) – 2
    • Nicolas Jackson (Senegal) – 2
    • Ibrahim Maza (Algeria) – 2
    • Amad Diallo (Côte d’Ivoire) – 2
    • Geny Catamo (Mozambique) – 2
  4. Morocco ta kai kwata fainal a Afcon za ta kara da Kamaru, Afcon Morocco 2025/26

    Morocco ta tsallaka zuwa kwata fainal a gasar cin kofin Afirka a ranar Lahadi da take karɓar bakunci, bayan da ta doke Tanzania da ci 1–0 a Rabat.

    Fitatcen ɗan wasanta mai taka leda a Real Madrid, Brahim Díaz ne ya ci ƙwallon, hakan ya kara kwarin gwiwa ga ƴan wasan tawagar da ke fatan lashe kofin karo na biyu jimilla.

    Yanzu haka Morocco ta kai matakin kwata fainal ne karo na uku kacal tun bayan kai wa wasan ƙarshe a shekarar 2004, za kuma a fara wasannin zagayen kwata fainal ɗin a Rabat ranar Jumma’a, wadda za ta fuskanci Kamaru.

  5. Tuni Afirka ta Kudu ta yi ban kwana da Afcon ranar Lahadi, Afcon Morocco 2025

    Tawagar Afirka ta Kudu ta fice daga gasar AFCON, bayan ta sha kashi 2–1 a hannun Cameroon a zagayen ƴan 16 ranar Lahadi.

    Kenan Afirka ta Kudu mai Afcon ɗaya a tarihi za ta koma gida domin shirye-shiryen tunkarar gasar kofin duniya a bana da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico, wadda tana daga cikin masu wakiltar Afirka.

    Indomitable Lions ta Kamaru, wadda ta fitar da Afirka ta Kudu za ta haɗu da mai masaukin baƙi, Morocco ranar Juma'a a Rabar a zagayen kwata fainal.

  6. Benin ta canja ɗan wasa, Masar 2-1 Benin

    Mattéo Ahlinvi ya maye gurbin Yohan Roche.

  7. An kammala karin lokaci na farko, Masar 2-1 Benin

  8. Tunisiya ta kori kociyanta, Trabelsi bayan kasa cin Mali, Afcon Morocco 2025/26

    Ƙasar Tunisia ta sallami babban kocinta, Sami Trabelsi, bayan fitar da iata a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Tunisia (FTF) ta tabbatar da wannan mataki a ranar Lahadi, kasa da awanni 24 bayan Tunisia ta fita daga gasar bayan ta sha kashi a hannun Mali a bugun fanareti a zagayen ƴan 16, bayan wasan ya kare 1–1 har da ƙarin lokaci.

    Tunisia ta fara gasar AFCON 2025 da nasara 3–1 a kan Uganda, sakamakon da ya ɗan farfaɗo da fatan yin nisa a gasar.

    Sai dai wannan fata ta ragu bayan shan kashi 3–2 a hannun Najeriya, sannan ta yi kunnen doki 1–1 da Tanzania a wasan rukuni na ƙarshem.

    Haka kuma shakku ya bayyana a wasan da Mali ta yi waje da ita. Duk da cewa Tunisia ta fara zura kwallo daga baya aka farke, sannan Mali ta kare karewar da yan wasa 10 a cikin fili.

    Byana da suka tashi 1-1 ne har da karin lokaci, sai aka yi bugun fenariti, inda Mali ta kai kwata fainal da cin 3-2.

    Rashin wucewa zagayen kwata fainal wani koma baya ne ga Tunisia, ƙasar da ta lashe kofin AFCON a gida a shekarar 2004, amma tun daga wancan lokaci take fama da fuskantar kalubale a wasannin babbar gasar tamaula ta Afirka.

  9. Sakamakon wasannin Gasar Kofin Nahiyar Afirka 2025

    Dukkan sakamakon wasannin cin kofin nahiyar Afirka tun daga ranar da aka fara da wasannin zagaye na biyu da ake da kuma jadawalin gasar.

  10. Jama'a barkanmu da kasancewa a wannan lokacin

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skipper zan gabatar muku da sharhi da bayanan wasa tsakanin Najeriya da Mozambique karawar zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka a Morocco ranar Litinin.

    Za ku iya bayar da gudunmuwarku a lokacin da nake gabatar da shirin a BBCHausa Facebook.