Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Afcon 2025/26: Najeriya za ta buga kwata fainal karo na 12

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku sharhi da bayanai kan wasan Najeriya da Mozambique karawar zagaye na biyu gasar kofin nahiyar Afirka 2025/26 da ake yi a Moroko.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw

  1. , Najeriya 2-0 Mozambique

    An shiga cikin ƙarin lokaci na mintuna uku da aka ƙayyade.

    Mozambique ta samu bugun tazara ba nisa da ragar Najeriya a gefen hagu.

  2. , Najeriya 2-0 Mozambique

    Geny Catamo, wanda ke kai barazana ga Najeriya, ya yi bugun tazara daga gefen dama zuwa bayan sandar raga ta nesa, inda Faizal Bangal ya taɓa kwallon da kai amma ta tafi kusa da raga amma an busa satar gida.

  3. , Najeriya 2-0 Mozambique

    Bright Osayi-Samuel ya kawo kwallo daga gefen dama ta kai ga Victor Osimhen a cikin gidan Mozambique, ya sa kai, amma kwallon ta je kusa da raga amma ba ta shiga ba.

    Mai tsaron ragar Mozambique, Ernan, ya ji rauni yayin da yake ƙoƙarin dakatar da wƙwallon.

  4. GOAL Najeriya 2-0 Mozambique, Victor Osimhen

    Alex Iwobi ya sake bayar da ƙwallo daga layin rabin fili a gefen hagu, inda ya buga kwallo ba tare da kallon ba zuwa ga Ademola Lookman a gabansa, daga kusa da da'ira.

    Akor Adams ya taɓa kwallon a hankali daga bugun da Lookman ya yi a cikin gidan Mozambique, sai ya bai wa Victor Osimhen wanda ba a san yana wajen ba, sai ya ci ƙwallon cikin sauki.

    Mai Afcon uku ta fara samun natsuwa a wasan.

  5. , Najeriya 1-0 Mozambique

    Najeriya sai kara kai hare-hare take ta san ƙwallo ɗaya ba abin dogara bace, kuma tun kafin wasan ya yi nisa take son kammala shi

  6. GOAL Najeriya 1-0 Mozambique, Ademola Lookman

    Alex Iwobi ya ɗaga kai sannaun ya buga wa Ademola Lookman shi kuma bai ɓata lokaci ba ya zura a raga.

  7. , Najeriya 0-0 Mozambique

    Reinildo ya samu bugun kusurwa, Mozambique ta buga ƙwallon da ƙarfi daga bugun kusurwar, ta fitar zuwa jifa ga Najeriya.

  8. , Najeriya 0-0 Mozambique

    Najeriya ta samu bugun tazara ba nisa da bakin ragar Mozambique a gefen hagu.

    Ademola Lookman ya daga hannu yana kiran ‘yan wasansa da ke cikin da'ira ta 18 domin su shirya karɓar kwallon.

  9. Osimhen ya na bugan wasan ba tare da kariyar fuskar roba ba, Najeriya 0-0 Mozambique

    Victor Osimhen, ya na wasan daren yau ba tare da abin rufe fuska na kariya ba.

    Wannan abin kariyar fuska mai launin baki da aka ƙera masa na musamman ya zama koda yaushe ɗan wasan mai shekaru 27 na amfani da shi, tun bayan dawowarsa fili daga raunin fuska da ya samu a watan Nuwamba 2021.

    Wannan rauni na daga cikin dalilan da ya sa ya rasa halartar gasar AFCON 2021 da aka gudanar a Kamaru

    Yanzu dai ya cire abin kariyar, Osimhen na kokarin ganin ya zura ƙwallo a wasan da ake yi a Fes.

  10. , Najeriya 0-0 Mozambique

    An fara samun nutsuwa a wasan bayan an soke kwallon da Victor Osimhen ya zura a raga.

    Najeriya na ci gaba da taka rawar gani tare da neman hanyoyin damar cin ƙwallo.

  11. Osimhen ya ci ƙwallo amma an soke a satar gida, Najeriya 0-0 Mozambique

    Jim kaɗan bayan mai tsaron ragar Mozambique, Ernan, ya kama wata kwallo da Bright Osayi-Samuel na Birmingham City ya buga daga gefe, Najeriya ta kuma amfana, inda Frank Onyeka na Brentford ya bai Victor Osimhen ƙwallon.

    Shi kuwa ɗan wasan gaba ya zura kwallon da kai, amma nan take aka daga tutar satar gida.

  12. , Najeriya 0-0 Mozambique

    An samu ɗan jinkiri a wasan yayin da wani daga cikin ma’aikatan filin wasa ke gyara wani ɓangare na ragar kwallo.

    ‘Yan wasa kuma suna watsawa da buga kwallo domin su ci gaba da kasancewa cikin ɗumi.

  13. An take leda a karawar da ake yi a Fes, Najeriya 0-0 Mozambique

  14. Ana taken kasashen biyu a yanzu haka, Najeriya 0-0 Mozambique

    Ana kuma ruwa a filin ko ina ya jike.

  15. Ƴan Super Eagles da za su kara da Mozambique, Afcon Morocco 2025/26

  16. Ƴan Mozambique da za su fuskanci Najeriya

  17. Super Eagles na fatan lashe Afcon na huɗu a Morocco, Afcon Morocco 2025/26

    Najeriya na fatan lashe Afcon na huɗu a bana a Morocco, za kuma ta ƙara da Mozambique a wasan zagaye na biyu ranar Litinin a Stade de Fes.

    Wannan shi ne karo na biyu da za su kece raini a gasar cin kofin Afirka.

    Sun fara haɗuwa a karawar cikin rukuni a 2010, inda Najeriya ta yi nasara 3-0

    Jimilla sau biyar suka fafata a tsakaninsu, Najeriya ta yi nasara huɗu da canjaras ɗaya.

    Wasan baya-bayan nan da suka haɗu shi ne a sada zumunta da suka yi ranar 16 ga watan Oktoban 2023 a Portugal, Najeriya ce ta yi nasara 3-2.

  18. Faɗi tashin Mozambique a gasar cin kofin Afirka, Afcon Morocco 2025/26

    • Mozambique ta kawo wannan matakin karon farko daga Afcon na shida.
    • Ba ta kai zagaye na biyu ba daga karawa biyar baya a wasannin cikin rukuni.
    • Mozambique da Zimbabwe su ne tawagogin da aka zura wa ƙwallaye a kowanne wasa 18 da suka yi a Afcon.
    • Mozambique ta yi rashin nasara uku da ta fuskanci Ivory Coast ta fuskanci Masar sau huɗu an doke ta uku da canjaras ɗaya da fafatawa biyu da Ghana daga ciki ta yi canjaras ɗaya aka doke ta ɗaya.
    • Sannan ba ta zura ƙwallo ba a raga daga wasa bakwai da aka doke ta da ta fuskanci tawaga daga Yammacin Afirka.
  19. Ƙwazon da Super Eagles ke yi a gasar kofin Afirka, Super Eagles

    • Wannan shi ne karo na 18 da Super Eagles ta kai zagaye na biyu kai tsaye.
    • Karo na 16 a jere ta kawo wannan matakin, bayan da ta kasa kai wa zagaye na biyu a 1982.
    • Ta kuma lashe dukkan wasa uku da ta yi a rukuni a Morocco, bayan cin Tanzania 2–1 da doke Tunisia 3–2 da nasara akan Uganda da cin 3–1.
    • Karon farko da Najeriya ta yi nasara a dukkan wasa uku a cikin rukuni tun bayan 2021.
    • Idan har Super Eagles ta yi nasara, zai zama karo na 61 da za ta ci wasa a Afcon, ita ta biyu a yawan cin wasa a gasar kofin Afirka bayan Masar mai 62.
    • Ta ci ƙwallo takwas a karawar cikin rukuni, karon farko da ta zura da yawa a raga a Afcon a fafatawar cikin rukuni.
    • An kuma zura ƙwallo huɗu a ragar Najeriya a wasannin cikin rukuni a Morocco, kenan guda 99 aka ci Super Eagles a tarihin gasar.
    • Idan aka zura mata ƙwallo a wasa da Mozambique za ta shiga jerin waɗanda aka ci 100 ko sama da haka da ya haɗa da Ivory Coast da ci ƙwallo 112 da Jamhuriyar Congo 112 da kuma Tunisiya da aka ci ƙwallo 102.
    • Idan har Najeriya ta yi nasara za ta kai zagayen kwata fainals karo na 12, mai Afcon uku.
    • Tun lokacin da fara kwata fainal a 1992, sau ɗaya ne Super Eagles ba ta kai zagayen ƴan takwas ba, shi ne a 2021.
  20. Mozambique za ta kara da Najeriya da ƙyaƙƙyawan fata, Afcon Morocco 2025/26

    Har zuwa Lahadi, 28 ga watan Disamba, ƙasar Mozambique ba ta taɓa samun nasara ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

    Wasa 16 ta yi kuma tsawon shekaru masu yawa, sun wuce ba tare da ta yi murnar cin wasa ba a tarihin babbar gasar ta Afirka.

    Wannan dogon jira ya zo ƙarshe a Grand Stade d’Agadir, inda Mambas suka ba kowa mamaki ta hanyar doke Gabon da ci 3–2, ɗaya daga tarihin da ba za a manta da shi ba.

    Wannan sakamako ya zama tarihi a fani biyu: ya zama nasara ta farko a tarihin Mozambique a AFCON, sannan kuma ya tabbatar da karon farko da ta tsallaka zuwa zagayen ziri ɗaya ƙwale, duk da cewa wannan ne karo na shida kacal da suke halartar gasar Afcon.