Trump ya ce ya samu ƙwarin guiwa kan ƙare yaƙin Ukraine

Asalin hoton, Getty Images
Shugaba Trump ya ce bayan soma tattaunawa da Rasha, ya samu ƙwarin guiwa kan samar da zaman lafiya a Ukraine.
Tattauanwar ita ce ta farko tsakanin Amurka da Rasha tun bayan mamayar da Rashar ta yi wa Ukraine.
A wajen wani taron manema labarai a Ma-ra-La-go shugaba Trump ya ce, za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya cikin sauƙi, sai dai ya ce ya ji takaicin yadda Ukraine ta yi ƙorafin ba a sanya ta cikin tattaunawar ta Saudiya ba.
Wakiliyar BBC ta ce shugaba Trump ya dora wa Ukraine laifi na fara takalar yaƙin, inda ya ce da shi ne shugaban ƙasa a lokacin hakan ba za ta faru ba.
