Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Asuba ta gari.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Laraba, 19 ga watan Fabarairun 2025
Muhammad Annur Muhammad da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Asuba ta gari.
Shugaba gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce ganganci ne ayyana Volodymyr Zelensky a matsayin ɗan kama karya.
Kalaman shugaba Trump sun ƙara haifar da damuwa a Turai tun bayan sauyin manufofin Amurka game da Ukraine da Rasha.
Firaiministan Sweden Ulf Kristersson ya ce duniya na tsaka mai wuya kuma abin da zai biyo bayan yaƙin zai shafi Turai lokaci mai tsawo.
A nata ɓangaren Firaiministar Denmark Mette Frederiken ta sanar da ƙarin dala biliyan bakwai da za a yi amfani da su a fannin tsaro har shekaru biyu masu zuwa.

Asalin hoton, Getty Images
Babban ministan jihar Uttar Pradesh a Indiya ya dage cewa za a iya yin wanka da ibada da ruwan da ke Triveni Sangam wurin bukukuwan addini na Kumbh Mela.
Ya yi watsi da rahoton gwamnati wanda ya gano ruwan cike ya ke da kwayoyin cuta saboda ƙazantar da ke cikinsa.
Triveni Sangam, wuri ne mai tsarki ga mabiya addinin Hindu waɗanda suka yi imanin ruwan na tsarkake rai.
Hukumomi sun ce sama da masu ibada miliyan 500 suka yi wanka a tare da shan ruwan a bikin Kumbh Mela da aka fara tun 13 ga watan Janairu.

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin nemo wa tare da hukunta waɗanda suka shirya zanga-zangar tsadar rayuwa da ta riƙiɗe zuwa tarzoma.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi rahoton kwamitin da aka kafa don gudanar da bincike kan lamarin a gidan gwamnati da ke jihar.
Mutum goma ne suka rasa rayukansu, yayin da da dama suka samu munanan raunuka, a cewar rahoton.
Haka kuma - an yi asarar dukiya ta kusan biliyan 11 lokacin zanga-zangar.
"Ina da ƙwarin gwiwa kan aikin da kwamitin ya yi, mun zaɓe su ne bisa cancanta. Ba mu yi musu katsalanda ba wajen yin aikin da aka saka su," in ji Gwamna Abba Kabir.
Gwamnan ya tabbatar da cewa za ta ɗauki matakin da ya dace kan abin da rahoton ya gano domin hakan ya zama izina ga waɗanda ke son tayar da tarzoma.

Donald Trump ya wallafa kakkausar suka ga shugaban Ukraine, yayin da cacar-baki ta ɓalle sakamakon buɗewar sabon babin kawance tsakanin Washington da Moscow.
Ya yi iƙirarin cewa Mista Zelensky ya nemi Amurka ta kashe biliyoyin daloli a rikicin da ba zai iya yin nasara ba.
Mista Trump ya kira shi "Mai mulkin kama-karya ba" wanda ya kasa gudanar da zaɓe - inda ya ce zai fi kyau ya gaggauta ɗaukar mataki ko kuma ya rasa ƙasarsa.
Kyiv ta gudanar da zaɓe na karshe a shekara ta 2019 - ba ta samu damar sake shirya wani ba saboda mamayar Rasha a farkon shekara ta 2022.
Tun da farko dai Mista Zelensky ya ce Rasha ta yi wa Mista Trump karairayi.

Asalin hoton, Reuters
Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa an gudanar da tattaunawa cikin farin ciki a Saudiyya ranar Talata.
Ya ce Amurkawa sun yi adalci ba tare da goyon bayan kowanne ɓangare ba yayin tattaunawar.
Game da taron ƙoli a wannan watan, Mista Putin ya ce zai so ganawa da Donald Trump, amma bayan an aiwatar da wasu muhimman al'amura.
Ƙasashen Turai da dama na jin Amurka da Rasha sun jingine su, amma Putin ya ce Turai ta zargi kanta game da lalacewar dangantakar ta da Washington.
"Mun amince za mu yi aiki tare kuma a yanzu batu ake tsakanin Amurka da Rasha don haka ba ma bukatar shigowar wani ɓangare," in ji Putin.

Asalin hoton, facbook/Dauda Lawal
Wasu mutum biyu sun mutu bayan fashewar wani abu a wata kasuwa a Talata-Mafara, da ke jihar Zamfara.
Lamarin wanda ya afku ranar Talata, ya janyo fargaba da kuma ruɗani tsakanin ƴan kasuwa da masu saye.
Wani ganau ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa fashewar ta afku a wani shago da ake sayar da makaman da ake haɗa wa.
Shugaban karamar hukumar Talata-Mafara, Yahaya Yari, ya tabbatar da afkuwar lamarin.
Ya ce tuni aka garzaya da mutum 44 da suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Usman Danfodio da ke jihar Sokoto domin kula da su.
Shugaban karamar hukumar ya sanar da haramta sayar da makaman da ake ƙera wa a cikin gida a kasuwar.
Irin makaman da ake haɗawan dai, wanda yawanci ƴan bijilanti ke amfani da su - sun yaɗu ko ta ina abin da janyo fargaba kan tsaron lafiyar mutane.

Asalin hoton, Getty Images
Ademola Lookman ya ce ya ji takaicin irin kalaman da kocinsa Gian Piero Gasperini ya yi kansa, bayan da ya kwatanta ɗan wasan da "wanda ya fi kowa rashin iya buga fenareti" da ya taɓa gani.
Kocin ya yi kalaman ne bayan da Atalanta ta yi rashin nasara a hannun Club Brugge da ci 3-1 ranar Talata a gasar Zakarun Turai, abu kuma da ya sa ƙungiyar ta fice daga gasar da kwallo 5-1 gida da waje.
"Abin ɓacin-rai ne in yi martani a irin wannan rana - saboda abin da muka cimma a matsayin ƙungiya," kamar yadda Lookman ya rubuta a shafinsa na sada zumunta.
Ya ce ya ji takaicin ware shi kaɗai da kocin ya yi, duk da irin hazaka da kuma ƙoƙarin da yake yi wajen ganin ƙungiyar ta yi nasara.
Ana tuhumar sojojin Isra'ila biyar da cin zarafi da kuma yi wa wani fursunan Falasɗinu raunuka a wata cibiyar tsare mutane.
An zarge su da lakaɗa wa wanda ake tsare da yin duka a gidan yarin Sde Teiman a watan Yulin bara, bayan sun rufe masa fuska tare da ɗaure hannayensa da ankwa.
Fursunan ya samu muggan raunuka da suka haɗa da karyewar kashin kirji da kuma yi wa huhunsa rauni.
Kamen waɗanda ake zargin ya fusata wasu ministocin gwamnati da ƴan siyasar haɗaka da suka shiga sansanin don su dakatar da tuhumar.

Asalin hoton, Nigerian Senate
Majalisar Dattawan Najeriya ta gayyaci shugabannin hukumomin bayanan sirri da na tsaron ƙasar da su gudanar da bincike kan zargin da ɗanmajalisar wakilan Amurka Perry Scott ya yi cewa hukumar raya ƙasashe masu tasowa ta Amurka, USAID, na samar da kuɗaɗe ga ƙungiyoyin ta'addanci ciki har da Boko Haram.
Majalisar ta zartar da hakan ne bayan da Sanata Mohammed Ali Ndume, ya gabatar da buƙatar binciken.
Ndume ya buƙaci majalisar ta ɗauki maganar da muhimmanci bisa la'akari da iallar da 'yan ta'adda musamman ma Boko Haram suka yi.
Sanatan ya jaddada cewa cikakken bincike a kan lamarin zai iya kawo ƙarshen jita-jitar da ake yaɗawa a kan yadda 'yan ta'adda suka iya kaiwa tsawon waɗannan shekaru suna ta'asa a ƙasar.

Asalin hoton, OTHERS
Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa ƙasarsa ba za ta amince da korar Falasɗinawa daga Gaza ba.
Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karɓe ikon Zirin bayan sauya wa al'ummar Gaza matsuguni.
Shugaban na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a haɗa shi da shirin da zai samar da zaman lafiya.
A ci gaba da rangadin da Marco Rubio yake a Gabas ta Tsakiya tuni ya je Isra'ila da Saudiyya.

Asalin hoton, Wereldmuseum
Kasar Netherlands za ta mayar wa Najeriya mutum-mutumin tagulla 113 da Turawan mulkin-mallaka suka sace.
An sace su ne a shekarar 1897daga masarautar Benin wadda yanzu take a Najeriya inda aka rarraba su a gidajen ajiyar kayan tarihi a Netherlands.
Yayin da za a rattaba hannu a yarjejeniyar mayar da kayan tarihin zuwa Najeriya a yau, wani babban jami'in hukumar ajiyar kayan tarihi a Najeriya Olugbile Holloway ya ce suna fatan ɗaukar wannan mataki za ta zama misali ga sauran ƙasashe.
Wakiliyar BBC ta ce Ministan al'adu na Netherlands ya ce mayarwar ta haifar da matsin lamba ga gigajen ajiyar kayan tarihi na ƙasashen ƙetare.
Mutum-mutumin tagullan ya zama ma'aunin gwaji ko ƙasashen Turai za su mayar da kayan tarihin da aka sace.
Jamus ma ta fara mayar da tagullar zuwa Benin amma gidan ajiyar kayan tarihi na London ya ce doka ta hana shi mayarwa.

Asalin hoton, Getty Images
Hamas ta ce a shirye take ta saki dukkanin Isra'ilawan da take riƙe da su a lokaci ɗaya, waɗanda daman za ta saki a mataki na gaba na yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta da Isra'ila, ba rukuni-rukuni ba kamar yadda take yi ba yanzu.
To amma kuma kakakin ƙungiyar ta Hamas, Hazem Qassem, ya ce wannan tayi da ta gabatar na sakin 'yan Isra'ila 60, ya dogara ne ga janyewar dakarun Isra'ila kacokan daga Gaza, da kawo ƙarshen yaƙin gaba ɗaya.
A sanarwar Hamas ta kuma yi watsi da buƙatar Isra'ila ta cewa Hamas ɗin ta zubar da makamanta kuma ta bar Gaza.

Asalin hoton, Reuters
Wani taron manema labarai da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi ya fito da ɓarakar da ke tsakaninsa da Shugaban Amurka Donald Trump, ƙarara.
Haka kuma maganganun da ya yi sun nuna yadda ƙasar ta Ukraine ke dab da rasaAmurka a matsayin ƙawa - har ma wasu na cewa ai tuni sun raba gari.
Kalaman da Shugaba Trump ke faɗi sun yi kusan daidai da abin da gwamnatin Rasha ke faɗa, to amma matakin da zai ɗauka ya kawo ƙarshen yaƙin shi ne ba a sani ba har yanzu.
Zelensky ya ce zuwa yanzu yaƙin ya laƙume dala biliyan 320, yana mai ƙari da cewa alƙaluman sun bambanta a ɓangaren gwamnatinsa da kuma Amurka.
Ya ce kusan dala biliyan 120 ta fito ne daga asusun Ukraine yayin da Amurka da Turai suka bada dala biliyan 200.
Amurka ta ba ta makamai da kuma tallafin kasafin kuɗi da suka kai na dala biliyan 67.
A baya Trump ya ce Amurka na son abin da yake daidai dala biliyan 500 na ma'adanan ƙarƙashin ƙasa na Ukraine, idan ƙasar na son Amurka ta ci gaba da ba ta goyon baya da tallafi.
Zelensky ya ce Amurka ta yi zargin cewa tana tallafa wa ƙasarsa da kashi 90 cikin ɗari a yaƙin da take yi -''to amma gaskiyar tana wani waje daban,'' in ji shi, ''to amma muna godiya da taimakonsu.''

Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiya da ke sa ido kan yawan hare-haren da ake kai wa Musulmi a Birtaniya ta ce ta tantance hare-haren da aka kai wa Musulmin waɗanda ba a taɓa samun yawunsu ba a ƙasar a shekarar da ta wuce.
Ƙungiyar Tell Mama, ta ce an kai irin waɗannan hare-hare kusan 6,000, waɗanda an kai su ne saboda ƙyamar Musulmi.
Ƙungiyar da danganta ƙaruwar a kan abin da ta kira yaɗa kalaman ƙarya da ke nuna Musulmi a matsayin 'yanta'adda ko kuma masu goyon bayan 'yanta'adda
A karon farko bincike ya nuna maza sun fi fuskantar haɗarin kai hari fiye da mata.

Asalin hoton, PA Media
Hukumar wata gunduma a kusa da babban birnin Philippines na biyan kuɗi ga jama'a domin su kama sauro don hana yaɗa cutar zazzaɓin Denge (dengue).
Shugaban ƙauyen Barangay Addition Hills, da ke wajen Manila, Carlito Cernal, na bayar da kuɗin ƙasar peso ɗaya -- kwatankwacin santi biyu na Amurka -- a kan duk sauro biyar da mutum ya kama ya kai.
An samu ƙaruwar cutar zazzaɓin Denge a ƙasar ta Philippines, a wannan shekara.
Cutar wadda sauro ke yaɗawa tana haddasa ciwon kai da ciwon jiki idan kuma ta yi tsanani takan kai ga mutuwa.
Sai dai wasu na ganin kamun sauran ba ita ce hanyar da ta fi dacewa da yaƙi da cutar ba.

Asalin hoton, PRESIDENCY NG
Aƙalla ma'aikata 450 ne da ke aiki a ofisoshin jakadancin Najeriya a ƙasashe 109 ba su samu albashinsu ba na wata biyar zuwa shida.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ma'aikatan da ke ƙarƙashin ma'aikatar harkokin wajen Najeriya na cikin mawuyacin hali na rashin kuɗi ta yadda wasunsu ba ko iya biyan kuɗin haya da kuɗin makarantar 'ya'yansu ko biyan wasu muhimman buƙatun iyalinsu.
Mai riƙon muƙamin kakakin ma'aikatar, Kimiebi Ebienfa, ya ce ma'aikatar na sane da wannan hali da ma'aikatan ke ciki, ya kuma bayar da tabbacin cewa za a shawo kan matsalar.
Manyan jami'an fadar gwamnatin tarayya da kuma jami'an da ke aiki a ma'aikatar harkokin wajen Najeriya sun bayyana wa jaridar cewa ana buƙatar dala biliyan ɗaya domin biyan bashi da kuma tafiyar da harkokin ofisoshin jakadancin ƙasar daban-daban a ƙasashen duniya.
A lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki ya sake nazarin manufofin waje na ƙasar inda ya dawo da jakadu 83 a watan Satumba na 2023.
Sai dai kuma matsalar rashin kuɗi ta haifar da jinkiri wajen naɗa sababbin jakadun har yanzu.
To amma jaridar ta ruwaito cewa rashjin naɗa jakadun ya ƙara haifar da jinkiri wajen biyan albashin ma'iakatan ofisoshin jakadancin na Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
A wani gagarumin bincike da aka gudanar tsakanin ƙasashe sama da 140, a cikin shekara 60 ya nuna cewa an samu ƙarancin amincewa gwamnati a ƙasashen da ake mulkin dimokradiyya a duniya.
Binciken da aka yi kan mutane sama da miliyan biyar ya nuna cewa an samu koma-baya wajen yin amanna da gwamnatocin dimokradiyya da suka hada da ƙasar Argentina da Brazil da Faransa da Koriya ta Kudu da kuma Amurka.
Haka kuma, binciken ya gano cewa, an samu raguwar yarda da amincewa majalisun dokoki, yayin da ɓangaren ƴansanda da ma'aikatun gwamnati da kuma tsarin shari'a yana nan da kimarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Babban mai gabatar da ƙara na Brazil ya bada shawarar a tuhumi tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro kan yunƙurin juyin mulki bayan ya sha kaye a zaɓen 2022.
Idan har kotun ƙoli ta amince da hakan, za a tuhumi Mista Bolsonaro da wasu mutum 30, inda za su fuskanci shari'a.
Wakiliyar BBC ta ce wata uku da ya gabata ƴansanda sun fitar da wani rahoto da ya yi zargin cewa Bolsonaro ya taka muhimmiyar rawa wajen shirya juyin mulki bayan ya fadi zaɓe.
Tsohon shugaban ƙasar ya musanta aikata ba daidai ba, inda ya ce ana yi masa bita-da-ƙullin siyasa ne.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴanbindiga sun kashe fasinjoji bakwai na wata motar bas a lardin Baluschistan na Pakistan.
Hukumomin yankin sun ce ƴanbindigan sun shiga motar ne tare da fasinjojin inda suka tilasta masu miƙa katin shaidar ƴan ƙasarsu.
Daga nan ne suka ware mutum bakwai da suka fito daga lardin Punjab suka harbe su. Har yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.