Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/01/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ibrahim Muhammad da Isiyaku Muhammed, Rabiatu Kabir Runka

  1. Rufewa!

    Masu bibiyarmu a wannan shafi nan ne muke yi muku ban-kwana, sai kuma gobe Talata za mu sake bude wani sabon shafi na kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Haruna Ibrahim Kakangi da Rabiatu Kabir Runka ke fatan mu kwana lafiya.

  2. Netanyahu na fuskantar adawa kan sharuddan yarejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    Benjamin Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Benjamin Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu na fusantar adawa kan sharuddan yarejeniyar tsagaita wuta a Gaza daga wasu mukarrabai da majalisar ministocinsa.

    Sai dai har yanzu akwai kyakykyawan fatan a cimma nasara.

    Akwai mambobin majalisarsa 10 ciki harda 'ya'yan jam'iyyar Netanyahu da suke aike masa da wasikar nuna adawa da sharudan yarjejeniyar.

    Wakilin BBC ya ce "Mun ji cewa a daren da ya gabata, Firaministan Banjamin Netanyahu ya gana da wasu daga cikin majalisar ministocinsa, musamman masu nuna adawa, domin cimma daidaito.

    A wani bangaren kuma sojojin Isra'ila sun sanar da mutuwar dakarunsu biyar a arewacin Gaza.

    Ita kuma ma'aikatar lafiyar Hamas na cewa an kashe Falasdianwa 21 a yau Litinni, mutum biyar sun kasance 'yan gida guda

  3. An zaɓi mace ta farko a matsayin shugabar majalisar dokokin jihar Lagos

    LAGOS STATE SPEAKER

    Asalin hoton, Lagos State House of Assembly

    Mojisola Lasbat Meranda ta kafa tarihin zama mace ta farko da ta samu nasarar zama shugabar majalisar dokokin jihar Lagos da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

    Zaɓen nata na zuwa ne bayan da aka tsige, Mudashiru Obasa a yayin zaman majalisar na yau Litiinin.

    Meranda mai shekara 44, ƴar majalisa ce da ke wakiltar Apapa 1, kuma ita ce mataimakiyar shugaban majalisar da aka tsige.

    An rantsar da Meranda a zauren majalisar dokokiin jihar Lagos, inda ta jadada aniyarta ta jajircewa kan aikinta.

    "Na yi alƙawarin zan kasance mai gaskiya a matsayina ta shugabar majalisar dokokokin jihar Lagos. Zan kamanta gaskiya a kan aikina bisa dokar da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada," in ji Meranda a lokacin da ake rantsar da ita.

    Tun bayan samar da majalisar dokokin jihar Lagos an samar da majalisa tara, kuma wannan ne karon farko da aka zaɓi mace a matsayin shugaba.

  4. An ceto mutanen da suka shafe kusan wata biyu ƙarƙashin ƙasa a Afirka ta Kudu

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, OTHER

    An ceto mutane bakwai daga karkashin kasa bayan shafe kusan wata biyu a makale sakamakon ruftawar wata mahakar ma'adinai a Afirka ta Kudu.

    Su ne rukuni na farko da aka ceto a aikin ceto daruruwan mahaka ma'adinan ta haramtacciyar hanya da suka rufta a Stilfontein.

    A watan Nuwamba ƴansanda sun ce za su kama mutanen da zaran an ceto su.

    Wata kungiyar ma'aikata ta fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna mutanen cikin yanayi na galabaita makale a karkashin kasa suna rokon abinci da kuma bayyana cewa akwai 96 da suka mutu.

    BBC dai bata tabbatar da sahihancin wannan bidiyon ba

  5. 'Doka ta tanadi ɗaurin wata uku ga wanda ya ƙi taimakon ɗansanda'

    NIGERUA POLICE

    Asalin hoton, NIGERUA POLICE

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta tunatar da al'ummar ƙasar cewa mutanen da suka ƙi taimakon jami'anta a lokacin da suke neman ɗauki, na iya fuskantar hukuncin ɗauri ko kuma tara.

    A cikin wani bayani da rundunar ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce wannan na ƙunshe ne a sashe na 99 na dokar ƴansanda ta ƙasar ta shekarar 2000.

    "Duk wanda aka kira domin ya taimaka wa jami'in ɗansanda wanda - a sa'ilin gudanar da aikinsa ke fuskantar cin zarafi ko hantara ko turjiya - sai mutum ya ƙi, ko kuma ya yi watsi da buƙatar taimakawa, to wannan mutum ya aikata laifi, wanda zai iya janyo a yanke masa tarar naira 100,000 ko ɗaurin wata uku, ko kuma duka biyun idan aka same shi da laifi," kamar yadda bayanin ya nuna.

    Rundunar ƴansandan Najeriya ɗaya ce daga cikin hukumomin tsaro da kundin tsarin mulkin ƙasar ya dora wa nauyin tabbatar da doka a cikin al'umma.

    Sai dai sau da yawa an sha kokawa kan yadda jami'anta ke gudanar da ayyukansu.

    Wannan ne ma ya haifar da ɗaya daga cikin zanga-zanga mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar, inda a cikin shekara ta 2020 matasa suka gudanar da zanga-zangar domin nuna adawa da 'zaluncin' wani ɓangare na rundunar, wanda ake yi wa laƙabi da SARS.

    Lamarin da ya yi sanadiyyar rushe ɓangaren.

  6. Majalisa ta tuhumi JAMB kan kashe kusan biliyan biyu kan abinci da maganin ƙwari

    JMB

    Asalin hoton, JAMB

    Kwamitin kudi na majalisar dokokin tarayyyar Najeriya sun tuhumi hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu, JAMB kan kashe kudin da suka wuce ƙa'ida kan abinci da lemu da ruwa da maganin sauro da sauransu a 2024.

    Kwamitin ya yi barazanar cire hukumar daga jerin ma'aikatun da za su shiga cikin kasafin kudin gwamnatin tarayya na 2025.

    Hakan na zuwa ne bayan da shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Olayede ya gabatar da kasafin kudin hukumar na 2025 a gaban kwamitin na hadin guiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai.

    Olayede ya ce JAMB ta samar da kudin shiga biliyan huɗu, yayin da gwamantin tarayya ta bata biiiyan shida, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Sai dai sanatan jihar Edo ta tsakiya, Adams Oshiomhole ya tuhumi JAMB kan kashe kudi masu yawa, inda ya buƙaci shugaban hukumar ya yi cikakken bayani kan yadda suka kashe naira miliyan 850 kan tsaro da share-share da kuma feshin kashe ƙwari a shekarar da ta gabata.

    "Kun kashe sama da biliyan ɗaya kan abinci da lemuka.Shin gwamnatin tarayya ke ciyar da ku kyauta? Abinda hakan ke nufi shine, kuna kashe kudin da kuke ƙarɓa daga dalibai marasa galihu wadanda da yawansu marayu ne. Kun kuma kashe naira miliyan 850 kan tsaro da share-share da feshin ƙwari a 2024. Wadanne irin ƙwari ne kuma kashe ? Shin sauro ne ya ɗauki dukkan kudaden?:"

    Oshiomhole ya kuma ƙalubalanci hukumar kan kashe miliyan 600 wajen tafiye-tafiyen cikin gida.

  7. Kotu ta bayar da belin sarauniya Naomi da wasu mutane uku a shari'ar turmutsistsin Ibadan

    ..

    Asalin hoton, BBC Pidgin

    Mai shari’a Kamorudeen Olawoyin na wata babbar kotu da ke zamanta a Ibadan ya bayar da belin wasu mutane uku da ake tsare da su bisa turmutsitsin da ya yi sanadiyar mutuwar yara kanana 35 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a watan Disambar bara.

    Mutanen ukun da ake zargin sun haɗa da tsohuwar sarauniya Naomi Silekunola, da wani ɗan jarida a Ibadan, Oriyomi Hamzat da kuma wani shugaban makarantar Abdullahi Fasasi.

    Suna dai tuhume-tuhume ne guda huɗu, ciki har da rashin samar da ingantaccen tsaro da wuraren samar da kiwon lafiya. Laifukan da aka ce sun saɓawa sashe na 324 na kundin dokokin Jihar Oyo

    Ko da yake masu gabatar da ƙara sun ki amincewa da batun belin, duba da tsananin turmutsitsin da kuma buƙatar a yi wa waɗanda abin ya shafa adalci, bayan sauraro bahasi daga ɓangarorin biyu kotun ta yanke hukuncin bayar da belin.

    A halin da ake ciki kuma, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya dage cewa dole ne wadanda ke da hannu a tirmutsitsin su fuskanci hukunci. Don haka, a ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnati ta shigar da ƙara kan wasu tuhume-tuhume 18 a kan waɗanda ake zargin.

  8. An fara bikin addinin hindu mafi girma a India

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Fiye da mutane miliyan 10 ne suka yi wanka a cikin kogi a bikin addinin Hindu na Kumbh Mela - wanda aka bayyana a matsayin babban taron bil'adama a duniya - a birnin Prayagraj na arewacin Indiya a ranar Litinin.

    Taron wanda ake gudanarwa sau ɗaya a kowace shekara 12 - yana farawa ranar Litinin kuma za a ci gaba da gudanar da shi har zuwa nan da makonni shida masu zuwa, masu ibada za su yi wanka a kogin Sangam wanda shi ne mahaɗin kogin Ganges da kogin Yamuna.

    Kimanin mutane miliyan 400 ne ake sa ran za su halarci bikin na kwanaki 45, wanda a kan iya hango shi daga sararin samaniya saboda tarin jama'a.

    Domin saukar da mahalarta bikin da masu yawon bude ido, an kafa wani katafaren sansanin tantuna mai faɗin hekta 4,000 a gaɓar kogin.

  9. An tsige shugaban majalisar dokokin jihar Legas

    ...

    Asalin hoton, Mudashiru Obasa/Instagram

    Ƴan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, sakamakon zarge-zargen da ake yi masa da suka jiɓanci batun saɓa dokokin majalisa da kuma almundahana.

    Tuni dai majalisar ta maye gurbinsa da mataimakinsa Mojisola Meranda.

    Misis Meranda, wadda ke wakiltar mazabar Apapa 1, ta kasance tsohuwar mai tsawatarwar majalisar. Yayin da Mojeed Fatai ya kasance sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin ta jihar Legas.

    Korar Obasa na zuwa ne wata guda bayan da ake zarge shi da kashe Naira biliyan 17 wajen gyara kofar da ke kai wa majalisar.

  10. Aƙalla Mutum 10 sun mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a Brazil

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutane 10 ne suka mutu bayan zaftarewar ƙasa da ta afku a wasu garuruwa biyu a jihar Minas Gerais ta ƙasar Brazil, kamar yadda jami'an jihar suka bayyana.

    Lamarin ya fi muni ne a Unguwar Betania da ke birnin Ipatinga, kuma hakan ya faru ne sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a yankin.

    Zaftarewar ƙasa bayan mamakon ruwan sama ba sabon abu ba ne a lokacin damina a wasu yakunan Brazil inda aka gina unguwanni da dama a kan tsaunuka da tuddai.

    Magajin garin Ipatinga Gustavo Nunes ya ayyana dokar ta bacia yankin.

    Aƙalla mutane 150 ne suka rasa matsuguni a birnin, wanda ke da tazarar kilomita 570 daga arewacin Rio de Janeiro.

    Magajin garin ya ce yawan ruwan saman da aka yi, ya bai wa mutanen yankin mamaki. "Mutane ba su samu lokacin shirywa ba," a cewar Nunes.

    Aƙalla mutane tara ne aka tabbatar sun mutu a Ipatinga, yayin da aka tsinci gawar wani a hanyar arewacin garin a yankin Santana do Paraíso.

  11. Hare-haren ƴanbindiga a Najeriya sun ragu a watan Disamba - Rahoto

    ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rahoto da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited da ke nazarin tsaro a Naigeriya da yankin Sahel ya fitar ya nuna cewa an samu raguwar kai hare-hare a Najeriya da kashi 1.6 cikin 100 cikin watan Disamban 2024.

    Rahoton ya ce aƙalla mutum 708 ne aka kashe a sassan ƙasar a watan na disamban da ya gabata sannan kuma an yi garkuwa da 674 sai wasu 671 da suka mutu.

    Rahoton ya ƙara da cewa yayin da aka samu raguwar tabarbarewar tsaro da asarar rayuka a watan na Diamban bara, yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas sun kasance wuraren da har yanzu ke cikin tashin hankali.

    Ya yi nuni da cewa, yaƙin da ake yi da ƴanbidiga a ƙasar ya ɗan yi tasiri a raguwar da aka samu a yawan hare-haren da ake kaiwa a ƙasar, amma duk da haka akwai buƙatar sake duba alamuran da suka haifar da matsalar tun farko wanda suka haɗa da taɓarɓarewar tattalin arziki, da ƙalubalen muhalli da kuma matsalolin da suka jiɓanci shigabanci na gari.

  12. Ba za mu lamunci shara ta mamaye birnin Kano ba - Hashim

    ...

    Asalin hoton, fb/Dr Hashim

    Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da wani gagarumin shirin yaƙi da matsalar shara da ke addabar sassan birnin.

    Shirin na haɗin gwiwa da ma’aikatun ciniki da sufuri zai tabbatar da kwashe sharar da ta cika wuraren da ake tattara ta a kasuwanni da kuma unguwanni.

    Jihar Kano na cikin jihohin da matsalar shara ke ci gaba da barazana a tituna da kuma unguwanni inda a wasu wuraren hayaƙin da ake kona bolar ke mummunar barazana ga jama’a.

    Ma’aikatar kula da muhalli ta jihar Kano ta tabbatar da cewa aikin kawar da sharar zai gudana ne ƙarƙashin wani shirin haɗin gwiwa na kar-ta-kwana wanda zai tabbatar da cewa tulin sharar da ake fama ta shi a sassan jihar an kawar da shi cikin ƙanƙanin lokaci.

    Kwamishinan ma’aikatar, Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce yanzu aiki an faro shi daga kasuwanni zuwa cikin unguwanni.

    "Akwai abubuwa da dama da gwamnati ba za ta ci gaba da lamunta ba don tabbatar da tsaftar muhalli da kare lafiyar al’umma."

    Bu-gu-da-kari Dr Dahiru Muhammad Hashim ya ce za su gayyato kamfanoni su zuba jari a harkar sarrafa shara, ta yadda jama’a za su daina kallon ta a matsayin shara, maimakon haka su kalleta a matsayin wani abu da za a iya samun arziki a cikinsa.

  13. Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta gabatar da sabon kocin Super Eagles

    ...

    Asalin hoton, X/Super Eagles

    An gabatar da Eric Sekou Chelle a matsayin sabon kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (Super Eagles).

    Wannan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta sanar da zaɓen Chelle a matsayin sabon kocin babbar ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya, daga cikin mutane da dama da suka nemi muƙamin.

    A yanzu Eric Chelle, ɗan asalin ƙasar Mali, ya zama mai horas da ƙungiyar na 37 a tarihinta.

    Sabon kocin shi ne zai maye gurbin Bruno Labbadia, ɗan asalin ƙasar Jamus, wanda naɗinsa bai je ko ina ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  14. An zargi mutane 64 da yi wa wata matashiya fyaɗe a India

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata matashiya ƴar shekara 18 daga jihar Kerala da ke kudancin Indiya ta zargi wasu maza 64 da yin lalata da ita tun tana da shekaru 13 da haihuwa.

    Ƴansanda sun kama mutane 28 da ake zargi da hannu a lamarin kawo yanzu - mutanen suna tsare kuma ba su yi wani bayani kan lamarin ba.

    Waɗanda ake tuhumar da ke da shekaru tsakanin 17 zuwa 47, sun haɗa da makwabtan matashiyar da kociyoyin wasanni da abokan mahaifinta, kamar yadda ƴansanda suka shaida wa BBC.

    Matashiyar ta ba da rahoton cin zarafin da ta ke zargin an yi ma ta ne bayan wata tawagar masu ba da shawara da ke aiki ƙarƙashin wani shiri na gwamnati sun ziyarci gidanta.

    Lauyan da ke jagorantar kwamitin kula da jin daɗin yara na gundumar, ya shaida wa jaridar Indian Express cewa matashiyar ƴar wasa ce kuma ta halarci sansanonin wasanni daban-daban.

    Ƴansanda sun ce ana zargin cewa an yi wa matashiyar fyaɗe sau uku a cikin shekaru biyar da suka gabata.

  15. Za mu yi bincike kan harin jirgin da ya 'kashe' ƴan sintiri a Zamfara - Sojoji

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Air Force HQ/Facebook

    Rundunar sojin saman Najeriya ta ce tana gudanar da bincike kan wasu rahotannin da suka ce an kashe fararen hula a yayin wani harin da aka kai a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar a karshen makon da ya gabata.

    Wata sanarwa da ta fito daga ofishin darektan sashen hulɗa da jama'a da yaɗa labarai na rundunar, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ta ce an kai harin ne kan wasu ƴan bindiga a yankin Tungar Kara da ke ƙaramar hukumar Zurmi a jihar ta Zamfara inda aka yi nasarar kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa, duk da ya ke harin ya yi nasarar tarwatsa wani sansanin ƴanbindiga da suka addabi yankin, rundunar ta nuna matuƙar damuwa kan rahotannin rashin rayukan fararen hula da aka samu inda ta ƙara da cewa tana kan gudanar da bincike kuma za a sanar da sakamakon hakan da zaran ya kammala.

    Ta kuma bayar da tabbacin cewa zata ci gaba da ɗaukar matakai da za su tabbatar da cewa an kiyaye rayukan fararen hula a yayin da ta ke ƙokarin tabbatar da ingantaccen tsaro a sassan ƙasar.

    A ranar Lahadin da ta gabata ne dai mazauna yankin na Tungar Kara suka ce aƙalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon harin sojoin, ciki ma har da ƴan sintirin da ke ƙoƙarin yaƙar ƴanbindigan.

    A cikin watan Disamba aƙalla mutane 10 ne suka mutu a lokacin da wani jirgin yaƙin soji ya kai hari bisa kuskure kan wasu fararen hula a jihar Sokoto da ke yankin arewa maso yammacin ƙasar.

  16. An ƙara wa Shugaban Koriya ta Kudu da aka tsige albashi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Koriya ta Kudu da aka dakatar, Yoon Suk Yeol, zai samu ƙarin albashinsa na shekara-shekara duk da tsige shi da aka yi bayan ya yi yunƙurin kafa dokar mulkin soji a ƙasar.

    Albashin Yoon zai ƙaru da kashi 3% zuwa $179,000 wanda ya yi daidai da ƙa'idojin aikin gwamnatin ƙasar.

    Tun bayan tsige shi a watan Disamba, Yoon yake kaucewa duk wani yunƙurin kama shi da masu bincike na ƙasar suka yi, lamarin da ya jefa ƙasar cikin ruɗanin siyasa.

    Duk da an dakatar da shi daga aiki, Yoon na ci gaba da riƙe muƙaminsa har sai kotun tsarin mulki ta Koriya ta Kudu ta amince da tsige shi.

    Labarin ƙarin albashin da aka yi wa Yoon ya janyo suka daga ƴan Koriya ta Kudu, waɗanda ke mamakin cewa har yanzu ana ma biyansa albashi, har ma da yi masa ƙarin albashi, yayin da aka dakatar da shi.

    Wasu a shafukan sada zumunta sun yi nuni da cewa ƙarin albashin Yoon na kashi 3% ya kusan ninka na ƙarin mafi ƙarancin albashin da aka yi wa sauran ma'aikatan gwamnatin ƙasar.

  17. Rikicin shugabanci ya janyo zanga-zanga a ofishin jam'iyyar PDP

    Jam'iyyar PDP na fama da rikicin cikin gida

    Asalin hoton, PDP

    Gomman masu zanga-zanga sun yi dafifi a shelkwatar jam'iyyar PDP ta ƙasa da ke Abuja domin nuna rashin amincewa da kama aikin sabon sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sunday Ude-Okoye wanda kotun ɗaukaka ƙara ta ayyana a matsayin sakataren jam'iyyar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.

    Bayanai sun nuna cewa shelkwatar jam'iyyar ta tafi hutun ƙarshen shekara ne a watan Disamba inda kuma a ranar Litinin ake sa ran komawa aiki ranar da sabon sakataren zai kama aiki.

    To sai dai masu zanga-zanga da ke goyon bayan senator Sam Anyanwu wanda ake taƙaddama a kansa sun mamaye ƙofar ofishin inda suke ta ihun cewa " ofishin sakataren jam'iyyar PDP na ƙasa akwai mai shi kuma senator Anyanwu ne sakataren."

    A baya-bayan nan ne dai kotun ɗaukaka ƙara ta Enugu ce ta ayyana cewa Sunday Ude-Okoye ne sakataren jam'iyyar halastacce.

    An jibge jami'an tsaro a ƙofar shelkwatar jam'iyyar.

  18. An saki ƴar Tanzania da aka kama a Kenya

    ...

    Asalin hoton, X/Amnesty International

    Fitacciyar yar gwagwarmayar Tanzania Maria Sarungi Tsehai da wasu mutane dauke da makamai suka kama a Kenya ta ce an sako ta, sa’o’i bayan akuwar lamarin.

    Mai magana da yawun ƙungiyar Amnesty International a Kenya, Roland Ebole, ta shaida wa BBC cewa an tilasta mata shiga cikin wata mota a Nairobi babban birnin ƙasar a ranar Lahadi da yamma.

    Amma an sako Ms Tsehai bayan sa'o'i kaɗan. Ta wallafa bidiyo a shafinta na X inda ta ke da mabiya sama da miliyan ɗaya, Ta ce: "An cece ni." Ms Tsehai ta kasance mai sukar shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan, kuma ta zargi gwamnatinta da tabbatar da zalunci a ƙasar.

    Jami’an gwamnatocin Kenya da Tanzania dai ba su ce komai kan lamarin ba.

  19. Ukraine ta yi tayin musayar fursunonin yaƙi da sojojin Koriya ta Arewa da ta kama

    Zelensky

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya yi tayin mayar da wasu sojojin Koriya ta Arewa biyu da aka kama suna taimakawa Rasha, a madadin fursunonin yaƙi na Ukraine.

    Hotunan bidiyo da aka yaɗa a Internet sun nuna mutanen, da alama sun ji rauni.

    Wani daga cikinsu ya ce a iya saninsa, an tura shi yin atisaye ne, bai ma san cewa yaƙi suka je yi Ukraine ɗin ba.

    Mista Zelensky ya ce jami'an tsaron Ukraine na ci gaba da aiki da sojojin na Koriya Ta Arewa, inda ya ƙara da cewa ɗaya daga cikinsu ya nuna sha'awar ci gaba da zama, yayin da guda kuma ya nuna yana son komawa gida.

    "Don haka idan da gaske Kim Jong Un ya damu da mutanensa, to muna jiran ji daga gare shi."

  20. Ƴan fansho a Najeriya sun koka

    A Najeriya dubban ƴan fanshon gwamnatin tarayya ne ke kokawa kan yadda suka ce gwamnatin ƙasar ta watsar da su bayan sun sadaukar da ƙarfinsu da lokacinsu wurin bautawa ƙasar a aikin gwamnati.

    Sun ce duk da hakan, da ƙyar suke samun kuɗadensu na fansho a duk wata.

    Tsofaffin ma’aikatan sun ce suna zargin gwamnatin da kasa cika alƙawari ta hanyar wasa da hankalinsu inda duk da an yi wa ma’aikatan gwamnati ƙarin albashi amma su ba su san inda aka ajiye su ba.

    Malam Sulaiman Muhammad Ƙaura, tsohon ma'aikacin gidan rediyo tarayya, ya ce an daɗe ana ɗanɗana musu zuma a baki game da kuɗaɗensu domin su dara, amma sai su ji shiru.