Walker ya raba hankalin Inter da AC Milan, Araujo na son barin Barca

Kyle Walker

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kyle Walker
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

AC Milan na neman kammala siyan dan wasan baya na Manchester City Kyle Walker, Napoli na son dauko dan wasan gefe na Manchester United Alejandro Garnacho da kuma dan wasan baya na Barcelona Ronald Araujo yana son barin kungiyar.

Dan wasan baya na kasar Ingila Kyle Walker, mai shekara 34, na shirin rattaba hannu kan kwantiragin shekara biyu da rabi da AC Milan, inda ake sa ran zai bar Manchester City nan da yan kwanaki masu zuwa. (Telegraph)

Sai dai wasu rahotanni na cewa a maimakon haka Walker zai iya koma wa abokan hamayyar Milan Inter Milan a matsayin aro na tsawon kaka. (Mail)

Kungiyoyi daga Saudiyya sun ci gaba da nuna sha'awar siyan Walker, amma mai tsaron bayan yana sha'awar ci gaba da zama a Turai. (Sky Sports Germany)

Kocin Napoli Antonio Conte na son dan wasan gaban Manchester United Alejandro Garnacho, mai shekara 20, ya maye gurbin dan wasan gefe na Georgia Khvicha Kvaratskhelia, mai shekara 23, wanda da alama zai koma Paris St-Germain. (Sport Italia)

Dan wasan baya na kasar Uruguay Ronald Araujo, wanda ake alakanta shi da Juventus, yana son barin Barcelona da wuri-wuri, amma kungiyar ta Catalonia tana son ci gaba da rike dan wasan mai shekaru 25. (Mundo Deportivo)

Dan wasan baya na Jamus Mats Hummels, mai shekara 36, ba ya gaggawar fara tattaunawa kan tsawaita kwantiraginsa a Roma, inda kwantiraginsa zai kare a watan Yuni. (Football Italia)

West Ham a shirye take ta kawo sabon dan wasan gaba bayan Niclas Fullkrug, mai shekara 31, ya ji rauni a kafarsa, a wasan da suka doke Aston Villa a gasar cin kofin FA ranar Juma'a. (Fabrizio Romano)

Fullkrug zai yi jinyar watanni uku a West Ham. (Sky Sports Germany)

Monaco ta nemi dan wasan tsakiyar West Ham Edson Alvarez, mai shekara 27, bayan da Hammers ta ki amincewa da tayin daukar dan wasan na Mexico a matsayin aro. (Fabrizio Romano)

Dan wasan gaban Brighton na Jamhuriyar Ireland Evan Ferguson, mai shekara 20, da dan wasan gaban Manchester United na Ingila Marcus Rashford, mai shekara 27, dukkansu ana alakanta su da komawa West Ham a matsayin aro. (TBR Football)

Atalanta na son kammala siyan dan wasan Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 27 a watan Janairu, wanda aka alakanta shi da komawa Newcastle United a bazara. (Sun)

Bayern Munich ta yi wa dan wasan bayan Canada Alphonso Davies, mai shekara 24, tayin sabon kwantiragi na Yuro miliyan 25 (£21m) yayin da Real Madrid ta yi tayin siyan shi kyauta a bazara. (Marca Spanish)