Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 29/10/2024

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Annur Muhammad, Isiyaku Muhammed, Umar Mikail da Ahmad Bawage

  1. Gwamnati na ɗaukar matakan dawo da wutar lantarki - Majalisar dattawa

    Yayin da al’umma jihohin arewacin Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da rashin wutar lantarki na tsawon kwanaki, majalisar dattawan ƙasar ta ce gwamanti na ɗaukar matakai na tsaro wajen ganin an shawo kan matsalar.

    Majalisar dattawan ta ce hari da wasu ƴan bindiga masu iƙirarin jihadi suka kai kan turakun wutar lantarki ne ya jano matsalar da ake fama da ita a arewacin ƙasar.

    Tun da fari dai kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya TCN ya ce tangarɗa aka samu a layin lantarki na Ugwaji-Apir mai ƙarfin 330kV, wanda ya yi sanadiyar rashin wuta a arewacin ƙasar.

    Sanata Barau Jibrin shi ne mataimakin shugaban majalisar datijjan Najeriya, ya koka kan yawan lalacewar da babban layin lantarki na Najeriya ya yi har sau uku a baya bayan nan, wanda hakan ya sa suka fara tattaunawa da ɓangaren gwamanti domin ɗaukar matakai na koma amfani da wutar lanatarki mai amfani da hasken rana don magance wannan matsala.

  2. An zargi ƴar siyasa da yunƙurin kashe shugaban ƙasar Malawi

    An zargi wata ƴar siyasa, ɓangaren hamayya a ƙasar Malami da yunƙurin kashe shugaban ƙasar, Lazarus Chakwera.

    Patricia Kaliati, wadda ita ce sakatare-janar a jam'iyyar UTM, ta shiga hannu ne a makon jiya bisa zarginta da "haɗa baki da wasu domin aikata babban laifi."

    Da ta bayyana a kotu a jiya Litinin, ƴar siyasar mai shekara 57 ba ta ce komai ba, amma lauyoyinta sun musunta zargin da ake mata, kamar yadda kafofin sadarwa a ƙasar suka ruwaito.

    Wasu dai suna zargin cewa kama ta da aka yi ba ya rasa nasaba da bambamcin siyasa.

    Alƙalin kotun ya amince ya bayar da belin Kaliati, duk da cewa mai gabatar da ƙara ya buƙaci a riƙe ta zuwa mako mai zuwa.

    A ɓangaren ƴansanda kuwa, sun ce suna aiki ne da doka, kuma za su kiyaye dukkan haƙƙinta.

  3. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.