Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Alhamis, 05-12-2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da Abdullahi Bello

  1. Gwamnatin Jigawa ta karrama gwarzuwar Hikataya ta BBC Hausa

    Gwarzuwar Hikayata ta BBC Hausa
    Bayanan hoto, Gwarzuwar Hikayata ta BBC Hausa

    Gwamnatin jihar Jigawa, ta karrama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024, Hajara Ahmed Hussain.

    A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Duste, Gwamnan jihar Malam Umar Namadi, ya bai wa gwarzuwar kyautar kuɗi naira miliyan biyu da kuma ɗaukar nauyin karatunta na digiri.

    An yi bikin karramawar ne a gaban kwamishinoni da iyaye da kuma ƴaƴanta biyar.

    Hikayata

    A ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata Hajara Ahmed Hussaini ta zama gwarzuwar gasar gajerun ƙagaggun labarai da BBC Hausa ke shiryawa, wato Hikayata.

    Inda ta samu kyautukan kuɗi da lambar yabo daga BBC Hausa, da ma wasu mahalarta taron.

    Hajara ta zo da ɗaya a gasar ne da labarinta mai take 'Amon 'Yanci'.

    • Hikayata 2024: Hajara Ahmad Hussain ce ta lashe gasar rubutu ta BBC Hausa
    Hikayata
  2. Lakurawa ne suka dasa bam ɗin da ya fashe a Zamfara - Ƴansanda

    Zamfara

    Asalin hoton, Channels TV

    Rundunar ƴansandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ƙungiyar 'yanbindiga ta Lakurawa ne suka dasa bam ɗin da ya tashi ranar Laraba kan hanyar zuwa garin Ɗansadau da ke ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara.

    Kwamishinan ƴansandan jihar Muhammad Dalijan shi ya bayyana haka a wani shirin gidan talbijin na Channels mai suna Sunrise Daily, inda ya ce sauran ƴan ƙungiyar da da sojoji suka fatattaka a Sokoto da Kebbi, sun koma kafa sabbin sansanoni.

    "Lokacin da suke wucewa ta ƙauyen zuwa Birnin-Gwari, sai suka dasa bam ɗin karkashi wata gada. Inda wata motar fasinja ta taka nakiyar. Nan da nan bam ɗin ya tashi tare da kashe direban da kuma raunata wasu mutum uku," in ji Dalijan.

    Kwamishinan ƴansanda ya ce an ga mambobin ƙugiyar a wurin da lamarin ya faru jim kaɗan kafin tashin bam ɗin.

    Dalijan ya ce dasa abubuwan fashewa wata sabuwar hanya ce ta kai hare-hare a jihar da ke arewa maso yammacin Najeriya.

    Ya ce duk da cewa Zamfara ta daɗe tana fama da matsalar ƴan bindiga, sai dai ba su da karfin dasa abin fashewa.

  3. Mutum 12 sun mutu a hatsarin mota a Yobe

    Hatsarin mota

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum 12 sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam a jihar Yobe a daren Talata.

    Mutanen sun ƙunshi maza goma da mace ɗaya da kuma wata 'yar ƙaramar yarinya ɗaya, kamar yadda shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasar, reshen jihar Yobe, Livinus Yilzoom ya bayyana a wata sanarwa ga manema labarai, a babban birnin jihar, Damaturu.

    Kwamandan ya ce haɗarin ya faru ne da misalin ƙarfe goma na daren Talata a ƙauyen Chelluri mai nisan kilomita 20, a kan hanyar Bayamari zuwa Geidam.

    Ya ce haɗarin ya afku ne lokacin da motar da mutanen da suka rasu ke ciki, kirar Sharon ta yi garu da wata babbar mota ƙirar Howo ta wani kamfanin aikin gine-gine wadda take tsaye a hanya.

    Mista Yilzoom, ya ce karon da Sharon ɗin ta yi ne ta kama da wuta kuma mutanen da ke cikinta suka ƙone har ta kai ba za a iya gane su ba.

  4. An gano gawar ɗan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da shi

    Itay Svirsky

    Asalin hoton, Hostage Families Forum

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an ƙwato gawar ɗaya daga cikin mutanen da ƙungiyar Hamas ta yi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban baran daga Gaza a wani samame na haɗin gwiwa da jami'an tsaro.

    A cikin watan Janairu, Hamas ta ce an kashe Itay Svirsky da Yossi Sharabi, a wani harin da Isra'ila ta kai ta sama.

    Rundunar ta ce tana ganin cewa Hamas ce ta harbe Svirsky jim kaɗan bayan mutuwar Sharabi a harin.

    Har yanzu ana tunanin akwai sauran mutum 96 da ake garkuwa da su a Gaza, inda ake hasashen 35 daga cikinsu sun mutu.

  5. An yanke wa mata da miji hukuncin kisa ta hanyar rataya a Jigawa

    Kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wasu ma'aurata hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin kashe wata mata mai suna Salamatu.

    Kotun ta ce ta same su da laifin kashe matar mai kimanin shekara 30, wadda suka zarga da mutuwar ɗansu sanadiyyar maita.

    Da yake yanke hukunci, mai sharia'a Ado Yusuf Birnin-Kudu, ya ce kotun ta same su da laifin aikata kisan, don haka ne ta yanke musu wannan hukunci.

    "Don haka wannan kotu ta yanke musu hukuncin ɗaurin shekara shida a gidan yari saboda laifin haɗa baki don aikata laifi da kuma kisa ta hanyar rataya saboda aikata kisan kai," in ji Ado.

    An dai fara zaman sauraron shari'ar tun shekara ta 2019, inda masu gabatar da ƙara suka gabatar da shaidu biyar da kuma rahoton bincike na lafiya.

    Kotun ta ce ta gamsu da hujjojin da aka gabatar, inda haka ne ma ya sa ta yanke wa ma'auratan da wasu ƴan uwansu biyu wannan hukunci.

    Yanzu dai suna da damar ɗaukaka ƙara cikin kwanaki 90.

  6. Daga Bakin Mai Ita tare da Humaira ta Daɗin Kowa

    Ummusalama Abubakar ɗaya ce daga cikin taurarin fim ɗin Daɗin Kowa na tashar Arewa 24.

    Haifaffiyar ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano, ta fito a matsayin Humaira a cikin fim ɗin da ta fi sharara da shi, amma ba shi ne fim ɗinta na farko ba.

    Ta faɗa wa BBC cewa fitowar da take fara tunawa a fim ɗin ita ce fitowarta ta farko, wadda ta haɗu da Nasir.

    Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
  7. Farashin Bitcoin ya zarce dala 100,000 a karon farko

    Bitcoin

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko a tarihi farashin kuɗin kirifto na Bitcoin ya ketare dala 100,000.

    Farashin Bitcoin dai na ci gaba da samun tagomashi tun bayan da Donald Trump ya lashe zaɓen shugaban Amurka a watan jiya.

    Ana hasashen cewa Trump zai sauƙaƙa ƙa'idojin da ke tattare da yadda ake gudanar da bitcoin, kuma ya yi alkawarin mayar da Amurka ta zama cibiyar kirifto ta duniya.

    A ranar Laraba, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya zaɓi Paul Atkins, wani babban ma'abocin kuɗin kirifto a matsayin shugaban hukumar SEC wadda ke kula da ɓangaren hada-hadar kuɗi na Amurka.

  8. An samu ƙaruwar gobara a Kano saboda shigowar hunturu

    Gobara

    Asalin hoton, TWITTER/@GBOYEGAKOSILE

    Hukumar kashe gobara a Kano ta ce an samu ƙarin tashin gobara a faɗin jihar sakamakon shigowar yanayin hunturu a wasu yankunan arewacin Najeriya.

    Kakakin hukumar Saminu Yusuf Abdullahi ya shaida wa BBC cewa kafin zuwan yanayin hunturun an samu raguwar tashin gobara a jihar - wadda ita ce cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar.

    Saminu Yusuf Abdullahi ya ce a watan Nuwamban da ya gabata kaɗai an samu tashin gobara a jihar har sau 43, sakamakon yadda mutane ke ƙara ta'ammali da wuta a lokacin na hunturu.

    ''Adadin ya ninka, domin a watan Oktaba an samu matsalar tashin gobara a Kano sau 24, amma sakamakon shigowar hunturu a watan Nuwamban adadin ya kai 43'', in ji shi

    Ya kuma ce daga shigowar watan Disamba, zuwa yanzu hukumarsu ta samu labarin tashin gobara har sau bakwai, zuwa yanzu.

    Haka kuma hukumar kashe gobarar jihar ta ce mutum uku sun mutu, yayin da aka yi asarar dukiya da ta kai naira miliyan 130, a cikin watan da ya gabatan sakamakon tashin gobarar.

  9. Bakuwar cuta ta kashe mutum 79 a Kongo

    Kongo

    Asalin hoton, AFP

    Aƙalla mutum 79 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar bakuwar cuta a Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar.

    Ma'aikatar lafiyar ta ce yawancin waɗanda suka mutu na tsakanin shekara 18 zuwa 15.

    Sama da mutum 300 ne suka kamu da cutar, inda alamomin cutar suka haɗa da tari da ciwon kai da kuma matsalar numfashi.

    An aika jami'an lafiya zuwa lardin Kwango, inda cutar ta fi kamari domin takaita yaɗuwar ta da kuma binciko yanayin ta.

    Wani shugaban al'umma a yankin, Cephorien Manzanza, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa al'amarin abin damuwa ne ganin ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutar.

    "Panzi wani ƙauye ne da ke nan, kuma ana samun matsalar samar da magunguna," in ji shi.

    Hukumar lafiya ta duniya (WHO) reshen Afrika ta faɗa wa BBC cewa tuni suka aika jami'an lafiya zuwa yankin domin ɗauko sumfurin mutane don zuwa a yi bincike.

    Hukumomi dai sun buƙaci mutane su kwantar da hankali sannan su rika wanke hannayensu da sabulu da guje wa shiga tarukan jama'a da kuma kaucewa taɓa jikin gawawwakin da mutu a cutar ba tare da izinin jami'an lafiya ba.

  10. Amnesty ta zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar kare hakkin ɗan'adam ta Amnesty International ta zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi kan Falasɗinawa a Gaza.

    Ta ce Isra’ila ba ta mutunta rayukan Falasɗinawan Gaza ba, kuma ta ɗauki matakin ne da nufin halaka su.

    Agnès Callamard, sakatare janar ta ƙungiyar ta ce sun ruguza gidajen Falasɗinawa da abubuwan gudanar da rayuwarsu, sun kuma wargaza ababen more rayuwa da duk wata alaƙa da suke da ita da ƙasarsu.

    Isra'ila dai ta bayyana Amnesty International a matsayin ƙungiya mai tsatsaurar ra'ayi kuma ta ce an gina rahoton ne kan bayanai na ƙarya.

  11. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.