Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin da muke kawo muku labarai kai-tsaye na yau Alhamis.
Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye - Alhamis, 05-12-2024
Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da Abdullahi Bello
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafin da muke kawo muku labarai kai-tsaye na yau Alhamis.
Da fatan kun ji daɗin kasancewa da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Sabon shugaban ƙungiyar Hezbollah, ya ce ƙungiyarsu za ta goyi bayan gwamnatin Syria a yayin da masu tayar da ƙayar baya ke ci gaba da faɗaɗa ayyukansu a ƙasar.
Cikin wani saƙo da aka naɗa, Naim Qassem, ya ce hare haren da ƴan tawayen ke kai wa Syria Amurka da Isra'ila ne suka kitsa su.
Hezbollah na taka muhimmiyar rawa wajen kasancewar shugaba Bashar al- Assad a kan mulkin Syria.
Sai dai ana ganin hare-hare ta ƙasa da sama da Isra'ila ke kai wa Lebanon, ya rage wa Hezbollah ƙarfi.
Ƙungiyar malaman jami'a ASUU, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta guji yin duk wasu abubuwa da za su kassara asusun bayar da tallafi ga manyan makarantu ta Najeriya wato TETFUND.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da tashar talabijin ta Channels, inda ya yi zargin cewa matakin, "zai kassara jami'o'in Najeriya, da kuma bautar da yaran talakawan ƙasar."
"Hanyar jami'o'in Najeriya suke samun kuɗi ita ce TETFund, don haka idan ka taɗile ta, kamar ka taɗiye jami'o'in Najeriya ne," in ji shi.
Shugaban na ASUU ya ce ƙudurorin harajin da Tinubu ya kawo, ba a yi shawara da masu ruwa da tsaki a ɓangaren ilimi ba kafin a tura majalisa.
"Gwagwarmayar ASUU ce ta samar da TETFund. Bai kamata a yi ƙudurorin haraji ba, ba tare da an nemi shawarar ASUU ba. Kuma ba a nemi shawarar shugabannin jami'o'i ba. Wasu ne kawai suka zauna a wani wurin suka shirya dokokin nan. Ba haka ya kamata a yi ba, musamman a mulkin dimokuraɗiyya," in ji shi.
Osodeke ya ce maimakon a ce za a cire kuɗaɗen da ake ba TETFund domin a inganta asusun ba ɗalibai lamuni wato NELFUND, gara a nema wa asusun na NELFUND kuɗi daga kuɗin harajin VAT.
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar lll, ya ce musulunci ba ya hana yara mata karatu.
Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a jihar Bauchi a wajen taron shirin inganta ilimin mata na AGILE, wanda ma'aikatar ilimi ta jihar Bauchi ta haɗa tare da babban bankin duniya.
An yi taron ne a ƙarƙashin taken: "kawo ƙarshen abubuwan da suke hana mata zuwa makaranta a arewa maso gabas: Rawar da sarakunan gargajiya da malaman addini za su taka."
Sarkin Musulmin ya ce, "Musulunci ba ya hana yara mata neman ilimi. Akwai wasu abubuwan da suke kawo musu tsaiko wajen neman ilimi. Da nake hanyata ta zuwa nan, na ga ƙananan yara suna talla a titi. Da na tambaye su, sai suka faɗa min cewa akwai makarantar safe da ta yamma.
"Karatun yara mata na da muhimmanci saboda su ne za su ilimantar da iyalinsu da al'umma," in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A ƙarshe ya yi kira ga gwamnonin arewa su ƙara zuba kuɗaɗe a ɓangaren ilimi domin ilimantar da yara mata da maza na yankin.
Sanatoci daga yankin kudu maso kudu na kudancin Najeriya sun bayyana goyon bayansu da ƙudurorin haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya tura majalisa.
Sanatocin, sun bayyana cewa ƙudurorin harajin za su taimaka wajen inganta tattara kuɗin shiga, da inganta tattalin arzikin Najeriya.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar sanatocin, Sanata, Senator Seriake Dickson (PDP, Bayelsa West), ya sanya wa hannu, sun ce za su yi duk mai yiwuwa domin ganin ƙudurorin sun zama masu amfani da ƙasar, musamman mutanen yankin kudu maso kudu, kamar yadda shafin intanet na Channels ya ruwaito.
Sun kuma yi kira ga gwamnonin yankin su yi aiki tare da ƴanmajalisar yankin domin yi wa ƙudurorin garambawul domin su yi daidai da buƙatun mutane, sannan suka ce a cire bambancin addini ko ƙabila domin tattauna batun.
A nan mataimakin shugaban ƙasar Ghana, Mahamudu Bamuwua na jam’iyyar NPP ne ya gudanar da taron gangamin rufe yaƙin zaɓensa na ƙarshe.
Majalisar dattawa ta ce za ta ci gaba da tattauna batun ƙudurorin haraji, domin ba ta dakatar da su ba.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana hakan a majalisar a ranar Alhamis, inda ya ce majalisar za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin kare muradun ƴanƙasar ba tare da tsoron komai ba.
Akpabio ya yi wannan jawabin ne bayan shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele, ya janyo hankalin majalisar kan maganar da ake yaɗawa cewa sun dakatar da tattaunawa game da ƙudurorin, wanda hakan ya sa Akpabio ya musanta, kamar yadda shafin intanet na Channels ya ruwaito.
"Babu wanda zai tursasa majalisar dattawa. Duk wata gyara da muke tunani za ta yi amfani ga ƴanƙasar nan, za mu yi aiki a game da ita. Waɗannan ƙudurorin suna ɗauke da abubuwa masu amfani ga Najeriya."
Akpabio ya ce ba sauri suke yi ba, don haka ya ce za su yi aiki a tsanake kan ƙudurorin kafin ɗaukar wani mataki.
Ya ce taron masu ruwa da tsaki da za a yi a nan gaba ne zai bayar da dama domin tattaunawa tare da nemo hanyoyin da za a magance duk matsalar da ake fargaba suna cikin ƙudurorin.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar ceto mutum 25 da aka yi garkuwa da su a kudancin Kaduna ranar Laraba bayan fatatttakar ƴanbindiga
Wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na dandalin X, rundunar ta ce an gudanar da aikin mai taken Golden Peace ne domin manoma su samu sukunin girbe gonakinsu, sannan a samar da yanayi mai kyau domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Daga cikin yankunan da aka yi aikin akwai Ruwan Sanye da Randa da Rafin Gora da Libere Gari da Libere Makaranta da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Haka kuma sojojin sun gano wani ƙaramin asibiti, inda ake jinyar ƴanbindiga idan sun ji raunuka.
Gwamnatin jihar Jigawa ta karrama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024, Hajara Ahmed Hussain, inda ta ɗauki alƙawarin ɗaukar nauyin karatunta na jami'a.
Yayin wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Duste domin taya ta murnar lashe gasar ta bana, Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya ba ta kyautar naira miliyan biyu.
An yi bikin karramawar ne a gaban kwamishinoni da iyaye da kuma ƴaƴanta biyar, inda ya ƙara da cewa.
"Bayan karatun digirin, idan ma za ta ci gaba za mu ɗauki nauyinta," a cewar gwamnan.
A ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata ne Hajara Ahmed Hussaini ta zama gwarzuwar gasar ta gajeru kuma ƙagaggun labarai da BBC Hausa ke shiryawa.
Hajara ta zo ta ɗaya a gasar ne da labarinta mai suna "Amon 'Yanci".
Jagoran ƙungiya mai rajin tabbatar da dimokraɗiyya a Arewa (Arewa Democrats League), Malam Ibrahim Shekarau ya roƙi shugaba Bola Tinubu da ya yi ganawar sirri da mataimakinsa, Kashim Shettima da kuma gwamnoni don ɗinke ɓarakar da ya ce ta ɓulla a tsakaninsu game da ƙudurin gyara dokokin haraji a Najeriya.
Shekarau ya yi iƙirarin cewa duka ɓangarorin sun tafka kuskure, abin da kuma ya kunna wutar rashin yarda tsakanin su da waɗanda suke mulka.
Ya ce ƙungiyarsu ta kafa kwamitin ƙwararru don samun kyakkyawar fahimta kan ƙudurin gyara dokokin harajin.
Ƙaruwar ayukkan haƙar zinare ba bisa ƙa’ida ba, wanda yake gurɓata ruwan koguna da lalata gonakki musamman na cocoa da haddasa cututuka ga mutane zai kasance babban ƙalubale ga duk wanda zai kasance shugabanta na gaba.
Domin kuwa tun gabanin zaɓen ya kasance wani batu mai santsi da kowane ɗan takara ke kaffa-kaffa da shi wajen yaƙin neman zaɓe.
Galibin talakawan ƙasar dai na son a kawo ƙarshen wannan safara da ake kira galamsey, amma ƴan siyasa na yin alƙawarin hakan ba tare da cikawa ba saboda yadda ake zargin manyan masu samar wa da jam’iyyun siyasa da kuɗaɗe na amfana da harkar.
Ma'aikatan da suka fi fuskantar haɗari a Saliyo ciki har da jami'an lafiya, za su zama na farko da za a yi wa allurar riga-kafin cutar Ebola a wani ɓangare na gangamin yaƙi da cutar.
Wannan zai kasance yunkuri na farko da za a yi a yammacin Afrika tun bayan ɓullar annobar shekaru 10 da suka wuce.
Sauran waɗanda za a yi wa allurar riga-kafin sun haɗa da jami'an tsaro da shugabannin addini da kuma direbobin manyan motoci.
Saliyo ta yi fama da annobar ta Ebola a 2014, lamarin da ya sa ta rasa kashi bakwai cikin 100 na jami'an lafiyarta.
'Yanmajalisar Wakilan Najeriya biyar sun sauya sheƙa daga jam'iyyar Labour Party (LP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulkin ƙasar.
Wakilan da suka sauya jam'iyyar a zaman majalisar na yau Alhamis su ne: Esosa Iyawe (jihar Edo), Tochukwu Okere (Ijihar mo), Donatus Matthew (jihar Kaduna), Bassey Akiba (jihar Cross River), Daulyop Fom (jihar Filato).
Sai kuma Erhiatake Ibori-Suenu (jihar Delta), wadda 'yar tsohon gwamnan jihar ce, James Ibori, da ita ma ta fice daga PDP zuwa APC ɗin.
'Yanmajalisar sun ce rikicin shugabanci da jam'iyyar tasu ke fama da shi ne dalilin da ya sa suka fice daga cikinta.
Ɗantakarar LP Peter Obi, shi ne ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da aka gudanar, abin da ya jawo wa jam'iyyar tagomashi karon farko cikin kusan shekara 20.
Al'ummar Ghana za su kaɗa ƙuri'a ranar Asabar domin zaɓen shugaban ƙasa, shin waɗanne abubuwa ne suka fi tayar da ƙura?
Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a ƙasar Ghana, Irbaɗ Ibrahim ya yi mana ƙarin haske.
An fi raɗa wa jarirai maza sabbin haihuwa sunan Muhammad a Ingila da kuma Wales a shekara ta 2023, inda aka saka wa kusan jarirai 4,600 sunan.
Sunan ya kasance cikin jeri na sunaye 10 da aka raɗa wa ƴaƴa tun 2016, sai dai a yanzu ya sha gaban sunan Noah, da a baya aka fi saka wa yara, a cewar hukumar kididdiga ta ƙasar (ONS).
Sai dai hakan ya bambanta a wasu yankuna, inda sunan na Muhammad bai fito a jeri na 10 ba a wasu yankuna uku na Ingila.
Hukumar ta kuma ce an fi saka wa jarirai mata sunan Olivia, sai kuma Amelia da Isla.
Ta ce ba a samu sauyi kan haka ba tun 2022.
Masu sharfi na ci gaba da bayyana yadda Arsenal take ƙara zama hatsari a yayin da ta samu bugun kwana, har suna kwatanta ta da Stoke City da ta yi shuhura wajen cin kwallo da kwana.
BBC ta yi nazari tare da fitar da ƙididdiga kan yadda Arsenal ta ɗauki kambun cin ƙwallo da kwana.
Arsenal ta ci kwallo 22 da bugun kusurwa tun farkon fara kakar 2023-24, kwallo bakwai sama da Manchester City da take biye mata a Premier.
Rundunar sojin Syria ta ce ta janye dakarunta daga birnin Hama wanda ƴan tawaye masu iƙirarin jihadi ke iko da shi.
Rundunar ta ce dakarunta sun fice ne bayan gwabzawar da aka yi inda aka tura su don su je su kare rayukan fararen hula a yankin.
Ƴan tawayen sun ce sun kwace ikon gidan yarin Hama inda suka saki ɗaruruwan fursunoni da ake tsare da su a ciki.
Sun kuma fara yunkurin kwace ikon Hama ne kwanaki biyu da suka wuce.
Kwace birnin Aleppo da aka yi a makon da ya wuce ya zo da mamaki inda ƴan tawayen suka shammaci mutane.
Ƙaruwar ayukkan haƙar zinare ba bisa ka’Ida ba wanda yake gurɓata ruwan koguna da lalata gonaki musamman na cocoa da haddasa cututuka ga mutane, zai kasance babban kalubale ga duk wanda zai kasance shugabanta na gaba.
Tun gabanin zaɓen, lamarin ya kasance wani batu mai da kowane ɗan takara ke kaffa-kaffa da shi wajen yaƙin neman zaɓe.
Galibin talakawan ƙasar dai na son a kawo karshen wannan safara da ake kira galamsey.
Sai dai ƴan siyasa na yin alkawarin hakan ba tare da cika wa ba saboda yadda ake zargin manyan masu samarwa da jam’iyyun siyasa da kuɗaɗe na amfana da harkar.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan ta'dda 8,034 daga farko zuwa ƙarshen shekara ta 2024.
Wata sanarwa da darektan yaɗa labarai na rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar, ta ce an samu nasarar ne a samame daban-daban da sojoji suka kai yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma da arewa maso tsakiya da kuma sauran yankunan ƙasar.
Ya ce an kama wasu 'ƴan ta'dda' 11,263 da kuma ceto mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su.
"Mun kuma samu nasarar ƙwato makamai 8,216 da harsasai 211,459. Mun kuma daƙile yunkurin satar ɗanyen mai da kuɗinsa ya kai sama da naira biliyan 57," in ji Buba.
Sai dai duk da irin waɗannan nasarori da rundunar sojin ke ayyanawa, Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro a yankuna daban-daban na ƙasar.
Ko a cikin kwanakin nan an samu ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ƴan bindiga arewa maso yammacin Najeriyar, waɗanda ake kira Lakurawa.
Haka nan ma a baya-bayan nan ƙungiyoyin ƴan bindiga sun riƙa dasa nakiyoyi a kan hanyoyin mota a jihar Zamfara, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.
Jihar Assam da ke arewacin Indiya ta haramta cin naman shanu a bainar jama'a, ciki har da wuraren sayar da abinci da kuma taruka.
Wannan ɗai ƙari ne kan wata doka da ta takaita sayar da naman na shanu a kusa da wuraren bauta, kamar yadda babban minista Himanta Biswa Sarma ya bayyana ranar Laraba.
Sai dai, duk da haka za a iya sayan naman daga kantuna a kuma iya cinsa a gidaje ko hukumomi masu zaman kansu a jihar.
Cin naman sa dai wani abu ne zai iya tayar da hargitsi a Indiya, kasancewar ana girmama shanu musamman ma ƴan addinin Hindu, waɗanda suka kai kashi 80 na yawan al'ummar ƙasar.
Jihohi da dama da jam'iyyar Firaminista Narendra Modi ta BJP ke mulka -wadda ke da iko a jihar ta Assam - sun saka tsauraran dokoki kan yanka shanu a shekarun baya-bayan nan.
Kusan kashi biyu bisa uku na jihohin Indiya 28, yawancin waɗanda jam'iyyar BJP ke mulka, sun haramta yanka shanu da cin naman sa baki-ɗaya ko kuma a wasu wurare.
Ana dai zargin ƙungiyoyin bijilanti masu kula da shanu da tirsasa haramcin ta hanyar tayar da rikici, abin da a wasu lokuta ke janyo munanan hare-hare kan Musulmi masu sayar da naman shanu da kuma kasuwancin dabbobu.