Gwamnatin Jigawa ta karrama gwarzuwar Hikataya ta BBC Hausa
Gwamnatin jihar Jigawa, ta karrama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024, Hajara Ahmed Hussain.
A wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke birnin Duste, Gwamnan jihar Malam Umar Namadi, ya bai wa gwarzuwar kyautar kuɗi naira miliyan biyu da kuma ɗaukar nauyin karatunta na digiri.
An yi bikin karramawar ne a gaban kwamishinoni da iyaye da kuma ƴaƴanta biyar.
A ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata Hajara Ahmed Hussaini ta zama gwarzuwar gasar gajerun ƙagaggun labarai da BBC Hausa ke shiryawa, wato Hikayata.
Inda ta samu kyautukan kuɗi da lambar yabo daga BBC Hausa, da ma wasu mahalarta taron.
Hajara ta zo da ɗaya a gasar ne da labarinta mai take 'Amon 'Yanci'.
- Hikayata 2024: Hajara Ahmad Hussain ce ta lashe gasar rubutu ta BBC Hausa