Yadda kwanar Arsenal ta zama hatsari a kwallon nahiyar Turai

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Masu sharfi na ci gaba da bayyana yadda Arsenal take ƙara zama haari a yayin da ta samu kwana, har suna kwatanta ta da Stoke City da ta yi shuhura wajen cin kwallo da kwana.

BBC ta yi nazari tare da fitar da ƙididdiga kan yadda Arsenal ta ɗauki kambun cin ƙwallo da kwana.

Arsenal ta ci kwallo 22 da kwana tun farkon fara kakar 2023-24, kwallo bakwai sama da Manchester City da take biye mata a Premier.

Jadawalin yawan cin kwallo da kwana a Premier

A faɗin manyan gasar Turai biyar kuwa, Arsenal ita ce ke sama da kwallo biyar tsakaninta da Leverkusen da take biye mata da 17.

A wannan kakar ƙungiyar ta Mikel Arteta ta ci kwallo 30 daga abubuwa irin kwana da jifa da bugun daga kai sai mai tsaron gida, hakan ya ɗau kashi 25.2 cikin kwallo 119 da suka ci a lig.

Declan Rice da Bukayo Saka sun sun fi kowa ba da kwallo a ci a irin wannan yanayi inda kowa ya ba da bakwai.

Jadawalin yawan cin kwallo da kwana a manyan gasar Turai