Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 18/08/2025.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida

  1. Mutum 44 sun ɓace bayan motar fasinja ta faɗa kogi a Jamhuriyar Benin

    Ana ci gaba da aikin gano mutane 44 da suka ɓace bayan wata motar bas ta faɗa cikin kogin Ouémé da ke tsakiyar ƙasar Jamhuriyar Benin.

    Motar mai ɗauke da fasinjoji 54 ta taso ne daga birnin Lomé na ƙasar Togo zuwa birnin Yamai na jamhuriyar Nijar a lokacin da ta faɗo daga saman wata gada.

    Yawancin fasinjojin ƴan ƙasashen Benin da Nijar ne.

    RAhotanni dai sun bayyana cewa fasinjoji 9 ne suka tsallake rijiya da baya inda aka gano gawar mutum ɗaya, sannan 44 suka ɓata.

    A cikin wata sanarwa, shugaban ƙasar Benin, Patrice Talon, ya bayyana alhininsa tare da miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan da bala'in ya shafa.

    Ya kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa matakan kiyaye hanyoyin ƙasar don hana afkuwar irin wannan mummunan lamari nan gaba.

    Shugaban ya kuma buƙaci kamfanonin sufuri da direbobi da su kiyaye dokokin ahnay tare da sanar da matakan da gwamnati za ta ɗauka na inganta bincike don tabbatar da lafiyar ababen hawa da kuma tilasta tsauraran mataka a kan titunan ƙasar.

  2. Shugaban Ghana ya yi wa fursunoni kusan 1000 Afuwa

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Ghana John Mahama ya yi afuwa ga fursunoni 998 da ke gidajen yari a sassa daban-daban na ƙasar.

    Shugaban ya yi amfani da ikonsa na jin kai na yin afuwa ga fursunonin bisa shawarar hukumar kula da gidajen yari da kuma tuntubar majalisar dokokin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, fursunoni tamanin da bakwai da aka yanke musu hukuncin kisa za a mayar da hukuncin ɗaurin rai-da-rai, yayin da fursunoni 51 da aka yi wa ɗaurin rai da rai za a sauya hukuncinsu zuwa ɗaukrin shekara 20.

    Fursunonin da aka ƴantar sun haɗa da mata masu shayarwa guda biyu da masu fama da rashin lafiya, da waɗanda laifin su na farko ke nan da kuma fursunoni da ke da sama da shekara 70, ba tare da la'akari da laifin da suka aikata ba.

    Hukumar kula da gidajen yari ta ba da shawarar sakin fursunoni 1,014 wanda daga ciki Shugaba John Mahama ya amince da 998.

  3. 'Ƴan Najeriyar da ke neman bizar Amurka za su gabatar da bayanan shafukan sada zumuntarsu

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta umarci duk ƴan Najeriya masu neman bizar shiga ƙasar sai ya samar da tarihin abubuwan da ya aikata a shafukan sada zumunta na shekara biyar a matsayin wani ɓangare na abubuwan da ake buƙata domin tabbatar da cancantarsa ta shiga Amurka.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya ce masu neman bizar da suka kasa bayyana tarihin abubuwan da suka aikata a shafukan sada zumunta na tsawon shekara biyar na fusknatar barazanar rashin samun bizar.

    “Ana buƙatar masu neman biza su jera duk sunayen da suke amfani da su a duk wani dandalin sada zumunta daga shekara biyar da suka gabata akan takardar fom ɗin neman biza ta DS-160.

    “Masu neman biza sai sun tabbatar da sahihancin bayanan da ke cikin takardar neman bizar ta su kafin su sa hannu a kai. Sanarwar ta ƙara da cewa "rashin bayar da bayanan da ake buƙata na iya haifar da rashin samun bizar a lokacin da da kuma sauran lokutan da za su biyo baya."

  4. Hotunan yadda Tinubu ya isa Japan taron ci gaban Afirka karo na tara

    Tinubu da hadiminsa lokacin da suke sauka daga jirgi

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa Japan domin halartar babban taron ci gaban Afirka karo na tara da za a gudanar a birnin Tokyo.

    Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasata ta fitar, ta ce jakadan ƙungiyar ci gaban ƙasashen Afirka, Ambasa Hideo Matsubara ne ya tarbi Tinubu yayin da ya sauka a birnin Yokohama.

    Shugaban na tare da ministar harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar.

  5. MDD ta Isar da tallafin abinci zuwa Arewacin Darfur

    ...

    Asalin hoton, WFP

    Shirin samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya shaida wa BBC cewa, jerin motocin da ke ɗauke da kayan tallafi sun isa yankin Arewacin Darfur na ƙasar Sudan, inda dubban ƴan gudun hijira ke buƙatar agajin gaggawa.

    Mutane da dama sun tsere daga babban birnin yankin, El Fasher, a ‘ƴan makonnin nan saboda tashin hankali da ke ƙara ta’azzara.

    Tallafin abincin ya kai tan 440, wanda za a raba ga mutum 50,000 da suka tsere daga El Fasher zuwa garin Al Malha.

    El Fasher shi ne birni na ƙarshe a Darfur da ke ƙarƙashin ikon dakarun gwamnati da abokan ƙawancensu.

    A ƴan makonnin nan, mutane da dama sun tsere daga El Fasher da kuma sansanin ƴan gudun hijira na Zamzam, wanda dakarun RSF suka mamaye.

    A halin yanzu, kimanin mutum miliyan 25 a Sudan na fama da rashin abinci saboda yaƙin basasan da ya addabi ƙasar.

    WFP ya ce yana buƙatar aƙalla dala miliyan 650 nan da ƙarshen shekara domin ci gaba da bayar da tallafin abinci a Sudan.

  6. Ƴantawayen M23 sun dakatar da tattaunawar sulhu da gwamnatin DR Congo

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar ƙungiyar ƴan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, M23, ta fice daga tattaunawar sulhu da ta ke yi da gwamnatin ƙasar, tana mai cewa ba za ta koma ba, sai dai idan mahukuntan ƙasar sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a baya.

    Faɗan da ake gwabzawa tsakanin ɓangarorin biyu ya yi ƙamari ne a cikin watan Janairu, lokacin da ƴan tawayen M23 suka ƙwace yankuna da dama da ke gabas masu arzikin ma'adinai, ciki har da Goma babban birnin yankin.

    A watan da ya gabata, ƴan tawaye da gwamnati sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, da nufin zama wani mataki na cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta dindindin.

    Sai dai a ranar Litinin, yayin da ake shirin ci gaba da tattaunawa, ƙungiyar ta M23 ta ce wakilanta ba za su halarci tataunawar ta Qatar ba.

    Mai magana da yawun ƙungiyar M23 Lawrence Kanyuka ya shaidawa BBC cewa gwamnatin Congo "ba ta son zaman lafiya".

    Ya zargi mahukuntan ƙasar da rashin mutunta sharuɗɗan da ke ƙunshe a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma, amma sojojin DR Congo sun musanta wannan zargi.

  7. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 15 a Pakistan

    Pakistan

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Aƙalla mutum 15 ake fargabar sun mutu a wata ambaliya da aka samu sakamakon mamakon ruwa da aka yi a yankin arewa maso yammacin Pakistan.

    Ambaliyar ta zo ne a daidai lokacin da yankin ke ƙoƙarin farfaɗowa daga mummunar yanayin da ya shiga ba a makon da ya gabata ba.

    Wani jam'in gwamnati ya ce ambaliyar ta mamaye gidage da dama, kuma ta tafi da wasu mutane a yankin Swabi da ke lardin Khyber Pakhtunkhwa.

    Wakiliyar BBC ta ce har yanzu ana ruwa a wasu yankunan, kuma ma'aikatan agaji na ganin akwai mutanen da suka maƙale cikin ɓaraguzai.

    Mutanen da suka mutu a Pakistan da Kashmir zuwa yanzu sun kai fiye da ɗari uku da talatin.

  8. Gobarar daji ta kashe mutum biyu a Sifaniya da Portugal

    ....

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Sifaniya ta ƙara tura sojoji 500 domin kashe gobarar da ta addabi yankunan inda adadin sojojin da aka tura ya kai 1,900, yayin da adadin mutanen da gobar ta kashe ya kai huɗu.

    A ranar Lahadi, wani mai aikin kashe gobara ya mutu sakamakon haɗari yayin aikin kashe gobara, bayan motarsa ta faɗi daga wani tsauni, in ji gwamnatin yankin Castile da León.

    Firaministan Sifaniya, Pedro Sanchez, ya bayyana "ƙunci da bacin rai" a shafinsa na X kan mutuwar da aka samu.

    Hakazalika a Portugal da ita ma ke fama da gobarar dajin, wani mai aikin kashe gobara shi ma ya mutu a ranar Lahadi wajen ƙoƙarin kashe gobarar", in ji Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa.

    Haka kuma gobar daji ta ɓarke a Girka da Faransa da Turkiyya da Balkans sakamakon tsananin zafin rana da ake samu a manyan yankuna na Kudancin Turai.

    Har yanzu akwai gobarar daji mai tsanani a Arewa maso Yamma na kuma Yammacin Sifaniya, inda a halin yanzu ana kwashe mazauna yankin wajen 27,000 daga gidajensu.

  9. Hamas ta amince da sabon ƙudurin tsagaita wuta a Gaza

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙungiyar Hamas ta amince da sabuwar ƙudurin da masu shiga tsakani na yankin suka gabatar na tsagaita wuta a Gaza wanda zai hada da yarjejeniyar sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su Gaza, in ji wata majiya daga ƙungiyar ta Falasdinawa.

    Majiyar ta shaidawa BBC cewa ƙudurin na Masar da Qatar an gina shi ne kan tsarin matakai biyu da wakilin Amurka Steve Witkoff ya gabatar a watan Yuni.

    Ƙudurin ya ƙunshi Hamas ta saki kusan rabin sauran Isra'ilawa 50 da aka yi garkuwa da su - 20 daga cikinsu da ake kyautata zaton suna da rai - a cikin rukunnai biyu yayin fara tsagaita wuta na kwanaki 60, yayin da kuma za a ci gaba da tattaunawa kan tsagaita wuta na dindindin.

    Ba a dai san ko mene ne martanin Isra'ila kan wannan ƙuduri ba, kamar yadda ofishin firaminista Benjamin Netanyahu ya ce a yanzu za ta amince da yarjejeniyar ne kawai idan "aka sako dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a lokaci guda".

    A cikin wani bidiyo da aka fitar bayan rahotannin amincewar Hamas sun bayyana, Netanyahu bai ce uffan ba kai tsaye ba amma ya ce yana da ra'ayin cewa ƙungiyar na fuskantar matsananciyar matsin lamba.

    A cikin makon nan ne ake sa ran majalisar ministocinsa za ta amince da shirin sojojin Isra'ila na mamaye birnin Gaza, inda hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa ya sa dubban Falasdinawa tserewa daga gidajensu.

    Firaministan ya sanar da aniyar Isra'ila ta faɗaɗa hare-hare tare da mamaye yankin Gaza - ciki har da yankunan da mafi yawan mazaunanta miliyan biyu suka nemi mafaka.

  10. Hukumar RMAFC ta Najeriya ta fara gyara kan rabon arziƙin ƙasa

    Shugaban Hukumar rarraba arziƙin ƙasa RMAFC, Mohammed Shehu, ya bayyana a Abuja cewa an fara aikin sake duba tsarin rabon kuɗaɗen shiga tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi.

    Ya ce tun daga 1992 aka yi karo na ƙarshe, kuma dole a yi gyara domin ya dace da halin tattalin arzikin yau da kuma nauyin kowace gwamnati.

    A tsarin da ake amfani da shi yanzu, gwamnatin tarayya na karɓar kashi 52.6. jihohi kuma 26.7, yayin da ƙananan hukumomi kuma ke da kaso 20.6.

    Haka kuma an ware kashi 1 ga kowanne da suka haɗa da FCT da asusun muhalli da albarkatun ƙasa da kuma asusun daidaita tattalin arziki.

    Shehu ya ce wannan mataki ya yi daidai da tanadin kuuɗin tsarin mulkin ƙasar, domin tabbatar da adalci da daidaito wajen rabon kuɗaɗen shiga.

  11. Masar ta soki Isra'ila kan kisan fararen hula da ke neman agaji a Gaza

    ..

    Ministan harkokin wajen Masar ya ce da gangan Isra'ila ke kai hari kan Falasɗinawa da ke zuwa karɓar agaji a zirin Gaza.

    Badr Abdel-Atty ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai wata ziyara a iyakar Rafah da Gaza tare da Firaministan Falasɗinawa.

    Firaminista Muhammad Mustafa ya ce akwai buƙatar ƙasashen duniya su ƙara matsa lamba kan isra'ila ta bayar da damar shigar da ƙarin agaji Gaza.

    Wakiliyar BBC ta ce Isra'ila na musanta zargin da ƙungiyoyin agaji fiye da 100 suka yi na cewa tana hana su shigar da agaji da gan gan, inda ta ɗaura laifin kan ƙungiyoyin da kuma Hamas.

  12. An ceto mutum 25 daga cikin waɗanda suka ɓace a haɗarin kwale-kwale a Sokoto

    Sokoto

    Asalin hoton, National Emergency Management Agency (NEMA) Nigeria

    Hukumomi a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya sun ce sun samu nasarar ceto mutum 25 da ransu daga cikin waɗanda suka ɓace a haɗarin kwale-kwale da ya auku a ƙauyen Kojiyo da ke ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar.

    Haɗarin ya auku ne a lokacin da mutum 50 suke hanyar tafiya babbar kasuwar Goronyo da ke Sokoto, inda tun a farko aka ceto mutum 10.

    Wani kansila da ke yankin ya bayyana wa BBC cewa har yanzu ana neman sauran mutum 25.

    "Mutum 50 ne a kwale-kwalen da babura 7 da wasu buhunan kayan abinci. An ceto mutum 25 zuwa yanzu, sannan ana ci gaba da neman sauran 25 ɗin," in ji Aminu Bare.

    Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Sokoto, Aminu Liman ya shaida wa BBC cewa an tura ƙwararrun masu aikin ceto domin su higa kogin domin ceto sauran waɗanda suka rage.

  13. Amurka ta yaba wa Najeriya bisa kama jagororin Ansaru

    Mahmud Muhammad Usman Mahmud al-Nigeri

    Asalin hoton, ONSA

    Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya yaba da kama fitattun shugabannin ƙungiyar Ansaru da jami'an tsaronta suka yi.

    A ranar Asabar ne gwamnatin Najeriya ta ce jami'an tsaronta sun kama ƴan ƙungiyar ta Ansaru, waɗanda take zargi da kitsa fasa gidan yarin kuje a shekarar 2022 har suka tseratar da wasu fursunoni.

    A wani rubutu da ofishin jakadancin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce, "muna yaba wa ƙoƙarin gwamnatin Najeriya da jami'an tsaronta bisa samun nasarar kama shugabannin ƙungiyar Ansaru da ake nema ruwa a jallo, Mahmud Muhammad Usman wanda aka fi sani da Abu Bara'a da Mahmud al-Nigeri da aka fi sani da Mallam Mamuda."

    Ofishin ya ƙara da cewa kama mutanen guda biyu, "babbar nasarar ce ga ƙasar a yunƙurinta na yaƙi da ta'addanci."

  14. Hutu na je a Landan ba asibiti ba - Akpabio

    Godswill Akpabio

    Asalin hoton, Godswill Akpabio

    Shugaban majalisar dattawa ta Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya musanta abin da ya kira raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana fama da rashin lafiya.

    Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da asuban ranar Litinin daga birnin Landan, inda wasu sanatoci da hadimansa da wasu magoya bayansa suka tarbe shi.

    Da yake jawabi ga manema labarai a filin jirgin, Akpabio ya ce batun rashin lafiyarsa ƙanzon kurege ne mara tushe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    "Babu maganar rashin lafiya, lafiyata ƙalau. Na tsaya a Landan ne kawai domin hutu, ba rashin lafiya ba," in ji shi.

    Kafin zuwansa Landan, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisa na ƙasashen duniya da aka yi a Geneva na ƙasar Switzerland daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa 31.

  15. An kama wani mutum da hannu a harbin ƴar shekara 9 a Landan

    ...

    Asalin hoton, MET POLICE

    Bayanan hoto, ...

    An same Javon Riley, ɗan shekara 33, da hannu a harbin da ya bar yarinya ƴar shekara 9 da harsashi a cikin kwakwalwarta.

    An same shi da laifin haddasa mummunan rauni da nufin cutar da yarinyar, wadda aka harbe ta a kai a gaban wani gidan cin abinci na Evin a Kingsland High Street, Hackney da ke gabashin London, a ranar 29 Mayu 2024.

    Haka kuma an same Riley da laifin ƙoƙarin kisan wasu maza uku waɗanda suke zaune a wajen gidan cin abincin a daren.

    Harin kan yarinyar ya faru ne saboda rikici mai tsanani tsakanin kungiyoyin dabar Turkiyya masu adawa da juna.

    Uwar yarinyar ta bayyana cewa: "A cikin ɗan lokaci, makoma da fatar da muke da shi kan yarinyarmu duk sun lalace saboda an harbin da aka yi mata.Yarinya ce me kuzari da son sanin abubuwa."

    "Yanzu, rauni da ta samu a gefen hagu na jikinta yana hana ta motsi, ta gefe take tana kallon abubuwa daga gefe, yanzu taana ɗauke da farantin titanium a cikin kwakwalwarta da harsashi ke ciki."

  16. BBC ta ga yadda Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke kai wa Falasɗinawa hari a gonakinsu

    ..

    Asalin hoton, Fred Scott, BBC

    BBC ta gane wa idanunta yadda Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke ƙaddamar da hare-haren a kan Falasɗinawa a yankin Yamma da Gaɓar Kogin Jordan.

    Gomman Yahudawa ƴan kama wuri zauna ɗauke da sanduna sun ƙaddamar da hare-hare kan wani manomi ba tare da ya yi musu komai ba.

    Wani manomi mai suna Brahimi ya nuna wa ma'aikatan BBC yadda Yahudawan suka kakkarya bishiyoyin da ke yankin kawai saboda su samu sandunan dukan jama'a.

    Ƴan kama wuri zaunar sun yi kan ma'aikatan BBC, inda ma'aikatan suka gudu su kuma suka haɗu da Falasɗinawa masu ɗauke da sanduna da gwafa domin kariyar kai.

  17. Mene ne ƙarin mahaifa, kuma me ya sa ƴanmata ke fama da shi?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Yawanci ana ganin cutar ƙabar mahaifa wato fibroids na damun mata ne daga shekaru 30 zuwa 50 inda ake kallon ta a matsayin wata cuta da ke shafar mata manya ne kawai. Sai dai labarin Aisha Musa, wata yarinya 'yar shekara 26 daga Kaduna, ya nuna cewa wannan cutar na iya shafar mata ƙanana fiye da yadda ake zato.

    Aisha ta fara lura da wasu canje-canje a jikinta shekaru biyu da suka wuce, lokacin da take cikin ƙuruciya. Ta shaida wa BBC Hausa yadda ta fara jin ciwon ciki mai tsanani da kumburin a ƙasan cikinta, da kuma jin zafi sosai lokacin da take fitsari da kuma lokutan al'ada.

    "Na fara jin wani irin ciwo a cikina, kamar yana matsa min gaba da baya. Bayan wani lokaci sai ciki na ya ƙara girma kamar ina da juna biyu. Hakan ya sa na fara jin tsaro da rashin jin daɗi sosai," in ji Aisha.

    Ta kara da cewa ta kuma lura da canji a al'adarta, inda jinin al'adarta ya ƙara yawa sosai fiye da da, kuma kwanakin al'adar ya ƙaru sosai inda yake ɗaukan tsawon lokaci kafin ya tsaya. Wannan ya sa ta damu kuma ta garzaya asibiti.

  18. Labarai da dumi-dumi, Aƙalla mutum 40 sun ɓace sakamakon haɗarin kwale-kwale a Sokoto

    Sokoto

    Asalin hoton, National Emergency Management Agency (NEMA) Nigeria

    Aƙalla mutum 40 ne ake nema bayan haɗarin kwale-kwale a ƙaramar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Lahadi.

    Tuni dai hukumar agajin gaggawa ta ƙasar tare da haɗin gwiwar hukumomin jihar suka bazama domin ceto waɗanda suka ɓacen.

    Waɗanda lamarin ya shafa yawanci ƴan kasuwa ne da suke hanyar tafiya zuwa babbar kasuwar Goronyo da ke ci duk ranar Lahadi a lokacin da kwale-kwalen ya kife ɗauke da matafiya kusan 50, amma hukumomi sun ce an samu nasarar ceto mutum 10.

    A mako uku da suka gabata ne aƙalla mutum 13 suka rasu bayan wani kwale-kwale ɗauke da mutum 100 ya kife a jihar Neja.

    Haka kuma manoma 16 sun rasu wani haɗarin a watan Agustan 2024 a jihar ta Sokoto, sannan a ranar 29 ga watan Yuli, ƴanmata shida sun nutse bayan kwale-kwale ya kife da su a jihar Jigawa.

    Ko a kwana biyun da suka gabata, wasu mutum 13 sun mutu a haɗarin kwale-kwale a jihar Neja.

    Sokoto

    Asalin hoton, National Emergency Management Agency (NEMA) Nigeria

    Sokoto

    Asalin hoton, National Emergency Management Agency (NEMA) Nigeria

  19. Hare-haren Rasha sun kashe mutum biyar a Ukraine

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    Hare-haren Rasha da jirage marasa matuƙa sun faɗa kan wani ginin rukunin gidaje da ke birnin Kharkiv a Ukraine.

    Magajin birnin, Igor Terek-hov, ya ce aƙalla mutane uku sun rasa rayukansu, ciki harda yaro ɗan shekara biyu.

    Da dama kuma sun jikkata. Likitoci na bada kulawa ga wata mata da aka ceto daga ƙarkashin ɓaraguzan gini, da kuma wata yarinya 'yar shekara shida.

    Kharkhiv, da ke yankin arewa maso gabashin Ukraine a kusa da iyakar Rasha, ya sha fuskantar irin waɗannan hare-hare a kai a kai daga Rasha tun ƙaddamar da mamaya shekaru uku da rabi da suka gabata.

  20. Za a kai ƙananan yaran Gaza Birtaniya domin kula da lafiyarsu

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    An fare shirye-shiryen kwasan ƙananan yara tsakanin guda 30 zuwa 50 daga Gaza zuwa Birtaniya domin kula da lafiyarsu.

    Hukumar Lafiya ta Duniya ce za ta tantance yaran da za a kwasa, waɗanda suka fi buƙatar kula tare da iyalansu kafin a tafi da su.

    Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan wasu ƴanmajalisar Birtaniya sun rubutu wasiƙa zuwa ga gwamnatin ƙasar, inda suka buƙaci a kwashe ƙananan yara da suke fama da rashin lafiya a Gaza zuwa Birtaniya ba tare da ɓata lokaci ba.

    A wasiƙar, ƴanmajalisa 96 sun yi gargaɗin cewa ƙananan yaran na fuskantar barazanar mutuwa saboda halin da suke ciki, sannan kuma ga rashin asibitoci masu kyau a Gaza da za a kula da su.

    Dama dai gidauniyar lafiya ta Project Pure Hope (PPH) ta kwasa wasu yaran zuwa Birtaniya a baya, amma yanzu gwamnati ce ta za ta ɗauki ragamar a hukumance.