An fara fitar da sakamakon zaɓen Kamaru

Asalin hoton, CRTV
Majalisar tsarin mulkin Kamaru ta fara bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru da aka gudanar ranar 12 ga watan Oktoban 2025.
Kawo yanzu majalisar ta bayayna sakamakon yankuna biyar daga cikin yankunan ƙasar 10 kamar haka:
- Adamawa - Issa Chiroma Bakary ya samu kashi 56 na ƙuri'un.
- Lardin Tsakiya - Paul Biya ya samu kashi 70.14 na ƙuri'un
- Lardin Gabas - Paul Biya ya samu kashi 73.88 na ƙuri'un
- Lardin Arewa Mai Nisa - Paul Biya ya samu kashi 45.93 na ƙuri'u
- Lardin Littoral - Tchiroma Bakary ya samu kashi 64.5
Za mu ci gaba da kawo sakamakon yayin da yake ci gaba da shigowa
Wanda ya fi samu ƙuri'u a duka lardunan ƙasar ne zai yi nasara a zaɓen.






