Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 27/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 27/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Fararen hula sun maƙale a birnin El-Fasher da RSF ta mamaye

    Fargaba na ci gaba da karuwa a kasar Sudan, sakamakon daruruwan fararen hula ne suka kasa ficewa daga birnin El-Fasher bayan da dakarun RSF suka bayyana iko da birnin.

    Kungiyar bayar da agajin ta ce dubban mutane ne suka isa Tawilla a cikin dare, inda galibinsu suka makale a El Fasher, birnin da ya kwashe lokaci yana fuskantar hare-haren dakarun sojin Sudan da na RSF.

    Kungiyar bayar da agaji ta Medicine San Frontiers, ta yi gargadin cewa za a iya samun kisan iyashi idan har ba a ba jama'a damar fita daga birnin ba.

    Ta ce gwamman mutanen da suka samu rauni sun samu isa garin Tawilla mai nisan kilomita shida yamma da birnin.

  2. Hamas ta sake gano gawar wani ɗan Isra'ila ɗaya

    Kungiyar Hamas ta ce nan gaba kadan za ta mika wata gawar wani dan Isra'ila da ta gano yau Litinin a Gaza.

    Har yanzu dai kungiyar ta Hamas na ci gaba da rike sauran mutum sha uku da ke hannunta ba, inda ta bayyana dalilai da dama da suka haifar da wannan jan kafar.

    Shugaban Hamas Kalil al-Hayya ya ce yanzu haka ba su san inda wasu daga cikin gawarwakin suke ba amma suna ci gaba da nema.

    A hirarsa da wata kafar watsa labaran Saudiyya shugaban na Hamas ya ce, wadanda suka binne gawarwakin su ma an kashe su a lokacin yakin, baya ga sauyawar wurare da dama a yankin na Gaza sakamkon luguden wutar da jiragen yakin Isra'ila suka yi.

  3. Luthiana ta ce za ta rufe kan iyakar ƙasarta saboda masu fasaƙaurin taba sigari

    Firaministar Lithuania ta ce ƙasarta za ta soma ɗaukar matakan harbo wasu ƙananan balanbalan da masu fasa ƙwauri ke amfani da su wajen ratsa sararin samaniyar ƙasar daga Belarus, bayan da a 'yan makonninan nan suka haifar da cikas ga zirga-zairgar jiragen sama.

    Da take jawabi a bayan wani taron gaggawa na Hukumar Tsaron Kasar, Inga Ruginiene, ta ce za a rufe kan iyakar ƙasar har sai yadda hali ya yi, inda jami'an doflomasiyya da sauran 'yan ƙasashen Turai ne kawai da za a bai wa damar ficewa daga Belarus.

    Lithuania ta ce ana amfani da balanbalan din ne wajen safarar taba sigari zuwa Turai, ta kuma bayyana matakin a matsayin wata farfagandar saka fargaba a zukatan al'ummarta.

    Sai dai Belarus wadda ke dasawa da Rasha ba ta ce kome ba akan matakin.

  4. An rufe makarantu a Mali saboda ayyukan masu iƙirarin jihadi

    Rundunar tsaron Mali ta bayar da umarnin rufe makarantu ciki har da jami'o'i saboda tsananin ƙarancin man fetur da ƙasar ke fuskanta saboda ayyukan ƴanbindiga masu iƙirarin jihadi.

    Tun a watan Satumba ne wasu mayaƙa da ake kira da JNIM da suka yi mubaya'a da ƙungiyar al-Qaeda suka hana shigar da men fetur ƙasar Mali.

    Mayaƙan suna kai farmaki kan tankokin sufurin man fetur da ke shigowa ƙasar daga ƙasashen Senegal da Côte d’Ivoire da ke maƙwabtaka da ita, lamarin da ya ƙara jefa ƙasar cikin wani mawuyacin halin taɓarɓarewar tattalin arziki.

    Rahotanni na cewa akwai ɗaruruwan tankokin man fetur da suka maƙale a bakin iyakokin ƙasar. Sojojin ƙasar sun yi rakiya ga wasu tankokin zuwa babban birnin ƙasar Bamako, inda wasu suka samu nasara, amma mayaƙan suka yi kwanton ɓauna kan wasu jerin gwanon motocin.

    A wata sanarwa da ministan ilimin ƙasar Amadou Sy Savane ya fitar, ya ce za a rufe dukkan makarantun ƙasar ne na mako biyu, "saboda ƙarancin man fetur da ya yi ƙamari, lamarin da yake haifar da tsaikon isar da kayayyakin karatu zuwa makarantu."

  5. Muna kiran a kawo ƙarshen rikicin Myanmar - Antonio Guterres

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta kawo karshen tashin hankali a kasar Myanmar. Ya kuma nemi shugabannin sojin kasar da su dauki matakan da suka dace domin maido da kasar bisa tafarkin dimkuradiyya.

    Da ya ke jawabi a kasar Malaysiya a yayin taron koli na Kasashen Asiya, Antonio Guterres ya ce bayan da sojojin kasar Burma suka yi juyin mulki a shekarar 2021, al'ummar kasar suka kara tsunduma cikin halin matsin rayuwa.

    Shugabannin sojin kasar dai na shirin gudanar da babban zabe ne a karshen wannan shekara, sai dai masu sharhi sun kira lamarin da kokarin ci gaba da tabbatar da karfin ikon da suke da shi.

  6. An ɗage fara tantance ƴantakarar shugabancin PDP

    Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya ta sanar da ɗage tantance ƴantakarar neman shugabancin jam'iyyar zuwa wani lokacin nan gaba.

    Tun da farko an tsara tantance ƴantakarar ne a gobe Talata, inda a ƙa'ida dukkan masu neman muƙami a jam'iyyar za su bayyana a gaban kwamiti domin a tantance su.

    Sai dai a wata sanarwa da jam'iyyar ta fitar, ta ce wasu abubuwa ne suka taso mata masu muhimmanci da suka sa dole a ɗage aikin.

    "Kwamitin tsare-tsaren babban taron jam'iyyar PDP na sanar da ɗage tantance ƴantakarar shugabancin jam'iyyar da aka tsara yi a ranar Talata 28 ga watan Oktoba saboda wasu dalilai.

    "Za mu sanar da wata ranar da za a yi tantancewar nan gaba kaɗan. Muna bayar da haƙuri kan rashin jin daɗin da wannan matakin zai haifar."

    Kwamitin ya ce a shirye yake ya tabbatar da shirya babban taro mai inganci a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba a Ibadan na jihar Oyo.

  7. Guguwar Melissa na ci gaba da nausawa ƙasar Jamaica

    Wata gugguwa mai tsananin karfi da aka yi wa lakabi da Melissa na ci gaba da nausawa zuwa kasar Jamaika, kuma a lokaci daya tana kara karfi da barna.

    Gwamnatin Jamaika ta bayar da umurnin gaggauta kwashe jama'a daga wasu sassan babban birnin kasar, Kingston. An dai bayyana gaba dayan tsibirin a matsayin mai matukar fuskantar barazana.

    Wakiliyar BBC ta ce; koda yake ana yawan samun guguwar Haurricane a kasar Jamaika, to sai dai wannan ne karo na farko da guguwar ta fi yin ta'adi a kasar, tun bayan Haurricane Gilbert da ta yi gagarumar barna a kasar a shekarar 1984.

    An dai yi hasashen zata dauki sa'a 24 tana tafiya tare da iska mai tsananin karfi kafin ta dira a kasar, abin da zai iya haifar da gagarumar ambaliya.

  8. Donald Trump ya fara rangadi a ƙasar Japan

    Shugaba Donald Trump na Amurka ya sauka a birnin Tokyo na kasar Japan, a daya daga cikin rangadin baya-bayan nan da yake yi a ƙasashen nahiyar Asiya.

    Zai gana da Basaraken ƙasar Naruhito, kafin daga bisani ya tattauna da sabuwar Firaministar Japan Sanae Takaichi a gobe Talata.

    Firaministar ta shaida wa Mista Trump cewa babban abin da ta fi mayar da hankali shi ne ƙara inganta alaƙar tsaro tsakanin ƙasarta da Amurka.

    Ana dai sa ran shugaba Trump zai kara matsa wa Japan lamba domin ta ƙara kashe kuɗi bangaren tsaro.

    Wakiliyar BBC ta ce gano ta ce wannan muhimmiyar ziyara ce ga kasar Japan, wadda ke muradin ganin alakatara da Amurka da ta shafi tsaro ta ci gaba da ingantuwa, musamman ganin yadda yankin ke fuskantar barazana.

  9. Ban yi laifin komai ba, ku sake ni kawai - Nnamdi Kanu

    Jagoran Ƴan'awaren IPOB, Nnamdi Kanu, ya sake nanata cewa shari'ar zargin ta'addanci da ake yi masa abin kunya ne, saboda babu takamammiyar tuhumar da ake yi masa.

    Kanu ya bayyana hakan ne a kotu ranar Litinin yayin da yake kare kansa da kansa a gaban Mai shari'a James Omotosho, wanda ke jagorantar shari'ar.

    A lokacin da aka fara zaman shari'ar, lauyan gwamnatin tarayya, Adegboyega Awomolo ya tuna wa kotun cewa an shiga kwana na uku cikin kwana shidan da kotun ta bai wa Kanu domin kare kansa.

    Nnamdi Kanu Ya ce ya samu lokacin nazarin takardun tuhumar, inda ya gano cewa babu wata tuhuma guda ɗaya da ake yi masa.

    "Idan akwai wata tuhuma, ina son mai shari'a ya karanto min ita, don haka bai kamata in shiga batun kare kaina ba, tun da babu wata tuhuma da ake yi mini ƙarƙashin dokokin Najeriya.'' in ji shi.

    Sai dai yayin da yake tsaka da jawabi, Alƙalin kotun, Mai shari'a Omotosho ya dakatar da shi, yana mai cewa ya kamata ya fahimci yadda tsarin kotu yake.

    To amma bayan jawabin da alƙalin kotun ya yi masa kan yadda al'amuran kotu ke gudana, Nnamdi Kanu ya dage cewa babu wata tuhuma a kansa, don haka kawai a sake shi ya yi tafiyarsa.

  10. Ba a sayar wa Sule Lamido takardar tsayawa takarar shugabancin PDP ba

    Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a kan hana shi samun takardar tsayawa takarar shugabancin babbar jam'iyyar adawar ƙasar, PDP.

    Lamido, wanda bai samu damar sayen form ɗin ba daga shalkwatar sakatariyar jam'iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja.

    Yayain da yake zantawa da manema labarai a gaban ɗimbin magioya bayansa, tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya nuna rashin gamsuwarsa kan matakin.

    Sule Lamido ya ce a shirye yake ya tsaya takarar shugabancin jam'iyyar a zaɓen da za a yi lokacin babban taron jam'iyyar na cikin watan Nuwamban a birnin Ibadan na jihar Oyo.

    Tsohon ministan harkokin wajen Najeriyar, ya sha alwashin tafiya kotu idan har aka ƙi sayar masa da Takardar tsayawa takarar.

    Tuni dai gwamnonin PDP suka nuna goyon bayansu da tsohon ministan ayyuka na musamman, Kabiru Turaki a matsayin shugaban jam'iyyar.

  11. 'Zanga-zanga ta ɓarke a birnin Douala'

    Rahotonni daga birnin Douala, cibiyar kasuwancin Kamaru na cewa an samu ɓarkewar zanga-zanga a birnin jim kadan bayan sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

    Wasu bidiyoyi da aka yaɗa a sada zumunta sun nuna gomman mutane sun fantsama kan titunan birnin, tare da rera waƙoƙin Issa Tchiroma Bakary, jagoran adawar ƙasar.

    Kamfanin dillancin labaran Kamaru, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda aka lalata wani ginin majalisar birnin, bayan da masu zanga-zangar suka far masa.

  12. An rufe makarantu da shaguna a birnin Yaoundé

    Yayin da ake ci gaba da zaman zullumi kan abin da ka iya faruwa bayan sanar da sakamakon zaɓen Kamaru, makarantu da shaguna sun kasance a rufe a Yaoundé, babban birnin Kamaru.

    Hatta ma'aikatan gwamnati sun ƙi fita wuraren ayyukansu, sakamakon fargabar.

    Girke jami'an tsaro da dama da aka yi a birnin ya taƙaita zanga-zangar da aka fara yi a birnin da na Douala cibiyar tattalin arzikin ƙasar da kuma birnin Garoua, mahaifar jagoran adawar ƙasar Tchiroma Bakary.

    Kawo yanzu dai, yan ƙasar da dama sun ci gaba da kasancewa a cikin gidajensu bayan da aka sanar da Shugaba Biya a matsayin wanda ya lashe zaɓen a wa'adin mulki na takwas.

  13. Labarai da dumi-dumi, 'An harbe wasu mutane a kusa da ƙofar gidan Tchiroma Bakary'

    An harbe tare da kashe wasu mutane a kusa da ƙofar gidan jagoran adawar Kamaru, Tchiroma Bakary da ke birnin Garoua, kamar yadda wani ɗan jarida da ke wurin ya shaida wa BBC.

    Ana iya jin ƙarar harbin ta cikin waya, yayin da ake magana da ɗan jaridar.

    Jagoran adawar ya wallafa a shafinsa ta Facebook cewa ''an bayar da umarnin harbi kan fararen hula a wajen ƙofar gidansa''.

    Kawo yanzu hukumomi ba su ce komai ba game da lamarin.

  14. Isra'ila ta zargi dakarun MDD ta kakkaɓo jirginta a Lebanon

    Isra'ila ta zargi masu wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da harbo ɗaya daga cikin jiragenta marasa matuƙa da gangan a Lebanon

    Dakarun na Majalisar Dinkin Duniya sun ce sun kai wa jirgin hari ne saboda yadda ya riƙa bibiyar dakarunta masu sintiri a wani yanayi na yaƙi.

    Sai dai Isra'ila ta ce jirgin nata maras matuƙi na kan aikinsa na tattara bayanan sirri da ya saba yi, kuma babu wata barazana da ya yi wa masu wanzar da zaman lafiyar.

    Bayan kakkaɓo jirgin, dakarun Isra'ila sun kai harin gurneti a yankin, kodayake ba a samu rahoton jikkata ba.

    Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare kan yankunan da ta ce na ƙungiyar Hezbollah ne a Lebanon, duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Nuwamban bara.

    Tana mai cewa tana kai hare-haren ne da nufin hana ƙungiyar sake mallakar makamai.

  15. Ana zaman ɗar-ɗar bayan sanar da sakamakon zaɓen Kamaru

    Ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar Kamaru, bayan da hukumar zaben ƙasar ta ayyana Shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

    Hukumar zaɓen ta ce Paul Biya ya lashe zaɓen da kashi 53.66 cikin 100, yayin da jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary ya samu kashi 35.19 cikin 100.

    A wata hira da BBC a ƴan kwanakin nan, Bakary ya yi iƙirarin lashe zaɓen.

    A ƴan kwanakin nan an yi samun zanga-zanga a wasu biranen ƙasar, inda har aka samu rahoton mutuwar mutum huɗu sakamakon arangama da jami'an tsaro.

  16. Paul Biya ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya

    Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya ya kasance shugaban ƙasa mafi tsufa da aka taɓa yi a duniya.

    Biya, mai shekara 92 ya fuskanci kiraye-kirayen haƙura da takara.

    An riƙa sukar shugaban da rashin halartar gangamin yaƙin neman zaɓe, inda ya halarci gangami ɗaya kawai tun da ka fara yaƙin neman zaɓen a wannan karon.

    Kasancewarsa a kan muƙamin shugaban ƙasar, tun shekarar 1982 - ƙarin shekara bakwai na sabon wa'adinsa zai sa ya shafe shekara 50 a kan karagar m ulki.

    A shekarar 2032 ne zai cika shekara 100 a duniya.

    Nasarorinsa a zaɓukan baya na cike da zarge-zargen maguɗin zaɓe, zargin da jam'iyyarsa da gwamnatinsa suka sha musantawa.

  17. Labarai da dumi-dumi, Paul Biya ya lashe zaɓen shugaban Kamaru

    Shugaban ƙasar Kamaru mai ci Paul Biya ya lashe zaɓen shugaban ƙasa karo na takwas.

    Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ce ta bayyana Paul Biya, mai shekara 92 a duniya a matsayin wanda ya lashe zaɓen.

    Wannan na nufin Biya zai ci gaba da jan ragamar ƙasar har zuwa shekara ta 2032.

    Biya ya lashe zaɓen da kashi 53.66% na ƙuri'in da aka kaɗa, inda ya samu ƙuri'a sama da miliyan biyu, sai kuma jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary ke biye da shi, inda ya samu kashi 35.19%, sama da ƙuri'u miliyan ɗaya.

  18. Ƴan Kamaru mazauna ƙetare sun zaɓi Tchiroma Bakary

    Ƴan Kamaru mazauna Turai sun zaɓi jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary.

    Bakary ya samu kashi 62.79 cikin 100 na ƙuri'un ƴan ƙasar mazauna ƙetare, yayin da Biya ya samu kashi 22.63.

  19. Zaɓen Kamaru: Sakamakon ragowar larduna biyu

    • Lardin Kudanci - Nan ne maihaifar Paul Biyas, kuma ya lashe lardin da kashi 90.86 na ƙuri'un lardin.
    • Kudu Maso Yamma - Kudan kashi 53 cikin 100 na al'ummar lardin ba su yi zaɓe ba, amma kashi 68.7 na waɗanda suka yi zaɓen sun zaɓi Paul Biya.
  20. Ƙarin sakamako daga larduna uku

    An ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru, inda aka ayyana sakamakon daga ƙarin larduna uku da suka haɗa da:

    • Lardin Arewa - Issa Tchiroma Bakary ya lashe da kashi 43.51
    • Lardin Arewa Maso Yamma - kashi 52.5 cikin 100 na al'ummar lardin sun ƙaurace wa zaɓen, amma kashi 86.31 na waɗanda suka yi zaɓe sun zaɓi Pual Biya.
    • Lardin Yamma - Paul Biya ya lashe da kashi 46.21, inda Tchiroma ya samu kashi 38.6

    Za mu ci gaba da kawo muku ragowar sakamakon yankuna biyu da suka rage.