Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 27/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Litinin 27/10/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. An fara fitar da sakamakon zaɓen Kamaru

    Majalisar tsarin mulkin Kamaru ta fara bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru da aka gudanar ranar 12 ga watan Oktoban 2025.

    Kawo yanzu majalisar ta bayayna sakamakon yankuna biyar daga cikin yankunan ƙasar 10 kamar haka:

    • Adamawa - Issa Chiroma Bakary ya samu kashi 56 na ƙuri'un.
    • Lardin Tsakiya - Paul Biya ya samu kashi 70.14 na ƙuri'un
    • Lardin Gabas - Paul Biya ya samu kashi 73.88 na ƙuri'un
    • Lardin Arewa Mai Nisa - Paul Biya ya samu kashi 45.93 na ƙuri'u
    • Lardin Littoral - Tchiroma Bakary ya samu kashi 64.5

    Za mu ci gaba da kawo sakamakon yayin da yake ci gaba da shigowa

    Wanda ya fi samu ƙuri'u a duka lardunan ƙasar ne zai yi nasara a zaɓen.

  2. Majalisar Kundin Tsarin mulkin Kamaru za ta fara sanar da sakamakon zaɓe

    Shugaban Majalisar Kundin tsarin mulkin Kamaru Clement Atangana na shirin bayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar a birnin Yaounde.

    Ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana.

    A wani bayani da ya yi, wanda kamar shaguɓe ne ga ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary, Atangana ya soki waɗanda suka yi hasashen sakamakon, yana mai cewa hanya ɗaya tal da doka ta amince, ita ce bin tanade-tanaden doka wajen yin ƙorafi.

    Aƙalla ƙorafe-ƙorafe 10 na zargin yin maguɗin a zaɓen na 12 ga watan Oktoba ne Majalisar Kundin tsarin mulkin ta yi watsi da su.

  3. Ana cikin zaman ɗar-ɗar a Kamaru gabanin ayyana sakamakon zaɓe

    Al'ummar Kamaru na cikin halin zaman dar-ɗar gabanin ayyana sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar 12 ga watan Oktoban da muke ciki.

    An samu rahotonnin gudanar da zanag-zanga a wasu biranen ƙasar, domin nuna damuwa kan halin da ake ciki game da zaɓen.

    Hukumomin ƙasar sun tabbatar da mutuwar mutum huɗu cikin masu zanga-zangar sakamakon arangama da jami'an tsaro.

    Tun da farko an tsara ayyana sakamakon zaɓen ranar Alhamis da ta gabata, sai dai hakan bai samu ba sakamakon wasu tsaiko da aka samu.

    Tuni dai jagoran adawar ƙasar, Issa Tchirmo Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya ya lashe zaɓen.

    Sai dai hukumomin ƙasar sun ce matakin nasa ya saɓa wa doka, kasancewar majalisar tsarin mulkin ƙasar ce kawai ke da alhakin bayyana sakamakon zaɓen a hukumance.

  4. Ya kamata ƙasashen waje su yi taka-tsantsan kan aiwatar da zaman lafiyar Gaza

    Sarki Abdullah na Jordan ya ce ƙasashen waje za su yi taka tsantsan game da roƙon da aka yi musu na su aiwatar da zaman lafiya a Gaza a ƙarƙashin shirin zaman lafiya na Shugaba Trump.

    Wannan yana kira ga ƙasashen Larabawa da sauran abokan hulɗa na ƙasashen duniya su samar da rundunar zaman lafiya, yayin da ake sa ran mayaƙan Hamas za su kwance damarar yaƙi su kuma haƙura da ikon siyasar Gaza.

    Amma da yake magana da BBC, Sarki Abdullah ya ba da shawarar cewa membobin ƙasashen duniya ba za su so a jawo su cikin rikici tsakanin Hamas da Isra'ila ba, ko kuma tsakanin Hamas da sauran ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi na Falasɗinu.

    Sarki Abdullah ya ce Jordan da Masar na burin horas da jami'an tsaron Falasɗinawa, amma hakan zai ɗauki lokaci.

  5. Sojojin Najeriya sun kashe ƴanbinga 80 da suka yi yunƙurin shiga Kebbi

    Dakarun sojin Najeriya sun kashe ƴanbindiga kusan 80 da suka yi yunƙurin shiga jihar Kebbi daga kan iyakar jihar da Zamfara.

    Cikin wata sanarwa da babban mai bai wa gwamnan jihar Kebbi shawara kan sadarwa da tsare-tsare, Abdullahi Zuru ya fitar ranar Lahadi ya bayyana matakin da babbar nasara da aka samu a yaƙi da ƴanbindiga a watannin baya-bayan nan.

    Ya ce lamarin ya faru ne a yankin ƙaramar hukumar Ngaski, bayan da gwamnan jihar ya buƙaci a girke jami'an tsaro da kayan aiki a kan iyakokin jihohin Kebbi da Sokoto da Zamfara da kuma jihar Neja.

    ''Kusan ƴanbindiga 80 aka kashe, tare da raunata wasu da dama sannan aka lalata gomman babura sakamakon arangama da jami'an tsaro'', in ji sanarwar.

    Tun da farko gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya buƙaci samar da ƙarin sansanin soji a jihar domin ƙarfafa tsaron jihar mai fama da barazanar Lakurawa, wadda kuma ta yi iyaka da jihohin da ke fama da matsalar ƴanfashin daji.

  6. Trump ya isa Japan a ziyarar da yake yi a Asiya

    Shugaba Trump na Amurka ya isa birnin Tokyo na ƙasar Japan a wata ziyara da yake yi a yankin Asiya.

    Mista Trump zai gana da Sarki Naruhito kafin ganawarsa da sabuwar firaiministar ƙasar, Sanae Takaichi.

    Ms Takaichi ta ce ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Amurka ta Japan ne babban abin da ganawar za ta mayar da hankali.

    Japan ta zuba maƙudan biliyoyin daloli cikin tattalin arzikin Amurka, lamarin da ya sa wasu ke ganin dalilin da ya sa ta tsallake harajin da Trump ya ƙaƙaba wa wasu ƙasashe.

  7. NiMet ta yi hasashen samun hazo na kwana uku a wasu jihohin Najeriya

    Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya, NiMet ta yi hasashen samun mabambantan yanayi a wasu sassan ƙasar, da suka haɗa da hazo da ruwan sama daga Litinin zuwa Laraba.

    Cikin wani rahoto da hukumar ta fitar ranar Lahadi ta buƙaci ƴanƙasar su zama cikin shiri domin tunkarar waɗannan yanayi.

    NiMet ta yi hasashen samun hazo har na tsawon kwana uku a jihohin Borno da Zamfara da Yobe da Jigawa da Kano da Katsina da kuma wasu yankunan arewacin Kaduna.

    Haka ma hukumar ta ce akwai hasashen samun ruwan sama haɗe da tsawa a wasu yankunan jihohin Taraba da Adamawa.

    Hukumar ta kuma yi hasashen samun rana a wasu jihohin arewa ta tsakiyar ƙasar, da kuma yiwuwar samun ruwan sama a jihohin Nasarawa da Kogi da Birnin Tarayya Abuja.

  8. Mutum huɗu sun mutu a zanga-zangar Kamaru

    Gwamnatin Kamaru ta tabbatar da cewa mutum hudu suka mutu a zanga-zangar da ƴanƙasar suka gudanar a ranar Lahadi a birnin Doula gabanin sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a yau Litinin.

    Ɗaruruwan magoya bayan ɗantakarar adawa, Issa Tchiroma Bakari ne suka fito zanga-zangar.

    Hukumomi sun ce an kai wa ƴansanda da jami'an tsaro hari ne, dalilin da ya sa suka kare kansu.

    Tchiroma Bakary ya ƙalubalanci shugaba Paul Biya - wanda ya shafe shekara 43 yana shugabanci a ƙasar.

    Tuni jagoran adawar ya ayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen, duk da cewa a yau Litinin ne ake sa ran sanar da sakamakon a hukumance.

  9. Ana shirye-shiryen sanar da sakamakon zaɓen Kamaru

    Nan gaba a yau ne ake sa ran fara sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar Kamaru mai cike da ƙalubale, yayin da al’ummar ƙasar ke cikin zullumi tare da fatan ganin an sanar da wanda suka zaɓa a matsayin wanda ya yi nasara lashe zaɓen shugaban ƙasar.

    An dai tsaurara tsaro a ƙasar a wani shirin ko ta kwana, yayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cak , gabanin fara sanar da sakamakon zaɓen.

    Tun da farko an tsara sanar da sakamakon zaɓen a ranar Alhamis da ta gabata, sai dai majalisar tsarin mulkin ƙasar mai alhakin sanar da sakamakon zaɓen ta ɗage zuwa yau Litinin.

    Manyan ƴantakara biyu ne dai a kan gaba a zaɓen wato, Shugaba Paul Biya da ya shafe shekara 43 yana jagorancin ƙasar,da kuma jagoran adawa Issa Tchiroma Bakary

  10. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki ko da nasara na tsoronki, kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a fain duniya.

    Kada manta da shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.