Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/06/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Haruna Kakangi, Aisha Babangida

  1. Ban tuntuɓi Iran don tattaunawar zaman lafiya ba - Trump

    ....

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya wallafa a dandalin sa na Truth Social cewa bai tuntubar Iran don tattaunawar zaman lafiya "ta kowace hanya ko tsari ko salo" ba.

    Trump ya ƙara da cewa Iran ya kamata a ce ta sa hannu a yarjejeniyar da ya gabatar a lokacin da aka yi taron karshe kan shirin nukiliyar ƙasar.

    Trump ya ce, “Wannan wani labari ne na ƙarya da aka ƙirƙira, Idan suna son tattaunawa, sun san yadda za su same ni. Ya kamata a ce sun amince da yarjejeniyar da aka gabatar musu — hakan da ya ceci rayuka da dama”.

  2. Najeriya ce kan gaba a yawan fitar da man fetur a Afirka cikin watan Mayu - OPEC

    Gangar mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC ta ce duk da raguwar fitar da mai da aka samu a Najeriya, har yanzu ƙasar ce ta fi kowace ƙasa yawa fitar da mai a Afirka.

    A cikin rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin, ƙungiyar ta OPEC ta ce fitar da ɗanyen mai daga Najeriya ya ragu zuwa ganga miliyan 1.45 a kullum a watan Mayu — daga ganga miliyan 1.48 da aka samu a watan da ya gabata.

    Rahoton ya bayyana cewa duk da wannan raguwar, Najeriya ta ci gaba da zama ƙasa kan gaba a yawan fitar da danyen mai a nahiyar Afirka, inda ta zarce ƙasashen Libya da Aljeriya da Kongo.

    OPEC ta ce ta samo waɗannan alƙaluma ne daga bayanan da ƙasashe suka bayar kai tsaye.

    OPEC ta ƙara da cewa alƙaluman da aka samu ya nuna cewa Najeriya ta fitar da ganga miliyan 1.54 a kullum a watan Mayu, wanda ya ƙaru daga ganga miliyan 1.52 da aka samu a watan Afrilu.

  3. Iran ta kafa cibiyar kula da rarraba kayayyaki masu muhimmanci

    Kafafen yaɗa labarai ta gwamnati Iran sun ce an kafa hedkwata ta musamman domin rarraba kayayyakin amfani masu muhimmanci.

    Kafar yaɗa labarai ta Tasnim ta bayyana cewa an kafa hedkwatar Shahid Salami wacce ke haɗa kai da ma’aikatar noma ta Iran da kuma ƙungiyar 'yan kasuwa don tabbatar da cewa ba a samu matsala wajen rarraba man fetur da shinkafa ba.

    Tasnim ta ruwaito cewa babu wata matsala wajen rarraba kayayyakin amfani masu muhimmanci kamar burodi da fulawa.

  4. 'Ministan harkokin wajen Iran ya yi magana da takwarorinsa na Turai'

    Ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Abbas Araghchi ya yi magana ta wayar tarho da ministocin harkokin wajen wasu ƙasashe uku na Turai, kamar yadda kafafen yaɗa labarai na Iran suka ruwaito.

    Ministan ya buƙaci Turai ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa ƙasar kamar yadda rahoton ya bayyana.

    Araghchi ya ce harin da aka kai wa ƙasarsa na nuni da koma bayan mafi muni ga tsarin diflomasiyya kuma ya ci karo da goyon bayan da ƙasashen yamma ke nuna wa Isra'ila.

  5. Hotunan dake nuna ɓarnar da harin Iran ya haddasa a Isra’ila

    Ga wasu sabbin hotunan da ke nuna barnar da harin sojojin Iran ya haddasa a Israila kamar yadda rundunar tsaron Isra’ila ta bayyana safiyar yau.

    Rundunar ta ce Iran ta harba makamai guda 30 zuwa kasar, inda mafi yawan makaman aka kame su.

    A cikin hotnan, za ku ga masu kashe gobara suna kashe wuta a kan motocin bas da suka ƙone kusa da kuma rami a Herzliya da ke arewacin Tel Aviv.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    ...

    Asalin hoton, Reuters

  6. Babban kwamandan sojin Iran ya mutu a harin Isra’ila – IDF

    Dakarun sojin Isra’ila (IDF) sun ce sun kashe babban kwamandan sojin Iran, Ali Shadmani, a wani hari da suka kai a Tehran da dare.

    Shadmani ne ke jagorantar hedikwatar da ke tsara ayyukan soja na haɗin gwiwa tsakanin dakarun juyin juya hali na IRGC da kuma rundunar sojin Iran ta gargajiya.

    Ya karɓi wannan matsayi ne bayan mutuwar wanda ya gabace shi, Gholamali Rashid, wanda ma harin Isra’ila ya kashe makon da ya gabata.

    Babu wani rahoto kai tsaye daga kafafen yada labarai na Iran da ya tabbatar da mutuwar Shadmani a yanzu.

  7. Iran ta sake ƙaddamar da hare-hare kan Isra'ila - IDF

    .

    Asalin hoton, EPA

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra'ila.

    An riƙa jin ƙarar na'urorin ankararwa a biranen tel Aviv da Jerussalam da asubahin yau.

    Tuni dai rundnar sojin Isra'ila ta umarci mazauna ƙasar su riƙa bin umarnin da ake ba su na inda ya kamata su zauna.

  8. Ba rikicin Gabas ta Tsakiya ne ya sa na bar taron G7 ba - Trump

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba don ƙoƙarin sulhunta rikicin Gabas ta Tsakiya ne ya sa ya bar taron G7 ba.

    Tun da farko Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Trump ya bar taron da wuri ne domin ƙoƙarin sulhunta rikicin Gabas ta Tsakiya.

    To sai dai cikin wwani saƙo da shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Amurka ya ce ba don sulhunta Isra'ila da Iran ya bar taron ba.

    "Bai san abin da ya sa na baro wurn taron ba, tahowata ba ta da alaƙa a da shirin tsagaita wuta, abin da ya taho da ni ya zarta haka'', in ji Trump.

    Kafin tafiyarsa Mista Trump da sauran shugabannin ƙasashen ƙungiyar sun fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da hakkin Isra'ila na kare kanta, tare da bayyana Iran a matsayin babbar mai haifar da rashin zaman lafiya da ta'addanci a yankin.

    A wani ɓangare kuma an bayyana cewa Amurka na tura karin kayayakin aikin soji zuwa yankin, duk cewa da an ambato jam'ian gwamnatin kasar suna cewa Amurka ba za ta hada hannu da Isra'ila wurin kai wa Iran hari ba.

  9. An samu sabbin fashewar abubuwa a birnin Tehran na Iran

    ...

    Asalin hoton, EPA

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar Iran sun ba da rahoton wasu sabbin fashewar abubuwa a birnin Teheran da sanyin safiyar yau Talata.

    Hakan ya biyo bayan gargaɗin da Isra'ila ta yi ne ga mazauna yankunan arewa maso gabashin birnin da su bar gidajensu.

    Tun da farko Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce hare haren da ake kai wa Iran sun sauya yadda lamura suke a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Ya ce sun wargaza shugabancin ɓangaren tsaro na Iran da suka haɗa da manyan hafsoshin soja guda uku da shugaban rundunar sojin sama da kuma shugabannin sashen leƙen asiri guda biyu.

    Sojojin Isra'ilar dai sun yi gargadin fuskantar hare-hare daga Iran har sau biyu amma daga baya sun janye.

  10. Assalamu alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin yau Talata.

    Sannunmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntarmu na intanet da facebook da X da kuma whatsapp.

    Ku kasance da mu