Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na musamman kuma kai tsaye daga Najeriya da sauran sassan duniya na 09/06/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ahmad Bawage

  1. Ana ci gaba da tarzoma a Los Angeles kan kamun baƙin haure

    LA

    Asalin hoton, Getty Images

    An shiga rana ta uku a tarzomar da ake yi a birnin Los Angeles na jihar California ta Amurka inda masu zanga-zanga ke Ɗauki-ba-daƊi da dakarun tsaron Ƙasa da Shugaba Trump ya tura domin kwantar da zanga-zangar da ta Ɓarke sakamakon kamen baƙin haure.

    Dakarun tsaron da Shugaban ya tura saɓanin ra'ayin gwamnan jihar da kuma shugabar birnin suna amfani da hayaƙi mai sa hawaye da harsashin roba wajen tarwatsa masu tarzomar.

    Yayin da zanga-zangar da ta rikiɗe ta zama tarzoma ta shiga kwana na uku, lamarin na ci gaba da ƙazanta inda masu tarzomar suke ƙona motoci da tayoyi kuma dakarun tsaron da 'yansanda da ke artabu da su, sun kama gommansu.

    Shugaba Trump ya bayyana masu tarzomar da gungun masu tayar da hankali da tawaye, yana mai cewa dole ne a tabbatar da doka da oda.

    LA

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkanku da Sallah. Da fatan an yi sallah lafiya . Da fatan an ci nama daidai buƙata. Allah ya maimaimata mana. Allah ya sa mu ga ta baɗin baɗaɗa. Kamar kullum yau ma mun dawo da shafin namu na kai tsaye da ke kawo irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku ci gaba da kasancewa da mu. Mun gode. Muna alfahari da ku.