Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni na musamman kuma kai tsaye daga Najeriya da sauran sassan duniya na 09/06/25

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Gwamnatin Sokoto ta ce ta bai wa kowane alhajin jihar riyal 1,000

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto State Govt

    Bayanan hoto, Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya sanar da bai wa alhazan jihar da ke Saudiyya gudumawar kuɗi Riyal 1,000, kimanin naira 415,000 ga kowanensu.

    Gwaman ya bayyana hakan ne bayan yaba wa mahajjatan kan yadda suka gudanar da aikin hajjin bana.

    Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin tallafa wa maniyyatan a shirye-shiryensu na komawa gida bayan kammala aikin hajji.

    A ranar Alhamis ne mahajjata 1,673,230 suka gudanar da hawan Arfa, ɗaya daga cikin ginshiƙan aikin hajji.

    Mahajjata 41,568 ne daga Najeriya suka isa kasar ta Saudiyya a wannan shekara domin sauke farali.

  3. An shigar da ƙarar Trump kan jibge jami'an tsaro ba da izinin gwamna a California ba

    Jami'an tsaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban Lauyan gwamnati a California ya shigar da ƙarar shugaba Trump a kotu sakamakon jibge rundunar tsaron tarayya da ya yi ba tare da izinin gwamna ba.

    An ce Mista Trump ya wuce gona da iri kuma ya taka ƴancin jihar a lokacin da ya kafa dokar da ta bai wa shugaban ƙasa damar tura tsaron tarayyar.

    Attoni Janar Rob Bonta ya zargi Trump da ƙokarin tayar da tarzoma saboda siyasa.

    An jibge jami'an rundunar tsaro ta tarayya a ƙofar gine-ginen gwamnati da ke Los Angeles, yayin da aka shiga rana ta uku a zanga-zangar Los Angeles game da kamen baƙin haure.

  4. SERAP ta buƙaci Tinubu ya dakatar da Wike rufe ofisoshin jakadanci 34 a Abuja

    Wike

    Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta buƙaci shugaba Bola Tinubu ya bai wa ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike umarnin janye barazanar da ya yi na rufe ofisoshin jakadancin ƙasashen waje 34 a Abuja.

    Martanin ƙungiyar na zuwa ne bayan da hukumar kula da babban birnin tarayya FCTA, ta ce ana bin aƙalla ofisoshin jakadanci 34 kuɗin haya tun 2014.

    Ofisoshin jakadanci da abin ya shafa sun haɗa da na Ghana, Thailand, Equatorial Guinea, Côte d’Ivoire, Rasha, Philippines, Netherlands, Turkiyya da Guinea, Ireland, Uganda, Iraqi, Zambiya, Tanzaniya, Jamus, Kongo, Venezuela da Koriya da Trinidad da kuma Tobago.

    Sauran sun haɗa da Masar, Chadi, Indiya, Sudan, Kenya, Zimbabwe, Ethiopia, Indonesiya da Tarayyar Turai da Switzerland da Saudiyya da China da kuma Afirka ta Kudu.

    Wata sanarwa da SERAP ta fitar a shafinta na X ranar Litinin, ta yi gargaɗin cewa barin Wike ya ɗauki matakin zai saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjeniyoyin hulɗar diflomasiyya.

    "Tinubu ya gaggauta dakatar da Wike daga ɗaukar wannan mataki na son rufe ofisoshin jakadanci 34 a Abuja. Sashe na 22 sakin layi 1 na yarjejeniyar Viena ya bayyana cewa ofisoshin jakadanci wurare ne da ba za a iya kutsa musu ba ko take su," in ji SERAP.

    A ranar 26 ga watan Mayu ne, Wike ya ba da umarnin ɗaukar mataki kan gine-gine 4,794 waɗanda ba su biya kuɗin hayarsu ba wanda ya kai na tsawon shekara 10 zuwa 43.

    FCTA dai ta ce ofisoshin jakadanci da abin ya shafa za su biya kuɗin tara da ya kai naira miliyan biyu ko uku.

  5. An fara musayar fursunoni tsakanin Rasha da Ukraine

    Rasha-Ukraine

    Asalin hoton, Telegram/Volodymyr Zelensky

    An fara sabuwar musayar fursunoni tsakanin Rasha da Ukraine. Babu tabbas ko fursinonin nawa aka yi nasarar musaya a yanzu.

    Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce an mayar da rukunin farko na sojojin Rasha ƴan ƙasa da shekaru da biyar a madadin adadinsu na ƙasar Ukraine.

    Shugaba Zelensky ya wallafa hoton wadanda aka saki, kawunansu a aske rataye da tutar ƙasar ana gaisawa da su a wani wuri da ba a bayyana ba.

    Ya ce za a kai mataki na gaba cikin kwanaki ƙalilan amma ya bayyana yanayin da ake ciki a matsayin mai wahala.

    Ɓangarorin biyu masu yaƙar juna sun amince da musayar fursunoni da kuma gawawwakin dakarun da suka mutu ne yayin wata tattaunawar kai-tsaye a birnin Santambul.

  6. Ƴansanda sun kama mutum 27, sun ƙwato muggan makamai a Kaduna

    Kaduna

    Asalin hoton, Kaduna Police Command

    Ƴansanda a jihar Kaduna sun ce sun kama mutum 27 waɗanda ake zargi da aikata laifuka daba-daban.

    Wata sanarwar da mai magana da yawun ƴansandan jihar DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce an samu nasarar kama ɓata-garin ne bayan wani samame da ta kai maɓoyarsu a yankin Kawo.

    "Mun kai samamen ne jiya Lahadi a lungu da sako na yankin Kawo. Abin ya kai ga kama mutum 27 da ake zargi da aikata laifuka har ma da ƙwato muggan makamai," in ji Mansir.

    Ya ce cikin makaman da suka ƙwato sun haɗa da wuƙaƙe da adduna da fartanyu da kuma ƙunshin ganyayyaki da ake kyautata zaton tabar wiwi ce da kuma sauran kayan maye.

    Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Rabiu Muhammad ya ƙara nanata ƙoƙarin rundunar wajen ganin an mutunta doka da oda a faɗin jihar.

    Kaduna

    Asalin hoton, Kaduna Police Command

    Ya ƙara da cewa Kaduna jiha ce mai zaman lafiya, don haka ba za a bari wasu ɓata-gari ko masu son aikata laifi su wargaza zaman lafiyar jihar ba.

    Ya kuma gargaɗi duk masu son tayar da hankali da su guji yin haka ko kuma su fice daga jihar, saboda ƴansanda za su ci gaba da farautarsu ko ina suka shiga a faɗin jihar.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ayyukan masu ƙwacen waya ke ƙara kamari a jihar, inda wani mai ƙwacen waya ya hallaka wani soja a gadar Kawo a jiya Lahadi.

  7. Antonio Guteres ya ja hankalin duniya kan tekuna

    Tekuna

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya shaida wa taron koli na duniya kan teku cewa kar a yi watsi da yanayin da manyan tekuna ke ciki.

    Hukumar Duniyar wadda ke da iko ƙarashin tekunan zata gudanar da taro a watan Yuli don tattaunawa game da hakar ma'adinai.

    An ayyana batun a matsayin na gaggawa bayan shugaba Trump ya shirya fara aikin haƙar ma'adinai cikin tekuna.

    Mista Guterrs ya ce "a yau muna da damar mayar da abinda aka rasa lokaci mai tsawo a baya.

    A shirya taron a birnin Nice da nufin duba batutuwan yawan kamun kishin a tekuna da gurbacewarsu da kuma sauyin yanayi.

  8. Isra'ila ta ce ta ƙwace jirgin ruwan ƴan gwagwarmaya da ke son kai agaji Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce sojojin ƙasar sun karɓe ragamar wani jirgin ruwan ƴan gwagwarmaya yan sa-kai, da suka lashi takobin kangarewa haramcin Isra'ila, don kai agaji har zirin Gaza.

    Wakiliyar BBC ta ce mutane goma sha biyu ne a cikin jirgin, kuma an musu bidiyon mintuna kaɗan kafin yanke sadarwarsu, an gansu sanye da rigunan ruwa, suna ihu, yayin da dakarun Isra'ilar ke daka masu tsawa suna neman su jefa wayoyinsu cikin ruwa.

    An barbaɗa wa jirgin wani sinadari mai kama da hayaƙi don hana shi ganin gabansa kafin yi masa ƙawanya.

    Za a kai su wata tashar jirgen ruwa ne da ke Isra'ila, daga nan a tasa keƴarsu zuwa gida.

    Fasinjojin jirgin sun haɗa da ƴar gwagwarmayar yaƙi da matsalar sauyin yanayin nan yar Sweden Greta Thunberg, da wata ƴar majalisar tayayyar Turai kuma Bafaranshiya Rima Hassan.

  9. Ra'ayoyin mahajjata na bana

    Bayanan bidiyo, Latsa alamar da ke sama domin kallo
  10. Malaman makarantar firamare a Nijar sun tsunduma yajin aiki na gargaɗi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kawancen ƙungiyoyin malaman makaranta na a jamhuriyar Nijar da ake kira Dynamique ya saké tsunduma wani sabon yajin aiki na kwanaki biyar daga wannan ranar Litinin.

    A wannan karon ƙawancen ya tsananta matsayinsa inda a yanzu zai haɗa yajin aiki da azumi a ranakun Litinin da Alhamis da kuma gudanar da jami'in sallah da addu'o'i a ranar Juma'a.

    Kazalika malaman sun yi barazanar bayar da maki kyauta ga dalibai a jarabawar makarantun firamare da na sakandare.

    Sati biyar kenan a jere da malaman makarantar ke yajin aiki ba tare da gwamnatin ta amince ta zauna da su ba domin cimma matsaya kan jerin koke-kokensu da ke gabanta.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kamar makonni biyu a gudanar da jarrabawar kammala karatun shekara a makarantun ƙasar.

  11. 'Idan ba a yashe Alo Dam ba za mu iya fuskantar matsala a Borno'

    ..

    Asalin hoton, Borno Gov/X

    Gwamnatin jihar Borno ta yi kira ga gwamnatin shugaba Tinubu ta hanzarta daukar mataki kan ɗan kwangilar da ta baiwa aikin yashe dam din Alou da ya haifar da ambaliya a bara.

    Ta ce duk da cewar sun yashe wani sashe na dam din amma, har yanzu akwai babbar barazana da za a iya fuskantar mumunar ambaliya.

    Kwamishinan yaɗ labarai da harkokin tsaro na jihar Borno, Farfesa Umar Tar da harkkokin tsaro ya shaida wa BBC cewa an bayar da kwantaragin kuma minista ya je ya ƙaddamar da aikin.

    "Har yanzu ba mu ga ƴan kwangila sun zo domin fara aikin ba kuma yanzu ga damuna ta riga ta sauka. Idan ba a yi aikin nan da wuri ba to idan ruwa ya zo ya yi halinsa to lallai za a samu matsala. Ya kamata ace an yashe ruwan saboda irin cunkushewar da ya yi. Idan aka yashe shi to ko ruwa ya zo da yawa ba zai ambaliya ba." In ji Farfesa Tar.

    A damunar bara ne dai madatsar ruwa ta Alo Dam ta cika ta tunbatsa inda ta kuma karye wani abu da ya janyo ambaliar ruwa da ya haddasa asarar rayuka da ta dukiyoyi a birnin Maiduguri.

  12. Iran ta gargaɗi ƙasashen Turai kan shirin tozarta ta dangane da makamashin nukiliya

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta gargaɗi ƙasashen Turai, game da mara baya ga wani ƙuduri da ta kira na tozartata a lokacin da hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya za ta yi taro a ranar Litinin.

    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Aragchi ya ce yin hakan zai zama babban kuskure.

    Ana sa ran Amurka da Birtaniya da Faransa da Jamus za su goyi bayan ƙudurin a taron kwamitin gudanarwa na hukumar ta IAEA, wanda ke zargin Iran da ayyukan nukiliya a asirce da kuma ƙin bayyana dukkan makamanta na nukiliya.

    A halin da ake ciki dai, tattaunawar nukiliyar Amurka da Iran a Oman ta kasa yin gaba ta kasa baya.

    Shugaban Majalisar Dokokin Iran Mohammad Bagher Ghalibaf, ya shaida wa kafofin watsa labaran ƙasar cewa Amurka ba ta sanya batun cire wa ƙasar takunkumi a maganar ba, yana mai bayyana shugaba Trump a matsayin wanda yake mafarki.

    Ko a makon da ya gabata sai da jagoran addinin ƙasar ta Ira, Ayatollah Ali Khamanei ya caccaki Amurka inda ya bayyana ta da "mai ɗagawa da shisshigi" da ke yi wa ƙsarsu katsalanda.

    "Me aka yi a kai Amurka da har za ta faɗa mana abin da ya kamata mu yi. Batun makamashin nukiliya abu ne da ya shafi Iraniyawa." In ji Khamenei.

  13. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'ƴan ta'adda" da dama a maɓoyarsu

    Da dukukun ranar Litinin, dakarun rundunar Haɗin kai sun ƙaddamar da hare-hare ta sama da ƙasa kan cibiyoyin ƴan Boko Haram da ISWAP da ke Nzalgana a ƙaramar hukumar Gujba da Timbuktu Triangle.

    Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na X ta ce rundunar ta ce sakamakon hare-haren ya haifar da kisan ƴan ƙungiyar da jagororinsu da suka haɗa da Ameer Malam Jidda wanda babban kwamanda ne a ƙauyukan a Ngorgore da Malumti.

    Bugu da ƙari, an samu ƙarin gawarwakin ƴan ta'adda sannan an ƙwato makamansu a wani hari da aka kai Malamfatori.

    A baya-bayan nan dai ana ta samun ƙaruwar hare-haren Boko Haram da ISWAP, inda ko a watan da ya gabata sai da ƙungiyar ta kai wani harin jirgi maras matuƙi a garin Marte da ke jihar Borno.

  14. Isra'ila ta ce ta gano tare da ƙwato gawar Mohammed Sinwar

    ..

    Asalin hoton, IDF

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta gano, tare da ƙwato gawar babban hafsan sojin Hamas, Mohammed Sinwar, makonni uku bayan da ta sanar da mutuwarsa a wani harin da ta kai ta sama.

    Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce binciken ƙwayoyin halitta na DNA, ya tabbatar da cewa gawarsa ce aka gano a wani ramin ƙarƙashin ƙasa a Khan Younis.

    Mai magana da yawun sojin Isra'ilar, ya ce an kuma samu gawar wani babban shugaban Hamas, Mohammad Shabana a wurin.

    Mohammed Sinwar dai ƙane ne ga Yahya Sinwar, shugaban Hamas da sojojin Isra'ila suka kashe a bara.

    Ana zargin yana kan gaba cikin waɗanda suka tsara, tare da kai harin ranar 7 ga watan Oktoba a Isra'ila.

  15. Umarnin Trump na hana ƙasashe 12 shiga Amurka ya fara aiki

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Umarnin nan da shugaban Amurka Donald Trump ya bayar na haramta wa ‘yan ƙasashe goma sha biyu shiga Amurka ya fara aiki a ranar Litinin da misalin ƙarfe biyar agogon GMT.

    Wani ɓangare ne na alƙawarin da ya yi na taƙaita ƙaurar jama'a.

    Kasashen da abin ya shafa sun hada da Afghanistan, da Myanmar, da Chadi, da Jamhuriyar Congo, da Equatorial Guinea, da Eritrea, da Haiti, da Iran, da Libya, da Somalia, da Sudan da kuma Yemen.

    An kuma sanya haramcin rabi da rabi kan karin wasu kasashe bakwai, da suka hada da Burundi, da Cuba, da Laos, da Saliyo, da Togo, da Turkmenistan, da Venezuela.

    A wa'adinsa na farko ma, Shugaba Trump ya haramtawa matafiya daga kasashe bakwai masu rinjayen musulmi shiga AMurkar.

  16. Wani soja ya rasa ransa a hannun mai ƙwacen waya a Kaduna

    DIV 1 Kaduna

    Asalin hoton, DIV 1

    Wani mai ƙwacen waya ya kashe wani soja bayan da ya nemi ya miƙa masa wayar da ke hannunsa.

    Wata sanarwa da rundunar sojin Div 1 da ke Kaduna ta fitar ta ce Lt Commodre M Buba da ke kwas na shiga layin manyan sojoji ya samu fanco a tayar motarsa abin da ya tilasta masa tsayawa a daidai gadar sama ta Kawo da ke Kaduna, inda fitowarsa ke dawuya sai wani ya zo ya same shi ya nemi ya ba shi wayarsa.

    Sai sojan ya nemi sanin dalilin bayar da wayar abin da ya sa mutumin ya fitar da wuƙa ya caka masa a ƙirji.

    Wani ɗn sintiri ya yi ƙoƙarin ceton sojan amma shi ma mutum ya daɓa masa wuƙar a hannunsa.

    An kai Lt Commodore asibitin Manalal amma kuma rai ya yi halinsa.

    Sai dai kuma mutanen da ke kusa da wurin da abin ya faru sun yi wa makashin tara-tara inda suka hallaka shi shi ma.

  17. Muna kira ga Tinubu ya mayar da hankali kan gyran Najeriya ba zaɓen 2027 ba - ACF

    Tinubu

    Asalin hoton, Bayo/X

    Ƙungiyar Tuntuɓar Juna ta Arewacin Najeriya ta yi kira shugaba Tinubu da manyan muƙarraban gwamnatinsa da su mayar da hankali wajen ganin sun kyautata rayuwar ƴan Najeriya maimakon gangamin yaƙin neman a sake zaɓen Tinubu a 2027, inda a cewar ƙungiyar hakan ya yi wuri.

    A wata sanarwa da kakakin ƙungiyar na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ta taya Musulmi murnanr Babbar Sallah, ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta dangane da taɓarɓarewar tsaro da tsadar rayuwa da rashin wutar lantarki da matsalolin lafiya, ilimi da karyewar darajar Naira da tashin farashin kayan abinci.

    Ƙungiyar ta kuma nuna takaicinta yadda duk da irin waɗannan ƙalubale amma jam'iyyar APC ta fi mayar da hankali kan gangamin yaƙin neman zaɓen Tinubun a 2027.

    Idan dai ba a manta ba a watan da ya gabata ne dukkanin gwamnaonin jam'iyyar APC 22 a faɗin ƙasar suka amince da cewa Bola Tinubu ne ɗan takararsu a zaɓen 2027 mai zuwa, wani al'amari da ya janyo cece-kuce a Najeriya.

  18. Mahajjata na kammala aiki ranar Litinin

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A ranar Lahadin da ta gabata ne alhazai miliyan 1.8 suka kammala aikin Hajjin bana a birnin Makkah na kasar Saudiyya, bayan kammala jifan shaiɗan a Jamarat da ke Mina.

    Ko da yake a shari'ance a ranar Litinin ne ranakkun aikin Hajjin shida ke cika, saboda yadda addini ya bai wa mahajjatan damar kammalawa cikin kwanaki biyar ko shida inda kuma mafi yawan alhazan ke zaɓar kammalawa cikin kwana biyar ɗin.

    Masu son ƙarawa su ma za su kammala ne ranar Litinin da jifan shaiɗan da ake kira Jamrat a rana ta huɗu maimakon uku da dama ke yi.

    Gabanin jifan Jamarat ɗin, mahajjatan sun yi hawan Arafa da kwanan Muzdalifah da Ɗawaful Ifadah da kuma Sa’ayi.

  19. Shin ko mata za su koma auren mazan da ba su kai su aji ba?

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    "Yanzu haɗa aure a tsakanin matasa yana wahala, saboda akwai mata masu ilimi sosai sama da maza," in ji Nadia Steiber, masaniyar halayyar ɗan'adam a Jami'ar Vienna da ke Austria.

    Saboda haka, mata da dama suna neman abokan zama ne masu ilimi irin nasu ko matsayin rayuwa.

    A lokuta da dama suna ɓigewa ne da auren wanda suka samu kawai ba dole sai yadda suke so ba, lamarin da ta ce ana bayyanawa da "rage aji".

    A baya dai a kan bai wa mata mazajen da suka fi su aji ta fuskar ilimi ko wadata inda suke kasancewa ƙarƙashin ikon mazan ta yadda sai yadda suka juya su.

    To amma yanzu da alama al'amarin yana sauyawa fiye da yadda ake tunanin a cikin dukkannin al'ummomin duniya.

  20. Tambayoyi tara da ƴan Afirka ke yi kan dokar hana shiga Amurka da Trump ya sa

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da sabuwar dokar hana tafiye-tafiye da ta shafi ƙasashe 12 - bakwai daga ciki sun fito daga Afrika.

    Mun bi diddigin abin da mutane a faɗin nahiyar suke tambaya a intanet ta hanyar amfani da manhajar Google Trends da kuma shafukan sada zumunta na BBC Afrika.

    Bakwai daga cikin ƙasashe 12 da dokar ta hana shiga Amurka sun haɗa: Chadi da Congo-Brazzaville da Equatorial Guinea da Eritrea da Libya da Somalia da kuma Sudan.

    Sauran su ne Afghanistan da Myanmar da Haiti da Iran da kuma Yemen.