Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 19/11/2024

Taƙaitattu

Ukraine ta harba makami mai cin dogon zango zuwa Rasha - Kremlin

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Annur Muhammad da Isiyaku Muhammed

  1. An yanke wa ɗan TikTok ɗaurin wata 32 a gidan yari

    ...

    Asalin hoton, Swaibu Ibrahim / BBC

    Wani matashi ɗan shekara 21 ya zama ɗan TikTok na baya bayan nan da aka tura gidan yari a Uganda bayan ya wallafa wani bidiyo da aka ce yana cin mutuncin shugaba Yoweri Museveni.

    Emmanuel Nabugodi ya bayyana ne a gaban kotu a ranar litinin bayan ya amsa laifinsa a makon da ya gabata kan wasu tuhume-tuhume guda huɗu da suka haɗa da kalaman nuna ƙiyayya da yaɗa munanan bayanai game da shugaban ƙasar.

    An yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 32 a gidan yari.

    Nabugodi, wanda ya shahara wajen wallafa abubuwan barkwanci ga mabiyansa 20,000, ya yi bidiyo na wani shari'ar izgili da ake yi wa shugaban ƙasa. A ciki ya yi kira da a yi wa Museveni bulala a bainar jama'a.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun yi ta korafin yadda ake tauye ƴancin faɗin albarkacin baki a ƙasar, suna masu zargin cewa shugaban - wanda ke kan karagar mulki tun 1986 - ba ya lamuntar suka a gare shi.

    A watan Yuli, an yankewa Edward Awebwa hukuncin shekaru shida akan irin wannan tuhuma da aka yi wa Nabugodi. Wasu uku kuma suna jiran hukunci kan abubuwan da suka wallafa a shafukan sada zumunta sada zumunta.

    A lokacin da take zartar da hukuncin Nabugodi, Stellah Maris Amabilis, babbar alƙaliyar kotun Entebbe, ta ce bai yi nadama ba, kuma hukuncin zai taimaka wajen daƙile sukar da ake kai wa miutane a shafukan sada zumunta ciki har da na shugaban ƙasa.

  2. Ɗaruruwan 'yan Nijar da ke tsare a Libya cikin 'ƙasƙanci' sun koka ga gwamnatinsu

    Ɗaruruwan 'yan cirani a zaune

    Asalin hoton, Twitter/Kwesi Quartey

    'Yan ƙasar Nijar, aƙalla 300 ne ake zargin hukumomin Libiya sun kama tare da tsare su a cikin wani mawuyacin hali na rashin kula tsawon wata da watanni.

    A cikin wani bidiyo da ake ta yaɗawa ta shafukan sada zumunta an ga ɗaruruwan mutanen cunkushe a cikin wani ɗaki suna kira ga hukumomin ƙasar ta Nijar da su kai masu ɗauki.

    Shugaban hukumar ƙoli ta 'yan Nijar mazauna Libya, Alhaji Sani ya tabbatar da cewa bidiyon na gaskiya ne, mutanen an kama su ne wasu a wajen aikinsu wasu kuma sun shiga ƙasar a kan hanyarsu ta zuwa Sabha aka kama su.

    Alhaji Sani wanda ya koka da halin da 'yan Nijar ɗin ke ciki ya ƙara da cewa ba ma a nan kaɗai ake tsare da 'yan Nijar ɗin a Libya ba akwai wasu ma a babban birnin ƙasar ta Libya, Tripoli waɗanda ya ce tun ma kafin azumi suke tsare.

    Ya ce ba abin da ba su yi na ganin hukumomin Nijar sun kawo musu ɗauki sun shiga lamarin a sake su amma hukuma ba ta yi hakan ba.

    Yanzu dai ƙungiyoyin fararen hula da na kare haƙƙin bil'Adama a Nijar ɗin sun shiga kira ga gwamnatin sojin Nijar da ta yi abin da ya dace a kan lamarin.

  3. An kashe 'yan daba masu satar kayan agaji a Gaza - Hamas

    Motar kayan agaji

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Hamas ta ce jami'an tsaronta sun kashe sama da ƴan daba ashirin waɗanda suke da hannu wajen satar kayan agaji a Gaza.

    Tun da farko, ma'aikatan jin ƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya sun ce an kai wa motocinsu sama da 100 hari a ranar Asabar.

    Kodayake babu wata hanya da za a iya tabbatar da iƙirarin ma'aikatar kai tsaye, amman ma'aikatan asibiti a Kudancin Gazar sun bada rahoton cewa an kai musu gawarwaki bayan faruwar lamarin.

    Wakilin BBC ya ce Hamas ce ke tabbatar da tsaron yankin, ga shi kuma tana yaƙi da Isra'ila saboda haka waye zai kula da yankin?

  4. Wata mota ta faɗa kan mutane a China

    Motar 'yansanda

    Asalin hoton, AFP

    Wata mota ta faɗa kan wasu mutane da ke gaban wata makaranar firamari a tsakiyar China, inda mutane da dama suka jikkata.

    Ya zuwa yanzu dai ba a sani ba ko mai motar, wanda yake hannun hukuma a yanzu, ya faɗa kan mutanen ne da gangan ko kuma hatsari ne.

    Haka kuma ba a samu cikakken bayanin yawan mutanen da suka mutu ba.

    Wani bdiiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna mutane sheme a ƙasa, yayin da a gefe guda ake ta dukan wani mutum.

  5. An ɗaure masu rajin Dumukuraɗiyya 47 a Hong Kong

    Masu fafutuka a Hong Kong

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Kotu a Hong Kong ta yanke wa masu fafutukar Dumukuraɗiyya 47 hukuncin ɗauri a wata shari'a mafi girma da ta shafi tsaron ƙasa a yankin tun bayan da Beijing ta murƙushe 'yan hamayya.

    An same su da laifin yin zagon ƙasa bayan da suka yi yunƙurin shirya zaɓe.

    An yanke wa waɗanda suka jagoranci yunƙurin hukuncin shekara goma a gidan yari.

    Shari'ar ta ɗauki hankalin 'yan yankin sosai inda gommai suka yi layi a wajen kotuntun kafin ranar yanke hukuncin ta zo domin samun shiga cikin kotu.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci zaman kotun ya ce Amurka ta yi kakkausar suka kan hukuncin.

  6. Rasha ta yi alƙawarin ɗaukar mataki mai tsauri idan Ukraine ta yi amfani da makaman Amurka masu cin dogon zango

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Rasha ta ce idan har Ukraine ta yi amfani da makaman Amurka masu cin dogon zango wajen kai mata hari, hakan zai matuƙar tayar da zaune tsaye.

    Idan harin ya auku, zai zama karo na farko da "Amurka ta shiga cikin yaƙin dumu-dumu."

    Shugaban ƙasa Joe Biden ne ya sahale wa Ukraine amfani da makaman masu linzami domin kai hare-hare a Rasha, wanda ke zuwa kimanin wata biyu kafin ya sauka daga kujerar mulki.

    Sai dai babu tabbaci ko an shawarci zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Donald Trump kafin a ɗauki wannan mataki.

    Ukraine ta mallaki makamin US ATACMS, wanda ke cin zangon kilomita 300 da na Faransa wanda shi ma yake cin irin wannan zangon, amma ƙasashen yamma suka hana ƙasar amfani da su wajen kai wa Rasha hari.

    Amma Biden yanzu ya sahale wa ƙasar amfani da makaman a yaƙin wanda aka fara a ranar 24 ga Fabrairun 2022.

    Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce ba za a sanar da fara amfani da makaman ba, kawai za a ji su ne.

    A lokacin yaƙin zaɓe, Trump ya yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙin cikin awa 24 idan ya zama shugaban ƙasa.

  7. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.