Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 25/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da Isiyaku Muhammed

  1. Rasha ta kama tsohon sojan Birtaniya da ke yaƙi a Ukraine

    Dakarun Rasha sun kama wani ɗan Burtaniya a cikin mayaƙan Ukraine, kamar yadda rahotanni suka nuna.

    A wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sadarwa, an ga wani mutum sanye da kayan sojoji yana cewa sunansa Jams Scott Rhys Anderson mai shekara 22, inda ya ce shi tsohon sojan Burtaniya ne.

    Kamfanin dillancin labarai na Tass da ke Rasha ya ruwaito daga wata majiya daga rundunar sojin ƙasar cewa, an kama wani "sojan haya a yankin Kursk" na Rasha, yankin da ke ƙarƙashin Ukraine tun a watan Agusta.

    Ofishin harkokin wajen ƙasar ya ce "suna tattaunawa da ƴanuwan ɗan Burtaniyar da aka kama."

    Scott Anderson, mahaifinsa, ya ce sai da ya roƙe ɗan nasa kada ya tafi Ukraine.

    "Ya ce yana so ya je saboda a tunananinsa abu ne mai kyau," in ji Mista Anderson a tattaunawarsa da Daily Mail.

    "Ɗana ya faɗa min cewa suna azabtar da fursunoninsu, wanda hakan ya sa nake fargabar irin azabar da zai sha."

    "Daga ganin bidiyon za ka fahimci yana cikin firgici da damuwa," in ji shi.

    A cikin da ke yawo, wanda aka fara wallafawa a kafar Telegram, an jiyo Mista Anderson yana bayyana wa wani wanda yake masa tambayoyi cewa ya yi aikin soja a Burtaniya tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.

  2. Gwamnan Edo ya kafa kwamitin binciken gwamnatin Obaseki

    A Najeriya, sabuwar gwamantin jihar Edo ta kafa kwamitin tantance kadarorin jihar mai mambobi 14 da zai binciki gwamantin da ta gada.

    Gwamnatin ta ce kwamitin zai fara aikinsa daga gobe Talata 26 ga wannan watan.

    Kafa kwamitin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na gwamnan Fred Itua, inda ya ce gwamna Monday Okpebholo ya kafa kwamitin ne ƙarƙashin Dr Ernest Afolabi Umakhihe.

    Tuni ɓangaren tsohon gwamnan jihar, Godwin Obaseki suka bayyana binciken da bita-da-ƙulli.

  3. Ƙungiyar SERAP ta buƙaci Tinubu ya bincika zargin badaƙala a ma'aikatar jinƙai

    Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya, ta buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu da ya gudanar da binciken kuɗi sama da naira biliyan 57 da ake zargin an sace ko sun ɓace daga ma’aikatar jinƙai da yaƙi da fatara ta tarayya a shekarar 2021.

    A cewar SERAP, binciken ya zama dole domin wanke gwamnatin tarayya daga zargin ɓoye masu aikata laifuka.

    Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen jin ƙai a sassa daban-daban na Najeriya.

  4. Isra'ila ta ce Hezbollah ta harba mata rokoki sama da 250

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Hezbollah ta harba mata rokoki kusan ɗari biyu da hamsin daga kan iyakar Lebanon a jiya Lahadi.

    Harin na ɗaya daga cikin mafi muni da Hezbollah ta kai tun fara rikicin tsawon wata biyu.

    Mutane da dama sun jikkata a arewaci da kuma tsakiyar Isra'ila.

    Harin na zuwa ne bayan hare-hare ta sama da Isra'ilar takai a tsakiyar birnin Beirut a ranar Asabar, wanda ma'aikatar lafiyar Lebanon ta ce an kashe mutum ashirin da biyar.

  5. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga nan sashen Hausa na BBC inda za mu riƙa kawo muku labaran muhimman abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya kuma leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.