Chelsea na hamayya da Arsenal kan Isak, City na son Zabarnyi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Chelsea ta shiga hamayya da Arsenal kan Alexander Isak - amma Newcastle United za ta buƙaci fam miliyan 115 kan ɗanwasan na Sweden mai shekara 25. (Teamtalk)

Aston Villa da AC Milan da Juventus na hamayya da Arsenal kan ɗanwasan gaba na Real Madrid Arda Guler, mai shekara 19, bayan da ƙungiyar ta ba ɗanwasan na Turkiya damar tafiya a matsayin aro. (Caughtoffside)

Kungiyar Hamburg ta Jamus na nazarin ɗaukar tsohon kocin riƙon ƙwarya na Manchester United Ruud van Nistelrooy a matsayin sabon kocinta idan ta raba gari da Steffen Baumgart. (Sky Sports Germany)

Kocin Fenerbahce Jose Mourinho ya yi watsi da rahotannin da ke cewa yana son ɗauko ɗanwasan Al-Nassr da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara 39. (Goal)

Ɗanwasan tsakiya na Lille da Ingila Angel Gomes, mai shekara 24, na shirin dawo wa zuwa Manchester United bayan sabon kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya nuna buƙatarsa. (Caughtoffside)

Nottingham Forest na tattaunawa da ɗanwasan baya Ola Aina kan sabuwar yarjejeniya. Kwangilar ɗanwasan na Najeriya mai shekara 28 za ta kawo ƙarshe a bazara wanda hakan ke nufin zai iya tattaunawa da wata ƙungiyar daga Janairu. (Athletic - subscription required)

Kocin Crystal Palace Oliver Glasner zai samu goyon bayan yin sabon zubin sabbin ƴanwasa a watan Janairu domin farfaɗo da ƙungiyar da ke ƙasan tebur. (Football Insider)

Real Sociedad ta gaza shawo kan ɗanwasanta na Spain mai shekara 25 Martin Zubimendi, mai shekara 25 da ke son barin ƙungiyar yayin da Arsenal da Liverpool ke ribibinsa (Todofichajes - in Spanish)

Wayne Rooney na son ɗauko ɗanwasan gaba na Liverpool da Ingila Jayden Danns, mai shekara 18, domin ƙarfafa gaban Plymouth. (Sun)

Manchester City na son ɗanwasan baya na Bournemouth Illia Zabarnyi kuma ƙungiyar na iya sayar da ɗanwasan mai shekara 22 ɗan ƙasar Ukraine domin samun kuɗi. (Football Insider)