Mutane 16 sun ɓace bayan nutsewar jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya
Hukumomi a ƙasar Masar sun ce mutane 16 sun ɓace, ciki har da ƴan kasashen waje, sannan an ceto 28 bayan wani jirgin ruwan ƴan yawon buɗe ido ya nutse a tekun Bahar Maliya.
Biyu daga cikin waɗanda suka ɓata ƴan Burtaniya ne, kamar yadda BBC ta fahimta.
Ƙasar Finland ta tabbatar da cewa ba a ga ɗaya daga cikin ƴan kasarta ba, yayin da hukumomi suka ce ƴan ƙasar Masar huɗu ma sun ɓace.
Hukumomin kasar ba su bayyana dalilin da ya haddasa nutserwar jirgin mai ɗauke da mutane 44 ba, sai dai bayanai daga waɗanda suka tsira sun nuna cewa igiyar ruwa ce ta afkawa jirgin da ya yi sanadin kifewarsa.
Masu hasashen yanayi sun yi gargadi game da tafiya kan teku a ranar Lahadi da Litinin.
Jirgin mai suna 'Sea Story' ya bar tashar jiragen ruwa kusa da Marsa Alam ranar Lahadi don balaguron na kwanaki biyar, a cewar jami'ai.
Gwamnan yankin Manjo-Janar Amr Hanafi ya ce an gano waɗanda suka tsira ne a yankin Wadi el-Gemal da ke kudancin Marsa Alam, kuma suna samun kulawar da ta dace a asibiti.