Farashin man fetur ya sake haura dala 100 kan kowanne ganga

Asalin hoton, Getty Images
Farashin ɗanyen man fetur samfurin Brent ya sake haura sama da dala 100 kan kowanne ganga, bayan ya yi ƙasa sosai a ranar Litinin.
A kasuwannin Asiya da safiyar Talata, farashin fetur ya ƙaru da kashi 3.75 zuwa dala 103.69.
A ranar Litinin ne dai farashin man ya faɗi da fiye da kashi 10 bayan da Donald Trump ya ɗage shirin kai hare-hare kan tashoshin lantarkin Iran bayan ya ce ya tattauna da Iran lamarin da Iran din ta musanta.
Dalilin haka ne masu zuba jari suke sake duba wannan lamari.


