MDD ta nemi Isra'ila ta ba da damar shigar da ƙarin kayan abinci a Gaza

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga Isra'ila ta ba da damar shigar da karin kayan agaji zuwa Gaza, bayan da dubban mutane suka kutsa cikin rumbun hukumar da ke tsakiyar Zirin.
An bayyana cewa an harbe mutane biyu, kana aka take ƙarin wasu biyu da mota yayin balahirar.
Hotunan bidiyo sun nuna mutane ɗauke da jakunkuna da kwalaye suna ficewa daga rumbun.
A wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, jakadan Isra'ila a MDD ya zargi majalisar da cin dunduniyar kasarsa, ta hanyar bin hanyoyin da suka saɓawa ƙasarsa wajen rabon kayan jin kai a Gaza.

