Ajax ta ɗauki Heitinga sabon kociyanta

Asalin hoton, Getty Images
Ajax Amsterdam ta naɗa John Heitinga a matakin sabon kociyanta, kamar yadda ƙungiyar da take buga Eredivisie ta sanar ranar Asabar.
Heitinga ya fara taka leda a makarantar ƙungiyar Ajax, wanda ya yi kaka bakwai da rabi a babbar Ajax a matakin mai tsare baya, shi ne mataimakin Arne Slot da Liverpool ta lashe Premier League a kakar da aka kammala.
Heitinga ya maye gurbin Francesco Farioli, wanda ya yi murabus bayan kaka ɗaya a kan aikin.
Ajax mai kofin babbar gasar tamaula ta Netherlands guda 36, ta kare a mataki na biyu a kakar bana, bayan da PSV Eindhoven ta lashe kofin - rabon Ajax da kofin tun 2021-22.

















