Rufewa
Masu bin shafin namu a daidai wannan lokaci muke sallama da ku.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 05/01/2025.
Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin namu a daidai wannan lokaci muke sallama da ku.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.
Biranen Kansas da Missouri, da wasu jihohin takiyar Amurka biyu na fuskantar saukar dusar ƙanƙara mafi girma cikin shekara 10.
A jihar Kansas, wata iska mai ciek da tsananin sanyi ce ke kaɗawa, yayin da ake hasashen yanayi zai kai maki -29 a ma'aunin salshiyos.
Kamfanin jiragen jiragen sama na 'American Airlines' ya fitar da gargaɗi ga filayen jirage kusan 50 a faɗin tsakiyar ƙasar da da na kusa da yankin tekun Atlantica
Tituna da bishiyoyi sun kasance a cunkushe yayin ake amfani da na'urori wajen share dusar da ke sauka.
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka, FBI ta ce mutumin da ya kai hari New Orleans a ranar sabuwar shekara har ya kashe mutum 14, ya ziyarci birnin har sau biyu watanni kafin ya ƙaddamar da harin.
Masu bincike sun ce Shamsud-Din Jabbar ya naɗi bidiyoyin wurin da ya kutsa da babbar motar cikin dandazon jama'a.
Bayan harin 'yansanda sun samu nasarar harbe mutumin - wanda ya yi mubaya'a ga ƙungiyar IS.
Jami'ai sun yi amanna cewa maharin ya shirya tare da kai harrin shi kaɗai.Suna kuma bincike game da tafiye-tafiyen da ya yi zuwa ƙasashen Canada da Masar.
Yankin tsakiyar Amurka na fuskantar tsananin hunturu hade da saukar dusar ƙanƙara da, lamarin da ya jefa yankin cikin tsananin sanyi.
Miliyoyin Amurkawa na fargabar fuskantar saukar dusar ƙanƙara da suka jima ba su ga irinta ba a cikin fiye da shekara 10.
A jihar Kansas, wata iska mai ciek da tsananin sanyi ce ke kaɗawa, yayin da ake hasashen yanayi zai kai maki -29 a ma'aunin salshiyos.
Kamfanin jiragen jiragen sama na 'American Airlines' ya fitar da gargaɗi ga filayen jirage kusan 50 a faɗin tsakiyar ƙasar da da na kusa da yankin tekun Atlantica.
Wasu 'yanbindiga a jihar Katsina da ke arewa masu yammacin Najeriya sun kai hari gidan shugaban ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah na jihar, Alhaji Siraja Ahmadu Mairana, inda suka kashe shi tare da sace matansa biyu.
Shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na ƙasa, Baba Usman Jandarma ne ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, wanda ya ce auku a ranar Asabar da daddare.
''Har gida suka je suka kashe sannan suka sace matansa biyu da kuma 'yarsa guda'', in ji Baba Jandarma.
Ya ƙara da cewa yanzu haka suna jiran binciken jami'an tsaro, domin gano waɗanda suka aikata wannan ta'asa tare da kuɓutar da iyalin nasa.
Lamarin na zuwa ne kusan shekara biyu kenan bayan ɓacewar tsohon shugaban ƙungiyar na jihar, Injiniya Mannir Atiku Lamido, kuma har yanzu babu labarinsa.
Kwanaki biyu da ɓacewar tasa ne dai aka tsinci motarsa tare da wayoyinsa na hannu a ciki a garin Mararrabar Jos na jihar Kaduna.
Kafar yaɗa labaran Somaliya ta ce aƙalla mayaƙan al-Shabab 10 aka kashe a lokacin wasu hare-hare da sojoji suka ƙaddamar bayan da suka samu tallafin Amurka ta sama.
Jami'ai sun ce babu farar hula ko guda da ya mutu sakamakon harin da aka kai a wani ƙauye da ke arewa maso yammacin birnin Kismayo mai tashar jiragen ruwa.
Abu ne dai mawuyaci a iya tabbatar da sahihancin rahotonnin.
Kusan shekara 20 kenan da sojojin Amurka ke taimaka wa dakarun ƙasar kan yaƙin da ƙungiyar al-Shabab.
A wannan wata ne ake sa ran aika dakarun wata sabuwar ƙawancen sojin Afirka mai dubban sojoji daga nahiyar zuwa ƙasar don fatattakar mahayƙan na al-Shabab.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kama hanyar zuwa Ghana a ranar Litinin - a bulaguronsa na farko zuwa wata ƙasar waje a 2025 - domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar, John Dramani Mahama da za a gudanar ranar Talata 7 ga watan Janairu.
Cikin wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar, ta ce Tinubu zai halarci bikin ne bisa gayyatar da zaɓaɓanen shugaban ƙasar ya yi masa bayan ya ziyarci Tinubu a Najeriya cikin watan Disamba.
''Tinubu da Mahama na da tarihin abota mai ƙarfi, kamar yadda Najeriya da Ghana suka jima da abota mai ƙarfi tsakaninsu'', in ji sanarwar.
Shugaba Tinubu matsayinsa na jagoran Ecowas zai haɗu da wasu shugabannin ƙasashen Afirka a wajen binkin rantsuwar, kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.
A watan Disamban da ya gabata ne aka zaɓi John Mahama - wanda tsohon shugaban ƙasar ne tsakanin 2011 zuwa 2017 - a matsayin sabon shugaban ƙasar Ghana.
Kylian Mbappe shi ne ya lashe ƙyautar Mahou Cinco Estrellas a matakin fitatcen ɗan wasa a watan Disamba.
Ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya buga wa Real Madrid wasa shida a cikin watan karshen shekarar 2024.
Daga ciki ya zura ƙwallo biyar a raga a karawar La Liga uku da Champions League da kuma Fifa Club World Cup da ya yi.
Ranar 18 ga watan Disamba Real Madrid ta lashe Intercontinental Cup, bayan doke Pachura 3-0 a karawar karshe, kuma Mbappe ya ci ƙwallo ɗaya daga ciki.
Ɗaruruwan mutane ne a wani ƙauye na Habasha mai tazarar kilomita 165 daga arewa maso gabashin babban birnin kasar Addis Ababa, ke barin gidajensu sakamakon wani dutse mai aman wuta, kamar yadda wani jami'i a yankin ya faɗa wa BBC.
Hayakin da ke fitowa daga tsaunin Dofan daga ranar Alhamis na cigaba da ƙaruwa," in ji wani mai suna Sultan Kemil.
Wani bidiyo da cibiyar nazarin ƙasa ta Habasha ta wallafa a shafinta na Facebook, ya nuna yadda tururi ke fitowa daga dutsen.
A cikin ƴan makonnin nan, an samu afkuwar girgizar ƙasa fiye da goma a kusa da Awash Fentale - wani yanki da ke fama da girgizar ƙasa a lardin Afar na Ethiopia.
Abdu Ali, wani babban jami'i a yankin Afar ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta FBC ta ƙasar Habasha cewa, ana ci gaba da aikin kwashe mutane daga yankin.
Ukraine ta kaddamar da wani sabon hari a yankin Kursk na Rasha, a cewar ma'aikatar tsaron Rasha.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce sojojinta na can suna ƙoƙarin lalata ƙungoyoyin Ukraine da suka kai harin.
Jami'ai a Ukraine sun ce suna yin wani shiri na sake kai farmaki.
Tun da farko, Ukraine ɗin ta kaddamar da mamaya kan yankin Kursk a watan Agustan bara, inda suka ƙwace iko da yankuna masu yawa.
A watannin baya-bayan nan, sojojin Rasha sun samu nasara a yankin, inda suka ƙori sojojin Ukraine suka ja baya, sai dai sun kasa fatattakarsu baki-ɗaya.
Shugaban gwamnatin Ostiriya mai ra'ayin mazan jiya, Karl Nehammer, ya ce zai yi murabus nan da kwanaki masu zuwa bayan da tattaunawar kawance tsakanin jam'iyyarsa ta People's Party da Social Democrat ta wargaje.
Nehammer ya ce sun kasa cimma yarjejeniya kan wasu muhimman batutuwa.
Ƙungiyoyin siyasa guda uku sun yi ta ƙoƙarin ganin sun cimma matsaya bayan da jam'iyyar Fredom party, mai kusanci da Rasha ta lashe zaɓe a watan Satumba.
Zaɓin da ya rage shi ne ko a bai wa jam'iyyar Freedom Party wadda ta lashe zaɓe damar kafa gwamnati ko kuma a sake wani sabon zaɓe idan hakan ya faskara.
Ƙungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sanar da cewa wasanta da Man United zai gudana kamar yadda aka tsara tun farko.
Hakan na zuwa ne bayan wani zama da aka yi domin duba yanayi sakamakon zubar dutsar ƙankara da ake fuskanta.
Tun da farko, lamarin ya janyo rufe filayen jirgin sama sai dai an sake buɗe su na wucin gadi.
Wani sako da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X ya ce: "Mun gode wa kowaye da ya taimaka wajen ganin an buga wasan a yau. Idan za ka yi tafiya zuwa Anfield to ka ɗauki matakan kariya. Sai mun haɗu a can."
Masana'antar Kannywood ta daɗe tana ƙyanƙyashe jarumai maza da mata, wasu sun tafi, wasu sun maye gurbinsu, kuma har yanzu ana cigaba da samun sababbin jarumai da suke jan zarensu a masana'antar.
Sai dai a zamanunnuka da suka shuɗe, an yi waɗanda suke shigowa masana'antar su yi finafinai kaɗan, sai su yi ɓatar dabo, a daina jin ɗuriyarsu baki ɗaya.
Amma akwai wasu waɗanda suka daɗe suna jan zarensu a masana'antar, inda suke yi shekaru suna fitowa a finafinai.
Wata jarida a ƙasar Rasha Izvestia ta ce an kashe ɗaya daga cikin wakilanta a wani harin jirgi marasa matuki da aka kai birnin Donetsk da aka yi ƙawanya a gabashin Ukraine.
Rasha ta zargi sojojin Ukraine da kai harin da gangan kan ɗan jaridar mai suna Alexander Martemyanov.
Kyiv dai ba ta ce uffan ba kan harin.
Jaridar ta Izvestia ta ce an afka wa wata motar farar hula ɗauke da ɗan jaridan nata ne yayin da take tafiya a kan wata babbar hanya a yankin da Rasha ta mamaye.
An bayar da rahoton cewa wasu ma'aikatan yaɗa labarai biyar sun jikkata a harin.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Rasha Maria Zakharova, ta yi Alla-wadai da lamarin, tana mai cewa kisan kai ne da aka aikata da gangan.
Hukumar karɓar haraji ta jihar Nasarawa ta ɓullo da shirin saka wa motocin sufuri sabon fenti da nufin inganta harkokin tsaro.
Hukuma ta ce za a yi hakan ne kuma don ƙara yawan kuɗaɗen shiga da ake samu.
Yanzu dai za a sauya wa motocin haya da keke-NAPEP launi domin a bambance tsakanin ababen hawa na haya da kuma waɗanda ba na haya ba. Launin ja ko tsanwa.
Hon Moses Abeh wanda ya wakilci gwamnatin jihar a taron kaddamar da tsarin, ya ce an ɗauki aniyar yin tsarin ne domin samar da lambobin tsaro da kume fentin ga direbobi domin kare kai daga ɓata-gari da ake kira 'One Chance'.
"Lambobin tsaron za su kunshi bayanan direba da suka haɗa da jihar da ya fito da kuma inda yake zama," in ji Moses.
Ya kuma ce dole sai an san ƙungiya da direba ke ciki domin kaucewa sajewa da ɓata-gari ke yi a matsayin direbobi.
Ƙungiyoyin direbobi da abin ya shafa sun nuna farin ciki da wannan sabon tsari, inda suka ce hakan zai sa a gano masu aikata laifi.
Sun kuma amince da fenti mai launin ja ko tsanwa wanda suka ce shi ya fi dacewa a saka wa motocin.
Rukunin na biyu na sojojin Guatemala 75 sun isa Port-au-Prince, babban birnin ƙasar Haiti domin karfafa tawagar rundunar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke marawa baya wanda ke da alhakin yaƙi da ƴan dabar da suka addabi ƙasar.
A ranar Juma'a ne rukunin farko suka isa ƙasar.
Mutane sun daɗe suna dakon lokacin da za a ƙarfafa wannan tawagar sakamakon rashin tasirin da ta yi wurin magance matsalar ƴan dabar da suka mamaye babban birnin kasar.
Kenya ce ke jagorantar tawagar wadda ta tura ƴan sanda kusan 400 a bara.
Wani rikici da aka danganta da kabilanci wanda ya barke tsakanin kauyukan Gululu da 'Yan-Kunama a jihar Jigawa, ya yi sanadin mutuwar mutum aƙalla tara.
Rikicin ya samo asali ne sakamakon zargin da aka yi wa wasu matasan Fulani da ɓalle wani shagon kayan masarufi, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki.
Sai dai zuwa yanzu, an samu nasarar shawo kan rikicin wanda kuma ya janyo asarar gidaje da dama.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ta Jigawa, DSP Lawan Shi'isu Adam, ya shaida wa BBC cewa tuni aka aika jami'an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar zuwa yankin domin kwantar da hankali.
"Za mu gudanar da bincike don ganin an kama waɗanda suka aikata wannan laifi da kuma hukunta su," in ji DSP Lawan.
Ya ce hankali ya fara kwanciya a garuruwan kuma jami'an tsaro suna ta kai kawo don tabbatar da cewa ba a sake samun tashin hankali ba.
Jihohin Kentucky da Virginia sun ayyana dokar ta-baci yayin da wata mummunar guguwar hunturu ke mamaye wasu sassan Amurka.
Guguwar ta zo da dusar ƙanƙara da kuma ruwan sama mai sanyin gaske.
Sama da mutane miliyan 60 ne rahotanni suka ce mummunan yanayin ya shafa.
Ƴan wasan ƙungiyar gasar NFL ta Kansas City Chiefs, sun maƙale a filin jirgin sama na garin Kansas na sa'o'i da dama lokacin da aka rufe shi na wani ɗan lokaci sakamakon guguwar.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce matakan tsaron sararin samaniyarta sun kakkaɓo wani makami mai linzami da aka harba daga ƙasar Yemen.
Rundunar ta IDF ta ce an harbo makamin kafin ya isa yankin Isra'ila.
Ƴan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran sun yi ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki kan Isra'ila a matakin da suka ce nuna goyon baya ne ga Falasɗinawa.
Barkan mu da safiyar Lahadi daga Sashen Hausa na BBC.
Ku kasance da mu a wannan shafin labarai kai-tsaye, domin kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da kuma sauran sassan duniya.
Ahmad Bawage ne zai jagoranci kawo labaran.