Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Jawabin sabuwar shekara da karɓar bashin Bankin Duniya
Wannan muƙala ce da ke kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata.
Tattalin arzikin Najeriya na farfaɗowa - Tinubu
A ranar ɗaya ga watan sabuwar shekara ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce tattalin arzikin ƙasar na ci gaba da farfaɗowa.
Yayin jawabinsa na sabuwar shekara da ya gabatar ranar Laraba, shugaban ya ce duk da dai shekarar 2024 ta zo da matsaloli da dama ga alummar ƙasar, ya na da yaƙinin cewa sabuwar shekarar 2025 za ta zo da abubuwan farin ciki da cigaba.
A cikin saƙon nasa, Tinubu ya ce alamomi na nuna tattalin arziƙin ƙasar na farfaɗowa, duk da dai farashin abinci da magunguna sun ci gaba da zama abin damuwa ga ƴan ƙasar, inda ya yi alƙawarin a shekarar 2025, gwamnatinsa za ta bunƙasa samar da abinci da kuma inganta samar da magunguna a cikin gida domin kawo sauƙi ga farashin su.
Ya kuma kuma ce sun duƙufa wajen rage hauhawar farashin kaya daga kashi 34.6 bisa 100 da yake a yanzu zuwa kashi 15.
Fintiri ya naɗa sarakunan sabbin masarautun da ya ƙirkira
A ranar juma'a ne kuma, gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri ya amince da naɗin sarakunan sabbin masarautu bakwai da aka ƙirƙira a jihar.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Humwashi Wonisikou ya fitar ranar Juma'a, ya ce naɗin sabbin sarakunan ya fara aiki ne nan take.
Matakin na zuwa ne bayan da gwamnan ya amince da dokar kafa sabbin masarutun bakwai da majalisar dokokin jihar da gudanar.
Gwamna Fintiri ya ce an zaɓo sarakunan ne bisa cancanta da ficen da suke da shi a tsakanin al'umominsu.
Jawabin Tinubu soki-burutsu ne - PDP
Kwana guda bayan jawabin na shugaban Najeriya, babbar jam'iyyar hamayyar ƙasar, PDP ta ce jawabin na Tinubu kalaman fatar baki ne kawai.
Tun da farko Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ɓullo da wasu tsare-tsare domin rage tsadar farashin abinci da samar da tsaro da kuma wasu nasarori da ya ce gwamnatinsa ta samu.
A dangane da kalaman shugaban, jam'iyyar PDP ta bakin tsohon sakatarenta na kasa Sanata Umaru Tsauri, ta mayar da martani da cewa kalaman soki-burutsu ne kawai.
Gwamnatin Tinubu ta karɓi bashin Bankin Duniya bayan cika sharaɗin cire tallafin mai
A cikin makon da ya gabatan ne gidan talbijin na Channels a ƙasar ya ruwaito cewa Bankin Duniya ya danƙa wa Najeriya bashin dala biliyan ɗaya da rabi bayan gwamnatin Bola Tinubu ta aiwatar da wasu daga cikin tsare-tsaren tattalin arziki.
Matakin na zuwa ne bayan bankin ya amince da bai wa Najeriyar bashi kashi biyu na jimillar dala biliyan 1.5 kan gyaran tattalin arziki (Reforms for Economic Stabilization to Enable Transformation) da kuma dala miliyan 750 domin ayyukan cigaba (Development Policy Financing Program).
Daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin ta aiwatar akwai cire tallafin man fetur, da kuma bijiro da sabuwar dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokoki.
'Ƴansandan Abuja 140 ne suka mutu a 2024'
A cikin makon ne kuma kwamashinan 'yansanda na birnin Abuja ya ce aƙalla dakarunsa 140 ne suka mutu a bakin aiki cikin shekarar 2024 saboda tashin hankali daban-daban.
Olatunji Rilwan Disu ya ce daga cikin dalilan da suka jawo mutuwar tasu har da arangamar da suka dinga yi da 'yan ƙungiyar IMN ta 'yan Shi'a a babban birnin.
Da yake magana cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, kwamashinan ya ce akwai kuma 'yansandan da suka kwanta barci amma ba su tashi ba.