Jaruman Kannywood da suka daɗe suna jan zarensu

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Masana'antar Kannywood ta daɗe tana ƙyanƙyashe jarumai maza da mata, wasu sun tafi, wasu sun maye gurbinsu, kuma har yanzu ana cigaba da samun sababbin jarumai da suke jan zarensu a masana'antar.

Sai dai a zamanunnuka da suka shuɗe, an yi waɗanda suke shigowa masana'antar su yi finafinai kaɗan, sai su yi ɓatar dabo, a daina jin ɗuriyarsu baki ɗaya.

Wasu sukan shigo da ƙafar dama, sai su ɓace ɓat, sannan daga baya su yi kome a sababbin finafinai.

Amma akwai wasu waɗanda suka daɗe suna jan zarensu a masana'antar, inda suke yi shekaru suna fitowa a finafinai.

Ga wasu jarumai waɗanda BBC ta rairayo da suka daɗe suna tashe.

Ali Nuhu

Ali Nuhu, wanda yanzu shi ne shugaban hukumar fim ta Najeriya, ya yi sama da shekara 20 yana taka rawa a finafinan Hausa.

Yanzu ana masa laƙabi da sarki a masana'antar, wasu kuma suna kiransa da yaya Ali da sauran sunaye daban-daban.

Fim ɗinsa na farko shi ne Abin sirri ne a shekarar 1999.

Yakubu Mohammed

Yakubu Mohammed shi ma fitaccen ɗan fim ne da ya daɗe yana jan zare a masana'antar.

Sai dai da farko ya shigo masana'antar ne a tsakankanin shekarar 1998 zuwa 1999 a matsayin marubuci da mawaƙi, kafin daga bisani ya koma fitowa a fim.

Adamsy yalo da Ayre jarumai na gasa da sauransu.

Hajara Usman

Hajara Usman, wadda aka fi sani da Mama Hajjo. A wata tattaunawarta da BBC a shekarar 2021ta ce tana da aƙalla shekara 36 a harkar fim a lokacin. Fim ɗinta na farko sunansa Farin Wata da bakar gizo waɗanda aka haska a talabijin.

Yanzu haka tana cikin fim ɗin Manyan Mata da wasu sababbin finafinai.

Rabiu Rikadawa

Ya daɗe yana taka rawa a finafinan talabijin, irin su Bagiringirin da Sahun Keke da sauransu.

A baya ya yi fice da sunan dila, amma yanzu ya fi yin fice a matsayin Baba dan audu.

Yanzu kuma cikin jaruman da suka taka rawa a finafinan Labarina da Gidan Sarauta da sauran sababbin finafinai

Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sadiq jarumi ne da shi ma ya daɗe yana jan zarensa a masana'antar, inda ya fara tashe a ƙarƙashin su Ali Nuhu da Sani Danja, amma har yanzu yake jan zarensa a matsayin matashi a finafinai.

Jamila Nagudu

Jamila Umar, wadda aka fi sani da Jamila Nagudu ita ma jaruma ce da ta fara shiga fim a ƴan tsakankanin shekarar 2002, kuma har yanzu tana ci gaba da taka rawa a masana'antar.

Daga cikin finafinanta na baya akwai Hindu da Jamila da Jamilu da Ƙauyawa da sauransu, sannan yanzu haka tana cikin fim ɗin Manyam Mata da sauransu.

Lawal Ahmed

Lawan Ahmad shi ma jarumi da shigo masana'antar tun a zamanin da su Ali Nuhu suke zan zarensu, amma ya yi ƙarko zuwa yanzu, duk da cewa ya fara ja baya, kafin shirin Izzar so ya dawo da shi kan ƙadami.

Ya fito a finafinan baya irin su Taraliya da Sansani da Sai wata rana da sauransu.

Tijjani Faraga

Shi ma Tijjani Faraga jarumi ne da ya daɗe a masana'antar fim, kasanecwar shi ma ya fara harkar ce tun daga finafinan daɓe a Jos.

Akwai jarumai irin su Bashir Nayaya da Tahir Fagge da Musa Muhammad wanda aka fi sani da Auta Baita da Shuaibu Lilisco da sauransu, waɗanda suma an daɗe ana ganin fuskokinsu, kuma har yanzu ana ganinsu, duk da wasu jefi-jefi ake ganinsu.