Arsenal na amfani da Viktor Gyökeres a gaba kamar wani injin—yana matuƙar wahala da ƴan bayan Burnley..
Ƙarfin jikinsa da yadda yake riƙe ƙwallo ya sa Burnley ta kasa kwacewa da sauƙi, kuma hakan ya haifar wa Arsenal da jefa ƙwallo daga gefen fili.
, Arsenal 1-0 Burnley
Mai tsaron ragaR Burnley, Max Weiß ya yi jinkiri wajen fita da ƙwallo, sannan Viktor Gyökeres ya matsa masa da matsin lamba sosai.
Gyökeres ya faɗi yayin da Weiß ya buga ƙwallon, amma alkalin wasa ya nuna cewa ba laifi ba ne.
, Arsenal 1-0 Burnley
Asalin hoton, Getty Images
, Arsenal 1-0 Burnley
Burnley na kokarin ci gaba da tazagawa a wasan, yayin da Loum Tchaouna ya fadi yana bukatar kulawar likitoci, sakamakon wani turewa ba tare da ƙwallo ba daga Piero Hincapié.
Duk da haka, al’amarin bai yi kamar rauni mai tsanani ba, shi ya sa ake ganin ba a bayyana dalilin da ya sa aka kira likitoci nan take ba.
, Arsenal da Burnley
Arsenal ta yi nasara a dukkan wasa 10 a Premier League
da ta buga da ƙungiyoyin da tuni suka fice daga gasar a wannan kakar — mafi
kyakkyawan tarihin nasara da kaso 100% a gasar.
Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a gida cikin wasan 44 a
Premier League da ƙungiyoyin da suka hau daga Championship (ta yi nasara 39 da canjaras biyar) tun bayan shan kashi 1-0 a hannun Newcastle United a Nuwambar
2010. Ta lashe wasa 15 na bayan nan da jimillar ƙwallaye 43-9.
Arsenal ma ta yi canji, Arsenal 1-0 Burnley
Wannan lokacin canji ne daga Arsenal, yayin da Kai Havertz da Eberechi Eze da kuma Riccardo Calafiori suka fita waje aka sauya su da Myles Lewis-Skelly da Viktor Gyokeres da kuma Piero Hincapie.
Canji daga Burnley, Arsenal 1-0 Burnley
Hannibal Mejbri da Lesley Ugochukwu sun fita daga fili, an mye gurbinsu da Zeki Amdouni da kuma Josh Laurent.
, Arsenal 1-0 Burnley
Sauran mintuna 30 a kare wasan a arewacin London.
Idan har bambancin ƙwallaye (goal difference) zai zama abin da zai ƙayyade komai tsakani da Manchester City, to Arsenal za ta bukaci ta ƙara cin ƙwallaye a daren nan.
, Arsenal da Burnley
Arsenal ta yi rashin nasara a wasan gida na ƙarshe a rufe gasar Premier League a kaka ɗaya kacal cikin shekara 28 da suka gabata (nasara 23 da canjaras huɗu), kuma
ba ta yi rashin nasara ba a irin wannan wasa cikin shekara 14 tun bayan shan
kashi 2-1 a hannun Aston Villa a kakar 2010-11.
Asalin hoton, Getty Images
Man City na shirin rabuwa da Guardila a karshen kakar nan, Arsenal 1-0 Burnley
Manchester City na shirye-shiryen rabuwa da Pep Guardiola a Etihad, bayan wasan Premier League a ranar Lahadi a karawa da Aston Villa.
Majiyoyi sun shaida wa BBC cewa ana sa ran fitaccen kocin zai bar Etihad Stadium a ƙarshen kakar bana.
City dai tana nan kan matsayinta cewa Guardiola yana da kwantiragi har zuwa kakar wasa mai zuwa, kuma tana fatan zai ci gaba da zama a kungiyar.
Sai dai ana ci gaba da shirye-shiryen ficewarsa a karshen kakar bana, inda wasu ma’aikata ke ganin zai bar aikin.
Haka kuma an fahimtar cewa wasu daga cikin ƴan wasan suna tsammanin zai yi bankwana bayan wasan ƙarshe a kakar bana da Villa.
Tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca, wanda ya taba aiki ƙarƙashin Guardiola a City, shi ne kan gaba wajen maye gurbin mai shekara 55.
Asalin hoton, Getty Images
, Arsenal 1-0 Burnley
Burnley tana samun ɗan lokaci mai kyau yanzu, yayin da Hannibal Mejbri ya kutsa gaba da gudu sannan ya yi buga kwallon da ƙarfi, amma ƙwallon ta wuce saman raga.
, Arsenal 1-0 Burnley
Leandro Trossard ya yi ƙoƙari sosai wajen aika ƙwallo daidai kan Eberechi Eze.
Eze ya yi ƙoƙarin kai ta kusurwar raga da kai, amma bai iya sarrafa ta yadda ya kamata ba.
, Arsenal 1-0 Burnley
Cristhian Mosquera ya ɗaga ƙwallo mai kyau zuwa ga Eberechi Eze a cikin gidan Burnley.
Eze ya yi ƙoƙarin ya buga kai tsaye da volley, ƙwallon ta buga ƙasa sannan ta gogi saman trken raga.
, Arsenal 1-0 Burnley
Eberechi Eze ya rasa ƙwallon cikin sakaci a tsakiyar fili, sannan Jaidon Anthony ya yi anfani da damar ya kwace ta.
Ya kutsa daga gefen hagu zuwa ciki sannan ya yi ƙoƙarin bugawa daga nesa, amma ƙwallon ta wuce saman raga.
, Arsenal 1-0 Burnley
Matuƙar wasan yana nan 1-0, za a ci gaba da samun ɗan fargaba tsakanin magoya bayan Arsenal F.C..
Amma idan suka mai da shi 2-0, hankalin kowa zai koma gaba ɗaya kan bambancin ƙwallaye.
, Arsenal 1-0 Burnley
Wannan wata sabuwar dabarar fara wasa ce daga Arsenal.
Declan Rice ya ɗaga ƙwallon sama kaɗan, sannan ya bugi ta da ƙarfi sosai zuwa gaba.
Da alama dabarar tana ƙoƙarin jefa ruɗani da rashin tabbas cikin masu tsaron bayan Burnley.
An koma zagaye na biyu, Arsenal 1-0 Burnley
An je hutun rabin lokaci
, Arsenal 1-0 Burnley
Burnley ba ta iya matsowa kusa da Bukayo Saka.
Ya karɓi ƙwallon da ƙafarsa ta hagu, ya buɗe jikinsa sannan ya nemi kusurwar nesa daga bakin akwatin fanareti, amma ƙwallon ta wuce ta gefen tirken raga.
Asalin hoton, PA Media
, Arsenal 1-0 Burnley
Yana da wuya Burnley take wasan kai hari mai ma’ana. ‘Yan wasan sun ja baya sosai suna ƙoƙarin dakile hare-haren Arsenal F.C.