Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya - Lahadi, 26-01-2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye -Lahadi, 26-01-2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Annur Muhammad

  1. Gwamnatin Sokoto za ta fara biyan albashi mafi ƙanƙanta na naira 70,000

    Ahmad Aliyu

    Asalin hoton, Sokoto State Government

    Bayanan hoto, Gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu

    Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da fara biyan mafi ƙanƙantar albashi na naira 70,000 ga ma'aikatar jihar.

    Cikin wani saƙo da gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce za a fara biyan sabon albashin ne daga gobe Litinin a faɗin jihar.

    Gwamnan ya ce sabon ƙarin albashin ya haɗa da ma'aikatan gwamnatin jiha da na ƙananan hukumomi.

    Haka kuma gwamnan ya yi kira ga ma'aikatan jihar su rama wa gwamnati ta hanyar cika mudun aikinsu

    Ahmad Aliyu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kyautata wa ma'aikatan jihar, ta hanyar biyansu albashi a kan lokaci kowane wata.

    Ya kuma alƙawarta ware naira miliyan 500 domin biyan bashin garatutin tsoffin ma'aikata a faɗin jihar.

  2. Shugaban Sudan ya ziyarci shalkwatar sojin ƙasar karon farko cikin shekara biyu

    Shugban mulkin sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al Burhan ya ziyarci shalkwatar sojojin ƙasar da ke Khartoum karon farko a cikin aƙalla shekara biyu.

    Ƙwace iko da shalkwatar sojin a babban birnin ƙasar, babbar nasara ce ga sojojin ƙasar.

    Janar Burhan ya yaba kan abin da ya kira jajircewa da sadaukarwar sojojin da suka kare shalkwatar.

    Ya kuma sha alwashin fatattakar dakarun RSF, wadanda ke iko da mafi yawan birnin Khartoum.

    To sai dai har yanzu El Fasher, babban birnin Arewacin Sudan, na ƙarƙashin ikon dakarun RSF, inda Majalisar Dinkin duniya ta ce an kashe mutum 70 a harin da aka kai wani asibiti ranar Juma'a a birnin.

    Harin ya kuma lalata ilahirin sashen bayar da kulawar gaggawa na asibitin.

    Jami'an lafiya a asibitin sun ce harin ya kashe gomman marasa lafiya da masu jinyar 'yan'uwansu.

    Bidiyon da aka yaɗa ya nuna gawarwaki da dama kwance cikin jini a ƙasa yayain da ɓaragunan gini ya danne su.

  3. Sojojin Najeriya sun tabbatar da kashe dakarunsu 22 a harin ƙunar bakin wake a Borno

    SOJOJIN NAJERIYA

    Asalin hoton, @NigerianArmy

    Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kisan dakarunta 22 tare da raunata wasu da dama a wani harin ƙunar baƙin wake da mayaƙan Boko Haram suka suka kai musu a jihar Borno.

    Cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaran shalkwatar tsaron ƙasar, Manyo Janar Edward Buba ya fitar ranar Lahadi ya ce lamarin ya faru ne a ƙarshen mako lokacin da sojojin suka ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin mayaƙan ƙungiyar da ke yankin Timbiktu da ya haɗa jihohin Borno da Yobe.

    Tun da farko dai rahotonni sun ce sojoji 27 mayaƙan na Boko Haram suka kashe a lokacin gumurzun.

    Ya ƙara da cewa sojojin rundunar Operetion Haɗin Kai', sun samu nasarar kakkaɓe 'yantawayen masu yawan gaske a maɓoyarsu a wani hari da suka ƙaddamar musu - tun daga ranar 16 zuwa 25 ga watan Janairu - da nufin murƙushe su.

    Manjo Janar Buba ya ce a lokacin harin kakkaɓe sansanonin mayaƙan, sojojin sun samu nasarar kashe mayaƙan ƙungiyar 70, cikin har da wasu manyan fitattun kwamandojin ƙungiyar uku.

    ''A lokacin kai harin, mayaƙan Boko haram ɗin sun girke abubuwan fashewa da ababen hawa da suka cika da abubuwan fashewa da 'yan ƙunar baƙin wake domin dakatar da farmakin sojojin'', in ji sanawar.

    To sai dai ya ce kasancewar dakarun sojin sun saba da wannan dabara ta mayakan ƙungiyar, sun samu nasarar kauce wa yunƙurin na Boko Haram, ciki har da harbi da jirage marasa matuƙa.

  4. MDD ta buƙaci Rwanda ta dakatar da goyon bayanta ga M23 a DR Kongo

    Antonio Guterres

    Asalin hoton, Reuters

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya buƙaci Rwanda ta janye dakarunta daga DR Kongo tare da dakatar da goyon bayanta ga 'yantawayen M23 da ke ƙaddamar da hare-hare domin ƙwace birnin Goma da ke gabashin DR Kongo.

    Cikin wata sanarwa da kakakinsa ya fitar a yau Lahadi. Mista Guterres ya bayyana matuƙar damuwa kan ƙaruwar rikici a gabashin DR Kongo.

    Ya kuma yi Allah wadai kan ƙungiyar M23 kan hare-haren baya-bayan nan da mayaƙanta ke kaddamarwa a birnin Goma da ke Arewacin Kivu ta hanyar goyon bayan da suke samu daga dakarun Rwanda, kamar yadda kakakin Guterres, Stephane Dujarric ya bayyana.

    Babban sakataren ya yi kira ga ƙungiyar ta M23 ta dakatar da hare-harenta tare da janyewa daga wuraren da mayaƙanta suka ƙwace, tare da kiran ta mutunta yarjejeniyar zaman lafiya.

    Haka kuma Mista Gutteres ya yi kiran gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa sojojin Majalisar Dinkin Duniya a yankin, yana mai gargaɗin cewa hari kan dakarun MDD ka iya zama laifin yaƙi.

  5. Harin Boko Haram ya kashe sojojin Najeriya da dama a Borno

    Soja da bindiga na wuce mota da aka kona

    Asalin hoton, OTHERS

    Rahotanni daga Najeriya na nuna cewa sojojin ƙasar da dama ciki har da kwamandansu sun rasu a wani hari da mayaƙan Boko Haram suka kai musu a sansaninsu da ke garin Malam-Fatori na karamar hukumar Abadam ta jihjar Borno.

    Wasu bayanai na nuna cewa sojojin da suka mutu sun kai 27 haɗi da kwamandan nasu.

    Wasu kafofi sun ruwaito cewa majiya mai ƙarfi ta sheda musu cewa maharan sun yi wa sansanin dirar mikiya ne inda suka yi ta bata-kashi da dakarun Najeriyar tsawon sa'o'i da dama a ranar Juma'a 24 ga watan nan na Janairun 2025, inda suka yi nasarar cin ƙarfin sansanin.

    Sojojin da suka tsira daga harin sun tsere daga sansanin, in ji rahotanni.

    Bayanai sun tabbatar da cewa mayaƙan masu iƙirarin jihadi sun je sansanin ne da motoci masu bindigogi a kansu.

    ''An ji wa sojoji da dama mummunan rauni, yayin da wasu da yawa kuma ba a san inda suke ba,'' kamar yadda tashar talabijin ta ce wata majiya ta sheda mata.

    Kwamandan rundunar, Laftana Kanar Alari da wasu manyan sojoji biyu da suka haɗa da babban darektan kula da lafiya na sansanin na daga cikin waɗanda aka kashe.

    Sansanin na Malam-Fatori na wajen da ke da tazarar kilomita biyu ne kacal daga garin Bosso na Nijar da kan iyaka a yankin tafkin Chadi.

    Sai dai kuma wata majiyar soji ta sheda wa tashar talabijin ɗin cewa an kai harin ne a sansanin lokacin da dakarun ke sintiri inda mayaƙan suka yi musu kwanton-ɓauna, da ya kai ga kisan kwamandan.

    Har yanzu hukumomin sojin Najeriya ba su ce komai ba game da harin.

  6. Kwamitin tsaro na MDD zai yi taron gaggawa kan rikicin Kongo

    Mayaƙan tawaye na ƙungiyar M23

    Asalin hoton, OTHERS

    Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taron gaggawa a yau Lahadi a kan mummunan fadan da ake yi a gabashin Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo.

    Hulɗar diflomasiyya tsakanin Kinshasa da gwamnatin maƙwabciyarta Rwanda ta katse, sakamakon Kongon na zargin maƙwabciyar tata da ɗaukar nauyin 'yantawayen M23, waɗanda ke kan hanyar kama birnin Goma mai muhimmanci.

    Rwanda na musanta zargin mara baya da 'yantawayen duk da zargin na Kongo da ƙasashen Yamma da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

    Sojoji 13 na rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a gabashin Kongon a faɗa da mayaƙan na M23.

    A cikin shekara uku ƙungiyar ta M23 ta ƙwace yankuna da dama a gabashin ƙasar.

    To amma a cikin makonnin da suka gabata mayaƙan sun durfafi babban birnin lardin na Goma yayin da faɗa ke ricaɓewa.

  7. Tinubu ya tafi Tanzania taron Afirka kan makamashi

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, Presisency

    Shugaba Bola Tinubu zai tafi Tanzania a yau Lahadi domin halartar taron ƙoli na Afirka kan makamashi a babban birnin ƙasar, Dar es Salaam, wanda za a fara gobe Litinin zuwa jibi Talata.

    Taron wanda gwamnatin ƙasar ta Tanzania za ta karɓi baƙuncinsa da haɗin gwiwar Bankin Raya Afirka da kuma Bankin Duniya, zai kasance ne da nufin tabbatar da shirin samar da wutar lantarki ga mutum miliyan 300 a Afirka nan da shekara ta 2030 - shirin da ake yi wa laƙabi da ‘‘Mission 300.’’

    A yayin taron shugabannin Afirka, da shugabannin harkokin kasuwanci a nahiyar da kungiyoyin farar hula za su yi ƙoƙarin samo dabarun ciyar da shirin gaba cikin hanzari.

    Haka kuma taron zai yi musayar dabaru kan yadda za a shawo kan matsalar makamashi a nahiyar.

    Mahalatta taron za su tattauna kan yadda za a samar da makamashi kan yankunan da suke da matsala cikin sauri da samar da makamashi maras gurɓata muhalli da ƙoƙarin shigar da 'yankasuwa cikin harkar samar da makamashin.

    A ranar farko ta taron ministocin makamashi na ƙasashen da ke halartar taron za su tattauna, yayin da a rana ta biyu shugabannin ƙasashen su kuma za su rattaɓa hannu kan daftarin shirin samar da makamashin na Afirka.

  8. Fashewar tankar mai ta kashe mutum 18 a Enugu

    Tankar mai

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 18, yayin da wasu 10 suka samu munanan raunukan ƙuna bayan fashewar tankar man fetur a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin ƙasar.

    Hukumar kiyaye aukuwar hatsura ta ƙasar, ta ce motar ta ƙwace wa direbanta bayan lalacewar birki, lamarin da ya sa ta bi ta kan wasu ƙananan ababen hawa a kan wani babban titi, kafin ta fashe.

    Fashewar tankar - wadda ta faru a ranar Asabar - ta ƙona mutane da dama ta yadda har ba aiya gena wasu.

    Hatsarin ya kasance na baya-bayan nan cikin hatsuran fashewar motocin tankokin man futer da suka yi sanadin rayuwa da dama a cikin ƙasar.

    Ko a makon da ya gabata ma wani hatsarin tankar man fetur a jihar Neja ya kashe kusan mutum 98.

  9. Trump ya nemi Falasɗinawan Gaza su koma Masar da Jordan

    Donald Trump

    Asalin hoton, AP

    Bayanan hoto, Ya ce ya kamata a mayar da Gaza fili - a haƙura kowa ya zauna lafiya

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana son ganin an share Gaza gaba ɗaya, inda ya buƙaci ƙasashen Masar da Jordan su karɓi ƙarin Falasɗinawan zirin na Gaza su koma can.

    Da yake magana da 'yanjarida a cikin jirginsa na shugaban ƙasa (Air Force One), a jiya Asabar, Trump ya ce tun da farko ya tattauna ta waya da Sarki Abdullah II na Jordan kuma nan gaba zai so ya yi magana da Shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi a yau Lahadi.

    Trump wanda ya yaba wa Jordan saboda karɓar 'yangudun hijirar Falasɗinawa, ya ce ya gaya wa Sarkin da ya ƙara karɓar wasu, sannan ita ma Masar yana son ta karɓi ƙari - a share komai a Gaza - ''shikenan kowa ya haƙura a samu zaman lafiya.'' In ji Trump ɗin.

    Hare-haren Isra'ila sun raba Falasɗinawa kusan miliyan biyu da dubu 300 da Gaza, wasu daga cikin a lokuta da dama.

    Trump ya ce a yadda Gaza take, ''a yanzu tamkar kufai ce kusan an rushe komai kuma mutane na mutuwa a canc.''

    ''Saboda haka gara na yi magana da wasu ƙasashen Larabawa a gina gidaje a wani wajen daban, inda za su iya zama a samu kwanciyar hankali.'' In ji shi.

    Sai dai ƙungiyar Falasɗinawa ta Islamic Jihad (PIJ), ta yi Allah-wadarai da shawarar shugaban tna mai bayyana ta a matsayin ƙara goyon baya da kuma ƙarfafa gwiwa ga aikata laifukan yaƙi.

    Ƙungiyar ta bayyana shawarar da cewa daidai take da manufar Isra'ila ta hana Falasɗinawa 'yancin wanzuwa cikin 'yanci da walwala, inda ta yi kira ga Masar da Jordan su yi watsi da shirin.

  10. Afirka ta Kudu ta yi dokar ƙwace fili ba tare da diyya ba

    Cyril Ramaphosa
    Bayanan hoto, Fararen fata marassa rinjaye sun mallaki gonaki fiye da baƙaƙen fata a ƙasar

    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanya hannu a dokar da ta bai wa gwamnati ikon ƙwace fili ko gona ba tare da biyan diyya ba.

    Lamarin ya haddasa saɓani a tsakaninsa da wasu mambobin gwamnatinsa, inda suka ce za su ƙalubalanci abin a kotu.

    Baƙaƙen fata waɗanda su ne suka fi yawa a ƙasar sun mallaki filaye da gonaki ne kaɗan saɓanin fararen fata da ba su da yawa kuma suka mallaki filaye masu yawan gaske.

    Kasancewar sama da shekara 30 kenan da kawo ƙarshen mulkin wariyar launin fata, ana nuna damuwa da ɓacin rai kan tafiyar hawainiya wajen aiwatar da sauye-sauye a ƙasar.

    Yayin da jam'iyyar Ramaphosa, ANC, ta yaba da sabuwar dokar wasu mambobin gwamnatinsa ta haɗaka na ja da dokar inda suka ce za su ƙalubalance ta a kotu.

    Gwamnati ta ce dokar ta tanadi karɓe fili ne kawai domin amfanin al'umma kawai.

  11. Amurka ta jaddada zarginta kan asalin annobar Korona

    Mutum sanye da kayan kariya na asibiti

    Asalin hoton, OTHERS

    Hukumar leƙen asiri ta Amurka, CIA, ta gabatar da sabon bayani kan binciken da ta yi game da abin da ake ganin ya haddasa annobar Korona (Covid19) a duniya, inda ta ce tana ganin zai fi yuwuwa ƙwayar cutar ta fita ne daga ɗakin bincike na kimiyya saɓanin daga jikin dabbobi.

    Kakakin hukumar ya ce bisa ga dukkan alamu ɓullar cutar na da alaƙa da aikin bincike -maimakon a ce haka kawai ta ɓulla, kamar yadda rahoto ya nuna.

    To amma kuma hukumar ta CIA ta ce ba ta da cikakken ƙwarin gwiwa a kan hakan.

    Shawarar fitar da wannan sakamako ta kasance ɗaya daga cikin matakan da sabon shugaban hukumar ta CIA, John Ratcliffe, wanda Donald Trump ya naɗa ranar Alhamis, ya yi.

    Daman tun a lokacin Trump na farko Ratcliffe, wanda a lokacin darekta ne a hukumar samar da tsaro ga shugaban ƙasa, yana da ra'ayin cewa cutar ta ɓulla ne daga ɗakin kimiyya na cibiyar binciken kimiyya ta Wuhan da ke China.

    Cibiyar tana da tazarar tafiyar minti 40 ne a mota daga kasuwar da ake sayar da kifi da sauran naman ruwa - inda ake cewa daga kasuwar ne cutar ta ɓulla.

    China dai a kullum tana watsi da zargin cewa ƙwayar cutar ta fita ne daga ɗakin kimiyya, inda take danganta hakan da haramben siyasa na Amurka.

  12. 'Yantawayen Kongo sun kashe sojin MDD 13

    Sojojin zaman lafiya na MDD

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Ko a ranar Alhamis 'yantawayen sun kashe gwamna

    An kashe sojojin wanzar da zaman lafiya 13 a Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo a rikici da ƙungiyar 'yantawayen M23 na ƙasar.

    Rundunar sojin Afirka ta Kudu ta ce dakarunta tara sun mutu a lokacin da suke taimakawa wajen dakatarwa tare da kokarin tura 'yantawayen baya don hana su kama birnin Goma, a gabashin ƙasar ta Kongo, yayin da sojin Mali uku da ɗaya na Uruguay shi ma ya rasu.

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ya yi magana da shugabannin Jamhuriyar Kongon da kuma na Rwanda a ci gaba da kiraye-kirayen da duniya ke yi a kawo karshen yaƙin.

    Yayin da faɗan ke ƙara tsananta Majalisar Ɗinkin Duniya na janye dukkan jami'anta waɗanda aikin bai zama dole ba, daga birnin Goma - wanda mutum sama da miliyan ɗaya ke zaune a cikinsa.

    An matso da wani taron gaggawa da kwamitin tsaro na Majalisar zai yi kan rikicin na Kongo daga Litinin zuwa Lahadi

    Ƙungiyar 'yantawayen ta M23 ta buƙaci dakarun ƙasar ta Kongo su ajiye makamansu su miƙa wuya domin kauce wa zubar da jinin.

    Kongo na zargin maƙwabciyarta Rwanda, wadda dangantaka tsakaninsu ta yi tsami da ɗaukar nauyin 'yantawayen.

    A ranar Alhamis 'yantawayen suka kashe wani gwamnan soji a Kongon.

  13. Buɗewa

    Jama'a masu bibiyarmu a wannan shafin da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, muna muku maraba a wannan safiya ta Lahadi 26 ga watan Janairun 2025.

    Ni ne Muhammad Annur Muhammad da Abdullahi Bello Diginza za mu kasance da ku daga yanzu zuwa wani lokaci a nan gaba.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu da sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo, har ma ku yi muhawara a kan wasu abubuwan da kuka gani a shafin.

    A yi jimirin kasancewa da mu.

    Mu fara da wannan karin maganar - Sai bango ya tsage ƙadangare kan samu wajen fakewa