Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/02/2025

Wannan shafi en da kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 08/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad

  1. Hamas ta gabatar da Isra'ilawan da za ta saki a kan dandamali

    Isra'ilawan da aka saki

    Mayaƙan Hamas sun gabatar da Isra'ilawa uku da za ta saki yau a kan dandamali a gaban ɗaruruwan Falasdinawa a unguwar Darel-a-Balah da ke tsakiyar birnin Gaza.

    Isra'ilawan sanye da tufafi mai launin makuba sun samu rakiyar mayaƙan hamas bibbiyu kowansu

    Mayaƙan na Hamas sun gabatar wa Isra'ilawan takardun shaida, sannan suka yi hira da su a gaban ɗimbin Faasɗinawan da suka hallara a wurin, kafin miƙa su ga jamai'ar Red Cross.

    Isra'ilawan da aka saki
  2. Ma'aikatan lantarki na Kaduna sun dakatar da yajin aiki

    Uba Sani

    Asalin hoton, Kaduna State govt

    Hadakar ƙungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta jihar Kaduna sun jingine yajin aikin da suka ɗauki kwanaki suna gudanarwa a jihar.

    Yajin aikin ya janyo ɗaukewar wutar lantarki a jihohin Kaduna da Zamfara da Sokoto da kuma Kebbi.

    Matakin na zuwa ne bayan gwamnan jihar, Sanata Uba Sani ya sanya baki tare da zama da duka ɓangarorin biyu.

    Yayin jagorantar zaman Gwamna Uba Sani ya nuna matuƙar damuwa halin da al'umma da masu sana'o'i suka shiga sakamakon yajin aikin.

    Sannan ya yi kira ga duka bangarorin biyu su sake nazarin matakan da suka ɗauka.

    Daga ƙarshen ganawar ma'aikatan sun amince su maido da wutar lantarki da suka katse tsawn kwanaki a Kaduna da sauran jihohin da ke samun wutar daga kamfanin.

    Haka kuma ɓangarorin biyu, sun cimma matsayar zama tare domin tattauna yadda za a rage ma'aikatan kamfanin.

    Ƙungiyar ma'aikatan dai ta shiga yajin aikin ne bayan da ta zargi kamfanin rarraba lantarki na Kaduna Electric da korar wasu ma'aikata kusan 900 da ta ce an yi ba bisa ƙa'ida ba.

    Kamfanin dai ya ce ma'aikatan da ya kora 450 ne ba kamar yadda ƙungiyar ke iƙirari ba, kuma ya kare matakin da cewa ya yi hakan ne sakamakon rashin kuɗin da yake fama da shi.

    Yajin aikin dai ya janyo wa masu sana'o'i da dama mummunar asara a harkokinsu.

  3. Hamas ta kafa dandalin da za ta miƙa Isra'ilawan

    Hamas

    Asalin hoton, Reuters

    Hamas ta kafa dandalin da za ta miƙa Isra'ilawan nan uku da za ta saki yau a Deir al-Balah da ke tsakiyar birnin Gaza

    Yanzu haka ana dakon motcin ƙungiyar agaji ta Red Cross mai shiga tsakani a musayar fursunonin da ake yi tsakanin hamas da Israila.

    Dandazon fararen hula ne suka taro a wurin domin shaida miƙa Isra'ilawan, yayin da mayaƙan Hamas suka taru a wurin

  4. Bayanan yadda za a saki Falasɗinawan da za a yi musayar Isra'ilawa da su

    Gidan yari

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Daya daga cikin gidajen yarin Isra'ila

    Yayin da ake dakon Hamas ta fara sakin Isra'ilawa uku domin Isra'ila ta sako Falasɗinawa 183 da ke tsare a gidajen yarinta, ga wasu bayanai dangane fursunonin Falasɗinawa da za a saki yau.

    Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ta tabbatar da karɓar sunayen fursunonin da ake sa ran saki a yau, to amma ba ta bayyana su ba kawo yanzu.

    A cewar hukumar za a ɗauki fursunonin daga gidajen yarin Ofer da Ktziot, sannan su jira a wuraren saukar baƙi na gidajen yarin har zuwa lokacin da Hamas za ta sako Isra'ilawa ukun da ta yi alƙawari.

    Daga nan sai a ɗauke su a manyan motacin bas zuwa wurin da za a miƙa su a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, yayin da za a wuce da wasu zuwa mashigar Kerem Shalom da ke kan iyakar Gaza.

    Daga cikin yarjejeniyar musayar fursunonin da aka cimma, Isra'ila ta amince da sakin Falasɗinawa 1,900 ciki har da waɗanda ke tsare ba tare da tuhuma ba.

  5. Amurka ta dakatar da agajin da take bai wa Afirka ta Kudu

    Shugaban Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta dakatar da agajin da ta ke bai wa Afirka ta Kudu, daidai lokacin da zaman tankiya ke ƙaruwa kan dokar filaye.

    Shugaba Trump na Amurkan ne ya bayar da umarnin, saboda zargin sabuwar dokar, ta bai wa gwamnati damar karɓe gonakin Turawa farar fata ba tare da biyan diyya ba.

    Sai dai gwamnatin Shugaba Cyril RamaPhosa ta ce Afrika ta Kudu ba za ta amince a yi mata barazana ba.

    Shi ma makusancin Mista Trump, kuma haifaffen Afirka ta Kudun, Biloniya Elon Musk, ya soki matakin na Afirka ta Kudu.

    A ƙarshe umarnin shugaban ƙasar ya soki Afirka ta Kudu kan ƙarar da ta shigar gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC kan kisan ƙare dangin da Isra'ila ke yi a Gaza.

  6. Hamas na shirin sakin Isra'ilawa uku domin musayarsu da Falasɗinawa 183

    mutane

    Asalin hoton, Family

    Nan gaba a yau ne Hamas za ta saki Isra'ilawa uku da take garkuwa da su, yayin da Isra'ila za ta yi musayarsu da Falasinawa 183.

    Wannan ce musayar ta biyar tsakanin ɓangarorin biyu tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Mutanen uku da Hamas din za ta saki a yau dukkansu fararen hula ne.

    Hamas ta bayyana sunayen mutanen da suka haɗa da Eli Sharabi da Ohad Ben Ami da Hamas ta sace a Kitburz, sai Or Levy da a ka yi garkuwa da shi a bikin kalankuwar Nova ranar 7 ga watan Oktoban 2023 lokacin da ta ƙaddamar da farmaki kan Isra'ila.

    Ranar Litinin ne ya kamata a fara zaman tattaunawar tsagaita wutar kashi na biyu, sai dai hakan ba ta samu ba.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da wanan lokaci.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki ta fuskar labarai.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.