Shugaban jbabbar jam'iyyar hamayya a Ivory Coast, Tidjane Thiam, ya soke takardarsa ta zama ɗan Faransa, gabanin babban zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Oktoban 2025.
Ɗaya daga cikin manyan sharuɗan tsayawa takara shugabancin ƙasar, shi ne kasancewa ɗan asalin Ivory Coast kaɗai ba tare da gauraye ba.
Tsohon Shugaban kamfanin Credit Suisse, na da takardun shaidar zama ɗan ƙasashe biyu - Faransa da Ivory Coast.
To amma bayan aniyarsa ta ƙalubalantar Shugaba Alassane Ouattara a zaɓen ƙasar da ke tafe, Mista Thiam ya sanar da soke takardar shaidar Faransar.
Thiam mai shekara 62, ana kallonsa a matsayin ɗan takarar da matasa ke mara wa baya a ƙasar da ke yammacin Afirka.
Ya koma kasar Ivory Coast shekara biyu da suka gabata bayan shafe fiye da shekara 20 yana ƙasar waje.
A shekarar 2020 ne aka zaɓi Shugaba Alassane Ouattara a wa'adin mulki na uku mai cike da ce-ce-ku-ce a zaɓen da 'yan adawa suka ƙauracewa, inda ya samu kashi 94 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Masana harkokin siyasa na hasashen samun kwanciyar hankali a zaɓen da ke tafe fiye da na baya, wanda aka kashe mutum 35 a rkicin da aka samu a ranar zaɓen.
Kawo yanzu dai Shugaba Ouattara bai bayyana ko zai tsaya a wa'adin mulki na huɗu ba.
An fara zaɓen Mista Ouattara a 2010 a wani zaɓe da aka tafka mummunan rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 3,000 a ƙasar, bayan da tsohon shugaban ƙasar, Laurent Gbagbo ya ƙi amincewa da shan kaye.