United na son Delap, Madrid za ta tsawaita zaman Vinicius

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na duba yiwuwar dauko dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a Ipswich Town, Liam Delap, 21, idan suka gagara daukar mai kai hari na Sweden da ke taka leda a Sporting wato Viktor Gyokeres, mai shekara 26, ko mai kai hari na Najeriya da ke taka leda a Napoli Victor Osimhen, wanda ke zaman bashi a Galatasaray. (GiveMeSport)

Manchester City na matsa kaimi domin samun tagomashi a kaka mai zuwa, sannan ta dana tarko kan dan wasan Atlanta kuma na tsakiyar Brazil mai shekara 26, Ederson. (Fichajes)

Dan wasan gaba na Brazil Vinicius Jr, mai shekara 24, na tattauna wa da Real Madrid domin tsawaita kwantiraginsa da kungiyar, duk da cewa har yanzu ba su cimma matsaya ba. (Relevo)

Borussia Dortmund ka iya sayar da matashin dan wasanta dan Ingila mai shekara 20, Jamie Gittens, wanda kungiyoyin Liverpool, Manchester United da Chelsea ke zawarcinsa, Dortmond za ta yi hakan ne idan ba su kai bantensu a Champions League a kaka mai zuwa ba. (Caught Offside)

Kungiyar Tottenham na son dan wasan tsakiya na Ingila mai taka leda a Crystal Palace Adam Wharton, 21, da dan wasan Southampton Tyler Dibling, 18. (Football Transfers)

Everton za tai kokarin dauko dan wasan gaba na Ingila mai taka leda a West Bromwich Albion, Tom Fellow mai shekara 21 a lokacin bazara. (Football Insider)

Toffees ta na da yakinin ya kamata su zage damtse da kara kaimi kan 'yan wasansu, a dukkan bangarori da sanya hakan cikin tsarin kudaden da za su kashe a nan gaba. (i Sport)

Tottenham na duba makomar Ange Postecoglou a matsayin manajan kungiyar idan suka gagara lallasa Aston Villa a kofin FA a karshen mako. (GiveMeSport)