Ma'aikatan lantarki na Kaduna sun dakatar da yajin aiki
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza da Muhammad Annur Muhammad
Sallama
Jama'a masu
bibiyarmu a wannan shafin na BBC Hausa, da ke kawo muku labaran abubuwan da ke
wakana a Najeriya da sauran sassan duniya kai tsaye, a nan za mu rufe shafin na yau Asabar 8 ga watan Fabarairun 2025.
A madadin
kowa da kowa muke fatan za ku kasance da mu gobe, Lahadi, idan Allah Ya yarda.
Amma za ku iya ci gaba da leƙawa shafukanmu da sada zumunta da muhawara domin karanta wasu labaran da kallon
hotuna da bidiyo, har ma ku yi muhawara
Mu rufe da
wannan karin maganar da ke cewa - Komai nisan dare gari zai waye
Shugabannin Afirka sun nemi a koma teburin tattaunawa kan rikicin Kongo
Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock
Shugabannin kasashen Afrika sun yi kira da a sake komawa kan teburin tattaunawa domin shawo kan rikicin da ke kara kamari a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo.
An bai wa hafsoshin tsaro daga gabashi da kudancin Afrika wa'adin kwanaki biyar da su tsara shirin tsaro a birnin Goma da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda suka mamaye.
Farmakin da 'yantawayen suka kai a lokacin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba wasu sama da dubu dari biyar da muhallansu.
Shugabannin kasashen na Afirka sun yi kiran ne a taronsu a birnin Dar-es-Salaam na Tanzania, inda kuma suka jaddada goyon bayansu ga yunkurin shiga tsakani daga sauran kasashen yankin.
Sama da mutum 30 sun bace bayan zaftarewar kasa a China
Asalin hoton, reuters
Kafar yada labarai ta gwamnatin China ta ce sama da mutum talatin sun bace bayan da zaftarewar kasa ta afku a wani kauye a kudu maso yammacin lardin Sichuan,
Jami'ai sun ce zuwa yanzu an ceto mutum biyu da rai, a zaftarewar da ta binne gidaje goma kuma mutane da dama suka makale, ba ta inda za su fita.
Hukumar agajin gaggawa ta kasar ta China ta ce tuni ta girke kayan aiki da jami'ai da suka dukufa aikin ceton.
Shugaba Xi Jinping ya bayar da umarni ga hukumomi su yi duk abin da za su iya domin ceto wadanda har hanzu ba a gani ba.
Taron shugabannin masu fifita fararen fata ya yaba wa Trump
Asalin hoton, Getty Images
Shugabannin jam'iyyu masu akidar fifita fararen fata da ra'ayin rikau na Turai sun yaba wa Shugaban Amurka Donald Trump kan irin manufofin da yake bullowa da su.
Jagororin na yaba wa Trump ne a wani taro da suka yi a babban birnin Sifaniya, Madrid.
Firaministan kasar Hungary, Viktor Orban, ya ce abin da ya kira 'Guguwar Trump' ta sauya duniya.
Shugabannin sun kuma yi kira da a bullo da tsauraran matakai kan shige da fice tare kuma da sukar dokokin muhalli na Tarayyar Turai, wadanda suka ce suna cutar da noma.
Taron wanda jam'iyyar Vox ta Sifaniya ta karbi bakuncinsa ya samu halartar jagororin kungiyar 'yan majalisar dokokin Turai masu kishin fararen fata.
'Amurka na maraba da manoma fararen fata da Afirka ta Kudu ke kwace wa gonaki'
Asalin hoton, AP
Amurka ta ce kofarta a bude take ga manoma fararen fata da ta ce gwamnatin Afirka ta Kudu ta bullo da shirin karbe gonaki da filaye domin jinsinsu na Turawa.
Ma'aikatar harkokin waje ta Amurka ce ta bayyana haka a martanin da ta yi bayan da Afirka ta Kudu ta yi zargin an yi mata karerayi da juya manufarta ta karbe filaye, domin yin raba daidai a tsakanin al'ummar kasar.
A game da shirin na Afirka ta Kudu ne Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da bai wa kasar tallafin kudi.
A martaninta Afirka ta Kudu ta ce matakin na Donald Trump, ba shi da ainahin hakikanin gaskiya sannan kuma bai yi la'akari da tarihin mulkin wariyar launin fata ba.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Afirka ta Kudu ya ce, ba a fayyace gaskiyar lamari game da shirin karbe filayen da gwamnatin kasar ta bullo da shi ba, kuma an jujjuya manufofin shirin domin bata kasar.
Gwamnatin Trump ta yi zargin cewa gwamnatin Afirka ta Kudu na kwace filaye da gonakin manoma farar fata ba tare da biya ko ba su diyya ba.
Sai dai gwamnatin Afirka ta Kudun ta ce ba wani fili da aka kwace a karkashin shirin wanda ta bullo da shi domin tabbatar da daidaito da adalci a tsakanin al'ummar kasar.
An kafa sabuwar gwamnati a Lebanon
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Alkali Nawaf Salam mai shekara 71 ya kasance shugaban kotun duniya kafin zamansa Firaministan
Bayan mako uku na tattaunawar da ake ta kiki-kaka a tsakanin jam'iyyun hamayya a karshe dai Lebanon ta samu sabuwar gwamnati.
Sabon Firaministan kasar Nawaf Salam, ya ce majalisar ministocinsa mai mambobi 24 za ta mayar da hankali ne a kan sauye-sauye na harkokin kudi da sake gina kasar da kuma aiwatar da shirin majalisar dinkin duniya na tabbatar da zaman lafiya a kan iyakarta da Isra'ila da ke kudanci.
Kafin zabensa Firaminista Salam ya kasance shugaban kotun duniya ta majalisar dinkin duniya a birnin Hague, inda aka nada shi wannan mukami a watan Fabarairu na bara.
Tabbatar da sabuwar gwamnatin abu ne da zai kai kasar ta Lebanon kusa da samun kudaden sake gina ta bayan kazamin yakin da ya lalata kasar a tsakanin Isra'ila da Hezbollah.
Kamar a kodayaushe ma'aikatun 24 an raba su ne a tsakanin bangarorin addinan kasar.
Kafin a kai ga wannan nasara ta kafa gwamnatin akwai lokutan da aka rika samun kiki-kaka a kan ministocin bangaren Shi'a - wanda Hezbollah da kawarta Amal ke bayarwa.
Netanyahu ya nuna damuwa kan halin da Hamas ta saki Isra'ilawa uku
Asalin hoton, Israel Defense Forces
Bayanan hoto, Eliyahu Sharabi ɗaya daga cikin waɗanda Hamas ta saki yau ya gana da mahaifiyarsa da kuma ƙanwarsa
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya ce ya kaɗu matuƙa dangane da mummunan halin ya ga Isra'ilawa uku da Hamas yau a Gaza.
Mutanen uku duka maza - sun yi matuƙar ramewa - a lokacin da Hamas ta gabatar da su a kan dandamali kafin miƙa su hannun Red Cross.
Kungiyar agajin ta Red Cross mai shiga tsakani ta nuna matuƙar damuwa kan yadda musayar fursunonin ke wakana, inda ta buƙa duka ɓangarorin biyu su ci gaba da mutunta yarjejeniyar.
Shugaban ƙasar Isra'ila, Isaac Herzog, ya bayyana halin da mutane ke ciki da cewa cin zarafin bil'adama.
Shugaban babbar jam'iyyar adawar Ivory Caost ya soke takardarsa ta zama ɗan Faransa
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban jbabbar jam'iyyar hamayya a Ivory Coast, Tidjane Thiam, ya soke takardarsa ta zama ɗan Faransa, gabanin babban zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Oktoban 2025.
Ɗaya daga cikin manyan sharuɗan tsayawa takara shugabancin ƙasar, shi ne kasancewa ɗan asalin Ivory Coast kaɗai ba tare da gauraye ba.
Tsohon Shugaban kamfanin Credit Suisse, na da takardun shaidar zama ɗan ƙasashe biyu - Faransa da Ivory Coast.
To amma bayan aniyarsa ta ƙalubalantar Shugaba Alassane Ouattara a zaɓen ƙasar da ke tafe, Mista Thiam ya sanar da soke takardar shaidar Faransar.
Thiam mai shekara 62, ana kallonsa a matsayin ɗan takarar da matasa ke mara wa baya a ƙasar da ke yammacin Afirka.
Ya koma kasar Ivory Coast shekara biyu da suka gabata bayan shafe fiye da shekara 20 yana ƙasar waje.
A shekarar 2020 ne aka zaɓi Shugaba Alassane Ouattara a wa'adin mulki na uku mai cike da ce-ce-ku-ce a zaɓen da 'yan adawa suka ƙauracewa, inda ya samu kashi 94 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.
Masana harkokin siyasa na hasashen samun kwanciyar hankali a zaɓen da ke tafe fiye da na baya, wanda aka kashe mutum 35 a rkicin da aka samu a ranar zaɓen.
Kawo yanzu dai Shugaba Ouattara bai bayyana ko zai tsaya a wa'adin mulki na huɗu ba.
An fara zaɓen Mista Ouattara a 2010 a wani zaɓe da aka tafka mummunan rikici da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 3,000 a ƙasar, bayan da tsohon shugaban ƙasar, Laurent Gbagbo ya ƙi amincewa da shan kaye.
Bayanai kan yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza da yadda take aiki
Asalin hoton, Bashar Taleb / AFP / Getty Images
Yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a ranar 15 ga watan Janairu ta soma aiki ne ranar 19 ga watan.
Tun daga lokacin sau huɗu aka aiwatar da musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas, yayin da aka gudanar da na biyar a yau.
An karkasa yarjejeniyar zuwa mataki uku kamar haka:
Matakin farko
Shi ne wanda ake ciki yanzu, da zai ƙare cikin kwanaki 42
Hamas ta ce za ta saki Isra'ilawa 33 da take garkuwa da su, yayin da Isra'ila za ta saki fursunoni Falasɗinawa kusan 1,900.
Za a bar Falasɗinawa su koma gidajensu, tare da bayar da damar shigar da agaji Gaza a kullum
Sojojin Isar'ila za su fice daga yankunan Falasɗinawa masu yawan jama'a.
Mataki na biyu
Za a fara tattauna wannan mataki ne bayan fara aiwatar da matakin farko
Ana sa ran cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin, yayin da Hamas za ta saki ragowar Isra'ilawan da ke hannunta, inda Isra'ila za ta sako ƙarin fursunoni
Isra'ila za ta kammala ficewa daga Gaza
Mataki na uku
Matakin ƙarshen shi ne mayar da duka gawarwakin Isra'ilawan da Hamas ke riƙe da su, tare da fara sake gina Gaza
Isra'ila ta kammala sakin fursunonin Falasɗinawa 183 da aka tsara saki yau
Hukumar kula da gidajen yarin Isra'ila ya ce an kammala sakin duka fursunoni 183 da aka tsara saki yau a wani ɓangare na yarjejeniya da Hamas.
Fursunonin da aka saka gidajen yarin Ofer da Ktziot an mayar da su Ramallah da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, yayin da aka kai wasu birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza.
Tun da farko dai Hamas ce ta fara sakin Isra'ilawa uku da take garkuwa da a Gaza.
'Falasɗinawa 18 cikin waɗanda aka saki yau na zaman hukuncin ɗaurin rai da rai'
Ofishin yaɗa labaran fursunoni na Hamas ya ce daga cikin Falasdinawa 183 da ake sa ran saki yau, 18 daga ciki na zaman hukuncin ɗaurin rai da rai ne, yayain da 54 daga ciki ke zaman hukuncin ɗaurin shekaru masu yawa, yayin da 111 daga cikinsu aka kama su bayan harin ranar 7 ga watan Okotabn 2023.
"Sakin fursunonin wani mataki ne kan gwagwarmayar sakin duka fursunonin Falasdinawa da muke yi,'' kamar yadda ofishin ya bayyana cikin sanarwa da ya fitar.
Kafin yau an saki fursunoi 383, a wani mataki na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas, wadda ta fara aiki a watan da ya gabata.
An kashe mutum 32 a wani hari a Mali
Asalin hoton, .
Jami'ai a Mali sun ce aƙalla mutum 32 ne suka mutu bayan wani hari da aka kai wa ayarin motocin fararen hula a arewacin Mali.
Rahotonni daga yankin sun ce masu iƙirarin jihadi ne suka yi wa jerin gwanon motocin - waɗanda ke samun rakiyar sojojin ƙasar da na sojojin hayar Rasha wato Wagner.
Harin ya auku ne tsakanin manyan garuruwan Gao da Ansongo a ranar Juma'a da maraice.
Wani jami'in ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa waɗanda suka mutun sun haɗa da fararen hula da kuma sojoji.
A baya-bayan nan hare-hare a kan manyan titunan Mali ma ƙaruwa, wani abu da ake ɗora alhakinsa kan masu iƙirarin jihadi da 'yan fashin daji.
Kawo yanzu sojojin mulkin ƙasar ba su ce komai ba kan harin.
Mali ta shafe tsawon shekara 10 tana fama da rikici tun bayan da 'yantawaye suka fara tayar da hankali a ƙasar.
Hotunan musayar fursunoni na biyar da aka yi yau
Isra'ilawa uku da Hamas ta sako cikin wadanda take garkuwa da su a Gaza sun isa Isra'ila, yayin da manyan motocin bas ke ci gaba da jigilar Falasɗinawan da aka sako daga gidajen yarin Isra'ila.
An fara ne da unguwar Deir al-Balah da ke Gaza, inda Hamas ta miƙa Isra'lawa uku ga jami'an Red Cross.
Asalin hoton, Reuters
Dandazon mutane sun taro a dandalin - tunawa da waɗanda Hamas ta yi garkuwa - da ke birnin Tel Aviv, domin kallon yadda sakin mutanen za ta kaya kai-tsaye ta allunan majigi.
Asalin hoton, EPA
Jim kaɗan bayan mutanen uku sun isa Isra'ila, wata motar bas maƙare da fursunonin Falasdinawa ta isa birnin Ramallah da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Asalin hoton, Reuters
Labarai da dumi-dumi, Falasɗinawan da Isra'ila ta saki sun isa Ramallah
Wata motar bas ɗauke da fursunonin Falasɗinawa kimanin 43 sun isa birnin Ramallah da ke Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Ƴan'uwa da abokan arzikin fursunonin sun yi wa motar ƙawanya cike da murna da farin ciki, inda suka riƙa ɗaukar hotuna da rungumar fursunonin a lokacin da fursunonin suka fara fitowa daga cikin motar.
Fursunonin sun riƙa murna da gaisawa da dandazon mutanen da ke yi musu maraba.
Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta fara sakin Falasɗinawa daga gidajen yarinta
Isra'ila ta fara sakin Falasɗinawan da ke tsare a gidajen yarinta.
Tuni motar bas ta fice daga gidan yarin Ofer ɗauke da fursunoni 43.
Fursunoni kimanin 183 ne ake sa ran ISra'ila za ta saki yau daga gidajen yarinta domin musayarsu da Isra'ilawa uku da Hamas ta saki tun da farko.
Kawo yanzu ISra;ila ta saki Falasɗinawa 383 da ke tsare a gidajn yarinta, inda ake sa ran sakin 1,900 kamar yadda yarjejeniyar ta nuna.
Za a kai fursunonin da za a saka yau zuwa gaɓar Yamma da Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza.
'Isra'ilawa uku da Hamas ta saki sun yi matuƙar ramewa'
Asalin hoton, .
Iyalan Isra'ilawan na uku da Hamas ta saki yau a Gaza sun ce mutanen sun bayyana cikin matuƙar ramewa, a lokacin da mayaƙan Hamas suka gabatar da su kan dandamali a unguwar Deir al-Balah da ke tsakiyar Gaza.
Ƙungiyar ta tilasta musu gabatar da jabawai gabanin miƙa su ga ƙungiyar agaji ta Red Cross.
An kama Eli Sharabi da Ohad Ben Ami daga kibbutz Be'eri, yayain da aka kama Or Levy a bikin kalankuwa na Nova.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar iyalan ISra'ilawan da aka yi garkuwa da su, ta ce yadda aka bayyana mutanen abin ''tayar da hankali'' ne.
Ta kuma ce hakan alama ce da ke tabbatar da cewa bai kamata a ɓata lokaci wajen sako sauran mutanen da ke hannun Hamas ba.
Ana sa ran masu shiga tsakani na Isra'ila za su nufi Qatar domin tattaunawa kan mataki na gaba na tsagaita wuta a Gaza.
Ƙasashen gabashi da kudancin Afirka na taro kan rikicin DR Congo
Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar ƙasashen gabashi da kudancin Afirka na gudanar da wani muhimmin taro a Tanzaniya domin lalubo hanyoyin magance rikicin da ke ci gaba da bazuwa a DR Congo.
Shugaba Felix Tshisekedi na DR Congo na halartar taron ta bidiyo, maimakon tura firaministansa, Judith Suminwa da ya yi niyyar yi tun da farko.
Shugaban ƙasar Burundi, Evariste Ndiyishimiye, wanda ke goyon bayan DR Congo shi ma ya aike da firaministansa zuwa taron.
Yayin da shugaban ƙasar Rwanda Paul Kamage ke halartar taron.
Ana sa ran taron zai cimma yarjejeniyar tsagaita wuta domin daƙile yaduwar yaƙin zuwa wasu yankunan kudanci da gabashin Afirka.
Tshisekedi ya sha faɗin cewa ba zai yi sulhu da M23 ba, a maimakon haka ya yi ta kiran janyewar Rwanda daga yankunanta tare da ƙaƙaba takunkumi kan Kigalin.
An samu gagarumar rashin jutuwa tsakanin DR Congo da Rwanda, yayin da shugaba Tshisekedi ke zargin Rwanda da mara wa 'yantawayen M23 baya wajen ƙwace iko da wasu yankunan ƙasarsa, ciki har da birnin Goma da ke gabashin ƙasar.
A ɗaya gefen kuma Rwanda ta yi watsi da dakarun wanzar da zaman lafiya na ƙungiyar ƙasashen Kudancin Afirka da ke aiki a DR Congo, bayan da ta zarge su da taimaka wa DR Congo wajen yaƙar al'umarta.
Bidiyon yadda Hamas ta saki Isra'ila uku a Gaza
Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Mayaƙan Hamas sun gabatar da Isra'ilawa uku da za ta saki yau a kan dandamali a gaban ɗaruruwan Falasdinawa a unguwar Darel-a-Balah da ke tsakiyar birnin Gaza.
Isra'ilawan sanye da tufafi mai launin makuba sun samu rakiyar mayaƙan hamas bibbiyu kowansu
Mayaƙan na Hamas sun gabatar wa Isra'ilawan takardun shaida, sannan suka yi hira da su a gaban ɗimbin Faasɗinawan da suka hallara a wurin, kafin miƙa su ga jamai'ar Red Cross.
Jiragen IDF na dakon Isra'ilawan da aka saki domin mayar da su Isra'ila
Rundunar sojin Isra'ila ta ce tuni jiragensta suka isa wurin da za karɓi Isra'ilawan da Hamas ta saki domin ɗaukarsu zuwa Isra'ila.
Cikin wata sanarwa da IDF ta wallafa a shafinta na X ta ce tana sa ran motocin ƙungiyar Red Cross da ke dauke da mutanen za su isa wurin nan ba da jimawa ba.
An samar da wuraren da mutane za su tsaya a kan iyakar Isra'ila domin yi wa mutanen tarba yayin da suka koma ƙasar.
Labarai da dumi-dumi, Hamas ta saki Isra'ilawa uku
Hamas ta miƙa wa ƙungiyar agaji ta Red Cross, Isra'ilawa uku da ta saki a yau.
Tuni dai jami'an na Red Cross suka ɗauki mutanen uku a motocinsu, domin hannunta su ga hukumomin Isra'ila.
Ƙungiyar za ta miƙa su ga rundunar sojin Isra'ila da za su ɗauke su a jirage masu saukar ungulu zuwa asibiti domin a duba lafiyarsu, kafin sada su da iyalansu.