'Yan hamayya sun kwarmata saƙonnin da suka shafi alaƙar Trump da Epstein
'Yansiyasar Amurka na jam'iyyar Democrat mai adawa sun fitar da wasu sakonnin imel da suka ce suna da alaka da masaniyar Shugaban Ƙasa Donald Trump kan laifin cin zarafi ta hanyar lalata da Jefferey Epstein ya aikata.
Ɗaya daga cikin sakonnin da Epstein ya aika ya ce shugaban ya san 'yanmatan, amma ba a yi cikakken bayani a kai ba.
Fadar gwamnatin Amurka ta zargi 'yan Democrat da yunƙurin ɓullo da bayanan ƙarya.
Mista Trump ya sha nanata cewa bai aikata komai ba kuma ba shi da wata alaƙa da Epstein.


