Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 28/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 28/10/2025

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Venezuela ta dakatar da yarjejeniyar makamashi da Trinidad & Tobago

    Venezuela

    Asalin hoton, Getty Images

    Venezuela ta ce ta dakatar da yarjejeniyar makamashin da ta kulla da makwabciyarta Trinidad da Tobago saboda ziyarar da wani jirgin ruwan yakin Amurka ya kai gabar ruwan kasar.

    Cikin jawabi daya gabatar ta kafar talbiji ga 'yan kasarsa, Shugaba Nicolas Maduro ya bayyana cewa Caracas za ta dakatar da duk wasu tsare tsare da aka yi akan wani aikin bunkasa makamashi na hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

    Jirgin ruwan na Amurka na aiki ne akan abin da gwamnatin Trump ta ce yaki da kananan jiragen masu ta'ammali da kwayoyi a gabar ruwan kasar.

    Mr Maduro ya kira matakin Trinidad na karbar jirgin ruwan yakin Amurka a matsayin cin amana. A ranar Lahadi Mr Maduro ya zargi Amurka da kokarin hambarar da gwamnatinsa.

  2. Trump ya yi alƙawarin ƙarfafa rundunar sojin Japan

    The White House

    Asalin hoton, The White House

    Shugaba Trump ya jinjinawa sabuwa Firaiminitsar Japan, Sanae Takaichi, a yayin ganawar da suka yi a Tokyo.

    Shugaban na Amurka ya shaida mata cewa za ta zamo daya daga cikin firaiminista na gari da aka yi a duniya sannan kuma ya yi alkawarin karfafa rundunar sojin Japan da kuma sayar mata da kayayyakin da za ta kare kanta daga abokan gaba.

    Wakiliyar BBC ta ce shugaba Trump ya ce Japan babbar abokiyar hulda ce inda ya kara da cewa a shirye ya ke a kodayaushe idan ana bukatar taimakonsa.

    Shugabannin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi da suka hada da na kasuwanci da kuma na albarkatun kasa masu matukar muhimmanci.

    A makon da ya gabata ne aka zabi Ms Takaichi a matsayin firaminitsar Japan din wadda ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin a kasar.

  3. Al'umar Jamaica na fargabar fuskantar guguwar Melissa

    Melissa

    Asalin hoton, CSU

    Jamaica na cikin shirin kar ta kwana dangane da isowar guguwar nan mai kafin gaske ta Melissa.

    Ana kyautata tsammanin guguwar za ta fada yankin da safiyar yau Talata, wanda kuma shi ne karon farko da wata guguwa za ta fada yankin a cikin shekaru sama da 35.

    Guguwar wadda gudunta ya kusa kai wa kilomita 300 a cikin sa'a guda, masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa za ta iya haddasa ruwan sama mai karfin gaske da zai iya janyo mummunar ambaliyar ruwa da kuma zaftarewar kasa.

  4. Kotu ta wanke ango da ƴanuwansa daga zargin kashe ƴarsanda a Rivers

    Kotu

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotu mai zamanta a birnin Fatakwal na jihar Rivers ta wanke wasu matafiya guda 12 da aka kama bisa zargin su da kashe wata jami'ar ƴarsanda, Insfekta Christiana Erekere a ranar 25 ga watan Afrilun 2024.

    Erekere jami'a ce da ke aiki a ofishin ƴansanda na Taabaa da ke ƙaramar hukumar Khana na jihar ta Rivers a lokacin da ta rasu.

    Mai shari'a Augusta Chukwu, wadda ta yanke hukuncin a ranar Litinin ta ce masu ƙara sun gaza wajen gabatar da gamsassun shaidu da za su tabbatar matafiyan ne suka kashe ƴarsandar.

    Waɗanda kotun ta wanke su ne: Efeoghene Uwheraka wanda shi ne angon da Joy Uwhereka da Shirley Wealth da Napoleon Uwhereka da Ejiro Ejogbamu da Moses Agege da Precious Iyota da Kikelomo Odusanya da Wealth Ojoh da Ighofose Oke da Blessing Ovie da Emeka Joshua kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.

    Lamarin ya auku ne a lokacin da suke kan hanyar tafiya bikin Efeoghene a jihar Akwa Ibom, inda ƴansanda suka tsayar da su domin binciken takardun motarsu, lamarin da ya haifar da saɓani a tsakaninsu har ƴarsandan ta rasa ranta.

    Mai shari'ar ta ce dukkan shaidun da aka gabatar jita-jita ne kawai, inda ta wanke waɗanda ake zargin sannan ta ce a ba kowannensu diyyar naira miliyan 1 bisa tsare su da aka yi na kusan wata 18 ba bisa ƙa'ida ba.

    Sai dai dangin marigayiyar sun nuna rashin jin daɗinsu da hukuncin, inda suka ce za su duba yiwuwar ɗaukaka ƙara.

  5. Zan tabbatar da haɗin kan ƴan Kamaru - Paul Biya

    Kamaru

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayan nasarar da ya samu a karo na takwas, shugaba kasar Kamaru Paul Biya mai kimanin shekaru 92 da haihuwa ya yi alkawarin dawo da hadin kai da zaman lafiya a kasar.

    Paul Biya ya kasance a kan mulki tsawon shekaru 42 da suka gabata sannan kuma shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya.

    Babban dan adawar kasar Issa Tchiroma Bakary, ya yi watsi da sakamakon zaben da aka fitar wanda ya janyo tashin hankali, inda ya yi zargin cewa wasu mutane sun kashe masa magoya bayansa biyu a kofar gidansa.

    Ƴansanda sun yi amfani da ruwan zafi da kuma hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zanga a Douala.

  6. Dakarun RSF sun ƙwace birnin El-Fasher na Sudan

    RSF

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban rundunar sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya ce sojojin ƙasar sun janye daga waje na ƙarshe da ya rage a ƙarƙashin ikon su a yammacin El-Fasher domin gudun kada a rusa shi, yayin da mayaƙan RSF suka ƙwace ikon birnin.

    Rahotanni sun ce akwai dubban sojoji da har yanzu mayakan RSF suka yi wa kawanya a wajen yammacin birnin. RSF dai ta musanta zarge zargen da ake yadawa cewa tana kashe fararen hula, to amma kungiyoyin agaji na fargabar an yi wa kabilun da ba larabawa da suka makale a birnin kisan kiyashi.

    Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce kawanyar da aka yi wa birnin na El Fasher tsawon watanni 18, ya jefa mazauna yankin cikin mummunan yanayi na yunwa da cutuka ga kuma tashin hankalin fadan da ake gwabzawa.

    Wakiliyar BBC ta ce Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa mutane dubu 26 sun tserewa birnin El Fasher a cikin kwana biyu da suka wuce abin da ke nuna yanzu mutanen da suka rage a birnin basu wuce kashi 10 cikin 100 ba.

  7. Buɗewa

    Barkanmu da safiyar Talata, barkanmu da sake saduwa a wannan shafin na labaran kai-tsaye.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu n sada zumunta domin karanta wasu labaran da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu