Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 28/10/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Talata 28/10/2025

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin kawo muku wasu sabbin labaran.

    Amma kafin nan, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Labarai da dumi-dumi, Isra'ila ta kashe Falasɗinawa biyar bayan ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza

    Sabbin hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza sun yi sanadiyyar mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda kamfanin dillacin labari na AFP ya ruwaito.

    AFP ta ruwaito ma'aikatan tsaron fararen hula da ke Gaza na cewa wani harin da ya faɗa kan wata mota da ke tsaka da tafiya a kudancin Gaza ya kashe mutum biyar.

    Hare-haren na zuwa ne sa'o'i bayan Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar su koma kai hare-hare, saboda taƙaddamar da aka samu kan wata gawa da Hamas ta mayar ƙasar.

  3. Guguwar Melissa na ci gaba da ɓarna a Jamaica

    Guguwar Melissa na ci gaba da ɓarna a garuruwa da dama na ƙasar Jamaica, inda Hukumomi suka yi hasashen samun ƙarin iska mai ƙarfin gaske, wanda ke tafiyar kilomita 300 cikin sa'a ɗaya.

    Hukumar Lura da Yanayi ta duniya ta ce guguwar ta Hurricane Melissa ita ce irinta ta farko a ƙasar da ta fi yin ɓarna a wannan ƙarni.

    Shugaban hukumar lura da yanayi ta Jamaica Evan Thompson, ya ce bayan da guguwar ta afka wa ƙasar har yanzu ana sa ran za ta ƙara yin babbar ɓarna ciki kuwa har da rasa rayuka.

    Hukumomin Jamaica na ci gaba da ɗaukar matakan kwashe mutane daga wuraren da guguwar ta fi ƙamari, duk da sun ce jama'a na ci gaba da watsi da umurnin gwamnati na neman wuraren fakewa.

  4. Jami'ai a Kenya sun tabbatar da mutuwar masu yawon shaƙatawa ƴan ƙasashen Turai da matuƙin jirgin da ya yi hatsari a ƙasar.

    Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta ƙasar, ta bayyana cewa Jirgin ya taso ne daga fitaccen wurin shaƙatawa na Diani da ke Maasai Mara.Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce jirgin na ɗauke da ƴan ƙasar Hungary takwas da Jamusawa 2 da kuma matuƙin jirgin ɗan Kenya a lokacin da suka yi hatsarin kuma dukkan mutanen sun rasu.

    Kafar yada labaran Kenya ta wallafa hotunan yadda jirgin ke ci da wuta, yayin da ɓaraguzansa suka watsu a inda ya faɗi.

    Kwamishinan yankin Kwale da hadarin ya faru a wurin Stephen Orinde ya shaidawa BBC jirgin ya fadi nisan kilomita 10 daga garin Kwale bayan tasowa daga Diani.

    Ya ƙara da cewa jirgin na kan hanyarsa ta zuwa wurin shaƙatawar Kitcha Tembo da ke Maasai Mara, wanda ke cike da nau'o'in namun daji daban-daban.

    Tuni dai hukumomi suka fara gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin da ake kyautata zaton rashin kyawun yanayi ne ya haddasa shi.Ko a watan Agusta da ya wuce wani jirgi mallakin ƙungiyar bayar da agaji ta Amref ya yi hatsari a wajen birnin Nairobi, inda mutum shida suka mutu wasu biyu suka jikkata.

  5. Amurka ta hana Wole Soyinka shiga ƙasar

    Fitaccen marubucin adabin nan ɗan Najeriya, Wole Soyinka, ya ce a bara Amurka ta dauki matakin kwace takardunsa na izinin shiga kasar.

    Mawalafin - wanda a shekarar 1986 ya lashe lambar yabo ta Nobel ɓangaren adabi - ya ce yanzu Amurkar ta soke takardun nasa domin haramta masa shiga ƙasar.

    Wole Soyinka ya ce Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya nemi ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiye-tafiye, domin a kammala ɗaukar matakin sokewar.

    Marubucin dai ya taɓa koyarwa a wasu daga jami'o'in ƙasar kimanin shekara 30 a baya.

    Kuma har kawo yanzu ofishin jakandin Amurkar da ke Najeriya bai ce kome ba akan batun.

  6. Ethiopia na son samun damar amfani da Tekun Maliya

    Ethiopia ta yi kira ga manyan ƙasashen duniya - ciki har da Amurka da China da Rasha - su sanya baki a yunƙurinta na samun damar amfani da tekun Maliya.

    Firaiministan ƙasar, Abiy Ahmed, ya bayyana ƙudirin ƙasar tasa da cewa ''babu makawa'', kuma ''dole ta samu''.

    Ethiopia ta rasa iyaka da bakin ruwa tun bayan da Eritrea ta samu ƴancin kai fiye da shekara 30 da suka gabata.

    A yanzu ƙasar na dogara da sauran makwabtanta, irin su Djibouti wajen shigar da fitar da kayyaki.

    Eritrea ta dage cewa ba za ta yarda a tattauna ko ƙulla yarjejeniya a abin da ya shafi ikonta ba.

  7. Netanyahu ya bayar da umarcin ƙaddamar da hare-hare a Gaza

    Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayar da umarni ga sojojin ƙasar su ƙaddanmar da munana hare-hare a Zirin Gaza.

    Hakan na zuwa ne bayan taƙaddama tsakanin ɓangarorin biyu kan wata gawar da Hamas ta mayar Isra'ila.

    Isra'ila ta ce da gangan Hamas ta mayar mata da guntun wata gawar da ta riga ta mayar kusan shekaru biyu da suka gabata.

    Sai dai Hamas ta dage cewa tana biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan da ya gabata.

    Tana mai cewa Isra'ila ne neman wata sila ce kawai don sabunta yaƙin.

  8. Za a aike da ƴansanda 45,000 don kula da zaɓen Anambra

    Babban Sifeton ƴansandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya amince da aika jami'an ƴansanda 45,000 domin bayar da tsaro a lokacin zaɓen gwamnan jihar Anambra da za a yi ranar 8 ga watan Nuwamban 2025.

    Egbetokun - wanda kwamishinan ƴansanda mai lura da dakarun kai ɗaukin gaggawa - ya bayyana hakan ne ranar Talata a lokacin wata ganawa da kwamitin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da aka gudanar a shalkwatar hukumar zaɓen ƙasar da ke Abuja.

    Babban Sifeton ƴansandan ya ce jami'an da za a tura za su tabbatar da tsaro a kafin zaɓen da lokacin zaɓen da ma bayan zaɓen.

    Ya ƙara da cewa za a fara tura jami'an ne tun daga ranar 1 ga watan Nuwamba domin kawar da duk wata barazana ga zaɓen.

    Egbetokun ya kuma ce baya ga jami'an ƴansanda akwai sauran hukumomin tsaro da za su taka rawa a zaɓukan da suka haɗa da na farin kaya, DSS da rundunar tsaron fararen hula da sibil difens da sojoji.

  9. Guguwar Hurricane Melissa ta isa Jamaica

    Hukumar da ke lura da yanayi ta duniya ta ce guguwar nan da aka yi wa laƙabi da Haurrcane Melissa za ta yi mummunar ɓarna a Jamaica.

    Guguwar dai na tafiya da iska mai ƙarfi kuma tana gudun fiye da kilomita ɗari uku a sa'a ɗaya.

    Hukumar lura da yanayin ta bayyana Melissa a matsayin guguwa mai matukar hadari da ta afkawa kasar, inda aka samu gagarumar ambaliya da zaftarewar kasa, baya ga dubban bishiyoyi da iskar ta tumbuke kana akalla mutum uku suka rasa rayukansu.

    "Muna sa ran samun karuwar taadin guguwar daga irin bayanan da muke samu daha Hukumar lura da yanayi ta Jamaika. Muna fuskantar gagarumin hadari, inda ya zama wajibi mu yi shirin ko-ta-kwana domin daukar dukar matakan da suka dace," in ji Richard Vernon, magajin birnin Montego

  10. Majalisar Ɗinkin Duniya na neman a binciki jami'an tsaron Kamaru kan zanga-zanga

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kaɗu da samun rahotannin da ke cewa an kashe da jikkata da kuma kama mutane tun bayan zanga-zangar da aka yi a fadin jamhuriyar Kamaru a ranar Lahadi, inda ta yi kira da a gudanar da bincike tare da kawo ƙarshen tashin hankalin.

    Amnesty International kuwa ta yi kira ne ga gwamnatin Kamarun da ta “girmama, ta kare, ta kuma ba da damar ‘yancin gudanar da taro cikin lumana.”

    Kungiyar ta kuma dage kan cewa wajibi ne a gaggauta gudanar da bincike mai zaman kansa kan mutanen da suka mutu, don yin ƙarin haske kan al'amuran da suka faru.

    Yayin da take kiran da a saki duk wadanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba saboda zanga-zangar da ta biyo bayan zaben, ƙungiyar Human Rights Watch ta buƙaci da a taka wa jami’an tsaron ƙasar birki, ta la’akari da yadda suke amfani da ƙarfin da ya wuce ƙima.

    Ilaria Allegrozzi, wata babbar mai bincike a Human Rights Watch reshen Afirka, ta ce kamata ya yi jami'an tsaro su kasance suna kare mutane, ba wai suna rura wutar tashin hankali ba.

    A nata ɓangaren ƙungiyar Tarayyar Turai EU, ita ma ta ce ta damu matuƙa game da yadda aka murƙushe masu zanga-zangar a ranakun 26 da 27 ga watan Oktoban 2025, tare da nuna rashin jin dadin yadda wasu fararen hula suka mutu sakamakon harbin bindiga.

    Kungiyar ta yi kira ga mahukuntan Kamaru da su tabbatar da gaskiya da kuma adalci wajen bincikar zargin amfani da karfin da wuce kima da cin zarafin bil'adama.

    Kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci dukkan bangarorin da su kiyaye da kuma kaurace wa duk wani mataki da zai kara ta'azzara tarzoma

  11. 'Mayaƙan RSF sun yi wa mutane kisan kiyashi a El-Fasher'

    Wasu masu bincike 'yan kasar Amurka sun ce sun gano shaidun an aikata kisan kiyashi lokacin da dakarun RSF suka karbe iko da birnin El Fasher daga sojojin gwamnatin Sudan.

    Cibiyar mai bincike akan ayukan jinkai ta Jami'ar Yale, ta ce wasu hotunan tauraron dan adam sun nuna gawawarwakin mutane birjik kwance kusa da ganuwar birnin da ma motocin mayakan na RSF.

    Iyalai da dama na bayyana yadda suke yawan samun labarin mutuwar 'yan'uwansu: Hashim ya ce a cikin kwana goma ya rasa 'yanuwa goma, wadanda dukan su na kusa da shi ne,

    "Idan ana maganar sauran 'yan uwa nesa kuwa adadin baya kirguwa."

    Kungiyar Kasashen Afirka, ta yi Allah-wadai da abin da ta kira mummunan yaki mai nasaba da take hakkin dan Adam da kuma ya saba wa dokokin kasa da kasa.

    To sai duk da haka, mayakan na RSF sun musanta zarge-zargen da ake yi cewa suna cin zarafin jama'a.

  12. Ƴansanda sun ƙuduri aniyar yaƙi da ƴan ƙungiyar asiri na Red Command a Brazil

    Ƴansanda a Brazil sun kaddamar da wani gagarumin samame domin dakile ayukkan kungiyar 'yan asiri ta Red Command da ke ayukanta a arewacin babban birnin kasar Rio de Janeiro.

    Kimanin jami'an tsaro dubu biyu da dari biyar ne suka bazama domin yaki da daruruwan membobin kungiyar tsagerun.

    Ƴansandan sun kuma kai samame a gundumomin Alemão da kuma Penha, inda can ma an samu arangama tsakaninsu da kungiyoyin asirin, wadanda suka mayar da martani ta hanyar harbi da bindiga da kuma amfani da jirage marasa matuka da suke jefa bama-bomai, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum hudu.

    Wakilin BBC ya ce an ga hayaki na tashi a wurare da dama na birnin.

  13. Zan ɗauki mataki kan Hamas saboda karya alƙawarin tsagaita wuta - Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin mayar da martani kan abin da ya kira saɓa alƙawarin yarjejeniyar tsagaita da ya ce Hamas ta yi wajen miƙa sassan gawar wani wanda ba ya cikin waɗanda ake nema su miƙa.

    Daga cikin yarjejeniyar da aka tsara akwai miƙa dukkan waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su d a suke raye da matattu.

    Sai dai ƙungiyar ta miƙa dukkan waɗanda suka raye, amma har yanzu ba ta kammala miƙa gawarwakin ba, lamarin da ya sa ake zargin ƙungiyar da yunƙurin karya yarjejeniyar.

    A nata ɓangaren, ta ce nemo gawarwakin na da wahalar gaske ne "saboda baraguzan gine-ginen da Isra'ila ta rusa ya rufe su."

  14. 'Guguwar Melissa za ta yi mummunar ɓarna a Jamaica'

    Hukumar da ke lura da yanayi ta duniya ta ce ana hasashen guguwar nan da aka yi wa lakabi da Haurrcane Melissa za ta yi mummunar barna a Jamaika nan da 'yan sa'o'i masu zuwa.

    Guguwar dai na tafiya da iska mai karfi kuma tana gudun fiye da kilomita dari uku a sa'a daya.

    Hukumar lura da yanayin ta bayyana Melissa a matsayin guguwa mai matukar hadari da ta afkawa kasar, inda aka samu gagarumar ambaliya da zaftarewar kasa, baya ga dubban bishiyoyi da iskar ta tumbuke kana akalla mutum uku suka rasa rayukansu.

    Magajin garin birnin Montego Richard Vernon ya ce "muna sa ran samun karuwar ta'adin guguwar daga irin bayanan da muke samu daha Hukumar lura da yanayi ta Jamaica."

    Muna fuskantar gagarumin hadari, inda ya zama wajibi mu yi shirin ko-ta-kwana domin daukar dukar matakan da suka dace.

  15. Gobe majalisa za ta tantance sababbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya

    A gobe Laraba ne majalisar dattawa ta Najeriya za ta tantance sababbin manyan hafsoshin tsaron ƙasar da Shugaba Bola Tinubu ya naɗa.

    Tinubu ya aike da sunayen sababbin hafsoshin ne zuwa ga majalisa domin tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

    Shugaban majalisar Sanata Godwill Akpabio ya tabbatar da karɓar wasiƙar ta shugaban ƙasa, inda ya ce kwamitin da ke da alhakin aikin zai zauna gobe ya tantance su.

    Tinubu dai ya yi sauye-sauye ne a ɓangaren tsaron ƙasar, inda ya ɗaga darajar Laftanar Janar Oluyede Olupemi daga babban hafsan sojin ƙasa zuwa babban hafsan tsaron ƙasar domin ya maye gurbin Janar Christopher Musa wanda aka cire.

    Sannan ya naɗa sababbin hafsoshin sojin sama da na ruwa da ƙasa, sannan ya bar babban hafsan sashen tattara bayanan sirri na sojin ƙasar, Manjo Janar E.A.P. Undiendeye.

  16. Ana zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaɓen Kamaru a Garoua

    Al'ummar yankin Garoua na ƙasar Kamaru na ci gaba da gudanar da zanga-zangar rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar.

    Paul Biya mai kimanin shekara 92 ne dai ya lashe zaɓen domin ci gaba da mulki bayan kusan shekara 42 yana mulkin ƙasar.

    Abokin takararsa Issa Bakary dai ya dage kai da fata cewa shi ne ya lashe zaɓen.

  17. 'Fargabar ɗaukar fansa ce ta sanya wasu ke adawa da Tanimu Turaki'

    A Najeriya, ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki ya mayar da martani kan masu zargin cewa an yi ƙarfa-ƙarfa wajen cimma matsayar goyon bayansa domin neman shugabancin jam'iyyar PDP na ƙasa daga shiyyar Arewa.

    Martanin nasu na zuwa ne bayan wasu daga cikin shugabannin jam'iyyar PDP na shiyyar arewa maso yammacin ƙasar, shiyyar da Turaki ya fito suka yi watsi da matakin da gwamnoni arewacin ƙasar suka ɗauka na tsayar da shi a matsayi ɗan takarar maslaha.

    Umar Sani Tsoro na hannun daman Turaki kuma a zantawarsa a BBC, ya ce ba a karya doka ba wajen amincewa da Turaki a matsayin ɗantakara.

    Ya ce, "yawanci suna fargabar idan ya hau zai yi wani ramakon gayya ne, alhali ba su san shi ba haka yake ba. PDP tana da tsari, kuma tsarin aka bi ba tare da kauce wa wata doka ba. Kafin a fitar da shi a matsayin ɗantakarar maslaha, sai da aka yi taro da wakilan kowace jiha."

    Umar Sani ya ce a wajen taron akwai dukkan ƴantakarar, "Sule Lamido ne kawai ba ya wajen. Aka ce duk wanda yake son takara ya ɗaga hannu. Turaki ya ɗaga hannu, Malam Ibrahim Shekarau ya ɗaga, sai Ahmed Makarfi ya ce Sule Lamido ba ya nan, amma yana da sha'awar takara sai aka ce ya wakilce shi a wajen taron," in ji shi.

  18. Hatsarin jirgin masu yawon shaƙatawa ya kashe mutum 11 a Kenya

    Wani jirgi ɗauke da masu yawon buɗe ido a ƙasar Kenya ya yi hatsari, inda ya kashe dukkanin mutum 11 da ke cikinsa.

    Mutane takwas daga fasinjojin da ke cikin jirgin sun fito ne daga ƙasar Hungary, sai biyu daga Jamus, yayin da matuƙin jirgin ya kasance ɗan asalin kasar ta Kenya.

    Ƙaramin jirgin saman na kan hanyarsa ce daga garin Diani da ke gaɓar teku zuwa gandun daji na Maasai Mara.

    Tawagar masu bincike ta isa wurin da lamarin ya faru.

    Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun wallafa hotunan yadda jirgin ke ci da wuta bayan faɗuwa ƙasa yayin da za a iya ganin tarkace jirgin da ya tarwatse.

  19. Mutumin da Hamas ta ba mu gawarsa jiya ba ya cikin waɗanda ta yi garkuwa da su - Isra'ila

    Isra'il ta tabbatar da cewa gawar mutumin da Hamas ta miƙa mata a ranar Litinin ba ta cikin gawarwakin da ƙungiyar ta yi garkuwa da su da aka tsara za ta mayar da su.

    Har yanzu dai ana neman gawarwaki 13 daga cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, waɗanda ake tunanin za ta miƙa domin cika sharuɗan yarjejeniyar tsagaita wuta da Shugaba Trump ya tsara domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

    Isra'ila ta ce wannan gawar da aka miƙa mata na cikin waɗanda ake tunanin an yi garkuwa da su, suka mutu a Gaza aka binne su a can.

    Hukumomin Isra'ila na dai ganin wannan a matsayin yunƙurin Hamas na karya alƙawarin da aka shiga domin kawo ƙarshen yaƙin.

    Yanzu haka dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana ganawa da jami'an gwamnatinsa domin tattauna matakin da zai ɗauka.

    Daga cikin matakan da ake tunanin Isra'ila za ta ɗauka akwai ƙara faɗaɗa wuraren da take da iko da su a Gaza.

  20. Mutum uku sun rasu a sanadiyar guguwar Melissa a Jamaica

    Guguwar Melissa wadda ake tunanin ita ce guguwa mafi ƙarfi a wannan shekarar na ƙara tunkarar Jamaica, inda take ƙara kutsawa ƙasar ta arewacin tekun Caribbean.

    Tuni aka kwashe mutanen yankunan ƙasar da dama zuwa wasu wuraren da ake tunanin akwai sauƙi, amma duk da haka, yanayin ƙarfin guguwar na ƙara jefa mutanen ƙasar cikin tashin hankali, kamar yada manema labarai suka ruwaito daga Jamaica.

    Zuwa yanzu ana tunanin guguwar ta yi ajalin mutum uku a ƙasar Jamaica, sannan ta yi ajalin mutum huɗu a Haiti da Jamhuriyar Dominican.