Ana fifita manyan sojoji a kan mu – Kananan sojoji

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Wasu tsoffin sojoji a Najeriya sun koka kan abin da suka kira gata da alfarma da ake nuna wa manyan hafsoshin sojin kasar bayan barin aiki, yayin da ƙananan jami'ai ke ci gaba da fama da rashin kula da kuma rashin biyan hakkokinsu duk da shekaru da suka kwashe suna hidimtawa kasa.

Tsoffin sojojin sun yi wannan kokaen ne bayan bayan sanar da irin abubuwan da za a ba wa Tsohon Babban Hafsan Tsaro da aka sauke, Janar Christopher Musa, tare da Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, da Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, a matsayin ladan barin aiki.

Bayanai sun nuna cewa kowanne daga cikin sojojin masu ritaya zai samu motar sulke daya mai daraja, sannan za'a dinga kulawa da ita tare da maye ta da sabuwa bayan duk shekara hudu, da kuma wata motar alfarma kirar Prado ko makamanciyar ta.

Akwai kuma damar rike kakin soji tare da ikon sanyawa a taruka, da kuma ba su masu yi musu hidima mutum biyar, biyu masu dafa musu abinci da dogarai guda biyu da mai aikin lambu daya, da dakaru biyu masu muƙamin Laftanar ko Kaptin, da kuratan soji tara, da direbobi uku da kuma rike bindigoginsu tare da dawo da su idan sun mutu, da ma kula da lafiyarsu a cikin Najeriya da kasashen duniya.

Wannan gata da aka nuna ma manyan sojojin da suka yi ritaya ya sanya tsoffin sojojin kokawa tare da ikirarin cewa ana nuna halin ko-in-kula da kuma bambanci a tsakanin manyan hafsoshin soji da ƙananan ta ɓangaren walwala da biyan hakkoki.

Wasu tsoffin sojojin da ke wannan koke sun shaida wa BBC cewa, " Bamu ji dadi ba kuma ba'ayi mana adalci ba, kuma irin wannan wariya da ake nuna mana shi ne dalilin barin aikin wasu daga cikinmu ma."

To sai dai a wata sanarwa da mai ba wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Sunday Dare, ya fitar, ya ce a cewar kundin dokar aikin Rundunar Sojin da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 14 ga Disamba, shekarar 2024, an tanadi wannnan tagomashi ga hafsoshin da suka kai matsayin Babban Hafsan Tsaro da shugabannin runduna bayan ritaya.

Amma Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya ne daga cikin masu magana da yawun shugaban ƙasa, ya shaida wa BBC cewa, wannan sallama da ake magana a kan ta ba sabon abu bane domin kusan shekara guda ke nan da shugaban kasa ya amince da bayar da irin wannan hakki ga manyan hafsoshi.

Ya ce," Ba wai su kadai ake kyautatawa ba hatta kanana sojoji ma shugaban kasar ya tuna da wasu domin suma akwai tanadin da aka yi musu musamman na inshorar rai."