Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2024

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/07/2024

Taƙaitattu

  • NATO ta ce za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine don ta zama mamba
  • Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan 'yancin ƙananan hukumomi
  • Isra'ila ta umarci 'duka mazauna birnin Gaza' su fice daga birnin
  • Ƙungiyoyin ƙwadago na duba yiwuwar amsa gayyatar Tinubu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Aisha Idris

  1. Isra'ila ta umarci 'duka mazauna birnin Gaza' su fice daga birnin

    Mazauna Gaza

    Asalin hoton, ..

    Sojojin Isra'ila sun buƙaci mazauna birnin Gaza su fice daga yankin kudanci zuwa tsakiyar Zirin Gaza, yayin da suke ci gaba da kai hare-hare a arewacin yankin.

    Wasu takardu da jirgin sama ya sako cikin birnin sun buƙaci duk wanɗanda ke zama a birnin Gaza su bar wurin da suka kira 'sansanin yaƙi mai haɗari' ta hanayr bin wasu tituna biyu da suka ce masu tsaro ne da za su kai mutanen yankin zuwa garuruwan Deir al-Balah da al-Zawaida.

    Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana damuwarta kan umarnin barin birnin da aka bayar kasancewar wannan ne karo na biyu da aka ɓukaci hakan tun fara yaƙin, inda ake buƙatar kowa ya fice.

    Cikin mako biyu da suka gabata ne sojojin Isra'ila suka ƙara kunna kai cikin unguwanni da dama da suke ganin a nan ne mayaƙan Hamas da ƙungiyoyin Falasɗinawa masu ikirrain jihadi ke taruwa tun farkon shekarar nan.

    Ƙungiyar Hamas ta ce sake ƙaddamar da hare-hare a birnin na barazana ga tattaunawar sulhu da aka fara ranar Laraba a Qatar domin tsgaita wuta da kuma batun sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su.

    Shugabannin hukumomin leƙen asirin ƙasashen Amurka da Masar da kuma Isra'ila da Firaministan Qatar na daga cikin masu halartar tarun sulhun.

    Wani babban jami'in Hamas Hossam Badran ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Isra'ila "na ƙoƙarin saka matsi kan yarjejeniyar ta hanyar kai hare-hare da ɗaiɗaita Falasɗinawa tare da aikata kisan kiyashi".

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da goyon bayan Isra'ila kan cimma yarjejeniyar, matuƙar ba a saɓa wa ƙa'idojinta a.

  2. Kotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan 'yancin ƙananan hukumomi

    ..

    Asalin hoton, ..

    A yau ne Ƙotun Ƙolin Najeriya za ta yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar gabanta tana buƙatar jihohi su bai wa ƙananan hukumomin ƙasar 'yancin gashin kai.

    Tuni dai kotun da aike wa lauyoyin duka ɓangarorin da ke cikin shari'ar.

    Gwamnatin Najeriyar dai ta maka gwamnonin jahohin 36 a gaban kotu inda ta ke ƙalubalantar su yadda suke take haƙƙin ƙananan hukumomi da ya danganci zaɓe da ba su damar amfani da kuɗaɗen gudanarwarsu.

    Sai dai gwamnonin sun buƙaci kotun da ta yi watsi da wannan buƙatar da gwamnatin tarayya ta shigar.

    Gwamnatin tarayyar na kuma son kotun ƙolin ta bayar da umarnin tura wa ƙananan hukumomin kuɗinsa kai tsaye daga asusun gwamnatin tarayya, kamar yadda kundin tsari mulkin ya tanadar.

    A Najeriyar ƙananan hukumomin sun jima suna ƙorafin cewa gwamnonin jihohin ƙasar na riƙe musu kuɗaɗensu, lamarin da suka ce shi ke janyo musu rashin gudanar da ayyukan ci gaba a yankunansu.

    Masana dai sun jima suna kiraye-kirayen bai wa ƙananan hukumomin 'yancin gashin kai, kasancewa ƙananan hukumomin sun fi kusanci ga jama'a, masanan na ganin hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan ci gaba a matakin farko.

  3. NATO ta ce za ta ci gaba da tallafa wa Ukraine don ta zama mamba

    nato

    Asalin hoton, Getty Images

    A rana ta biyu na taron ƙungiyar tsaro ta NATO da ke gudana a Amurka, ƙungiya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da taimaka wa Ukraine don zama mamba a cikin ƙungiyar.

    A sanarwar hadin gwiwa da Nato ta fitar da sakatare janar mai barin gado, Jens Stoltenberg, ya karanta, ya ce za su ba da tallafin soji na dala biliyan 40 ga Ukraine a cikin shekara guda.

    An cimma yarjejeniyar ƙawancen Nato ƙarkashin jagorancin Amurka, za su taimaka wa Ukraine horas da sojinta da kai makamai.

    Mista Stoltenberg ya ƙara da cewa za su taimaka wa Ukraine da abin da ya dace domin nuna wa Mista Putin ba zai yi nasara ba.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Abdullahi Bello Diginza tare da Aisha Idris, ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin sanar da ku halin da duniya ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke kawo muku a shafukanmu na sada zumunta.