Aljeriya ta yi kira da a ƙaƙaba wa sojojin Mali da sojojin haya na Rasha takunkumi
Jakadan Aljeriya na Majalisar Dinkin Duniya, Amar Bendjama ya yi kira da a kawo karshen cin zarafi da "dakaru masu zaman kansu" suke yi, a dai dai lokacin da ake samun takun saka tsakanin ƙasar da gwamnatin mulkin sojan Mali da ke samun goyon bayan sojojin haya na kasar Rasha, kamar yadda gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito.
Sanarwar ta biyo bayan rahotannin hare-haren jiragen sama marasa matuka da aka yi zargin ya ƙashe fararen hula 20 na kasar Mali kusa da kan iyakar Aljeriya a Tinzaouatene.
Mali ta ce ta kashe wani babban kwamandan mayakan a harin.
Da yake magana yayin taron Majalisar Dinkin Duniya a ranar 26 ga watan Agusta domin bikin cika shekaru 75 da amincewa da yarjejeniyar Geneva, Bendjama ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kakaba takunkumi kan waɗanda ke da alhakin wadannan tashe-tashen hankula.
Sojojin Mali sun kai hare-hare ta sama a Tinzaouatene a ranar 25 ga watan Agusta a lokacin da suke yaƙi da kawancen 'yan tawaye daga manyan kungiyoyin Abzinawa.
Har ila yau mayakan da ke kawance da al-Qaeda na ci gaba da kai hare-hare a yankin.
An mayar da gawarwarkin fararen hulan da aka kashe zuwa Aljeriya domin yi musu jana'iza.