Real Madrid v Liverpool, Arsenal v PSG: Yadda za a fafata a zagayen farko na Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Real Madrid mai riƙe da kofin gasar zakarun Turai ta Champions za ta fafata da Liverpool a zagayen farko na gasar da aka sauya wa fasali ta 2024-25.

A maraicen ranar Alhamis ne aka raba jadawalin sabon tsarin gasar da za a fara amfani da shi a kakar wasa ta bana mai ƙungiyoyi 36.

Sauran ƙungiyoyin da Real Madrid za ta kara da su a zagayen su ne Dortmund, AC Milan, Atalanta, Salzburg, Lille, Stuttgart, Brest.

Muhimmin sauyi da kwamitin zartarwa na UEFA ya sanar shi ne ficewa daga tsarin matakin rukuni da ake yi a baya, inda a yanzu kowace ƙungiya za ta buga wasa takwas - huɗu a gida, huɗu a waje.

A baya matakin rukuni na gasar zakarun Turai ya ƙunshi ƙungiyoyi 32, da ake raba wa cikin rukuni takwas, inda kowanne rukuni ke ƙunshe da ƙungiyoyi huɗu.

Sauran wasannin da za su fi zafi a zageyn sun haɗa da wanda PSG za ta kara da ƙungiyoyin Manchester City, Bayern Munich, Atletico Madrid, Arsenal.

Yaya raba jadawalin sabon tsarin ya kasance?

A yanzu ƙungiyoyi 36 ne za su shiga gasar, mai tsarin lig ɗaya, inda duka ƙungiyoyin za su kasance a teburi ɗaya.

Domin tantance ƙungiyoyin da za su fafata da juna, da farko an rarraba su a cikin tukwane huɗu bisa matsayin kowace ƙungiya.

An yi amfani da wata manhaja da Uefa ta samar domin fitar da ƙungiyoyin da kowacce ƙungiya za ta fafata da su.

Sannan a matakin farko babu ƙungiyar da za ta fafata da abokiyar hamayyarta da suka fito daga ƙasa ɗaya. Hakan na nufin kowace ƙungiya za ta kara da ƙungiyoyi biyu daga kowace tukunya cikin huɗu.

Wasannin Man City

  • Bayern Munich (h)
  • Borussia Dortmund (a)
  • Atalanta (h)
  • Benfica (a)
  • Young Boys (h)
  • Red Star Belgrade (a)
  • Brest (h)
  • Monaco (a)

Wasannin Arsenal

  • PSG (h)
  • Inter Milan (a)
  • Shakhtar Donestsk (h)
  • Atalanta (a)
  • Dinamo Zagreb (h)
  • Sporting CP (a)
  • Monaco (h)
  • Girona (a)

Wasannin Bercelona

  • Bayern Munich (h)
  • Borussia Dortmund (a)
  • Atalanta (h)
  • Benfica (a)
  • Young Boys (h)
  • Red Star Belgrade (a)
  • Brest (h)
  • Monaco (a)

Yadda sabon tsarin gasar zai kasance

Idan aka kammala wasannin zagayen farko (kowace ƙungiya ta kara da ƙungiyoyin da aka haɗa ta da su), ƙungiyoyin za su kasance a teburi ɗaya wato daga na ɗaya zuwa na 36.

Daga nan ne kuma sai ƙungiyoyi takwas na saman teburi su tsallaka kai-tsaye zuwa zagayen 'yan 16, yayin da daga kan ƙungiya ta tara zuwa 24 za su yi wasan neman gurbi (gida da waje), don kaiwa zagayen 'yan 16.

Su kuwa waɗanda suka ƙare a matsayi na 25 zuwa 36, an fitar da su daga gasar kenan, kuma ba za su samu damar shiga gasar Europa League ba, kamar yadda ake yi a baya.

Daga kan matakin zagayen 'yan 16 kuma sai a ci gaba da yadda aka saba gudanar da ita a baya - wato a kai matakin dab da kusa da na ƙarshe, da matakin kusa da ƙarshe, har zuwa wasan ƙarshe, wanda za a yi a birnin Munich na ƙasar Jamus.

Yawan wasannin da za a fafata a sabon tsarin zai ƙaru daga 125 zuwa 189.

Kowace ƙungiya za ta yi wasa takwas mafi ƙaranci maimakon shida da ƙungiyoyin da ake fitarwa daga gasar tun a rukuni ke samun damar yi a baya.

Za a gudanar da wasan zagayen farko har zuwa ƙarshen watan Janairu, maimakon a baya da yake ƙarewa kafin bikin Kirsimeti.

Waɗanne ƙungiyoyi ne za su buga gasar a bana?

Tukunyar farko: Real Madrid (Spa), Man City (Eng), Bayern Munich (Ger), Paris St-Germain (Fra), Liverpool (Eng), Inter Milan (Ita), Dortmund (Ger), Leipzig (Ger), Barcelona (Spa)

Tukunya ta biyu: Bayer Leverkusen (Ger), Atletico Madrid (Spa), Atalanta (Ita), Juventus (Ita), Benfica (Por), Arsenal (Eng), Club Brugge (Bel), Shakhtar Donetsk (Ukr), AC Milan (Ita)

Tukunya ta uku: Feyenoord (Ned), Sporting Lisbon (Por), PSV Eindhoven (Ned), Dinamo Zagreb (Cro), Salzburg (Aus), Lille (Fra), Red Star Belgrade (Ser), Young Boys (Sui), Celtic (Sco)

Tukunya ta huɗu: Slovan Bratislava (Ska), Monaco (Fra), Sparta Prague (Cze), Aston Villa (Eng), Bologna (Ita), Girona (Spa), Stuttgart (Ger), Sturm Graz (Aus), Brest (Fra)