KAI TSAYE, Jana’izar Khamenei da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahotanni game da jana’izar Khamenei da wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/07/2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello

  1. Tarukan addini 5 mafiya girma a duniya

    Hindu

    Asalin hoton, Getty Images

    Addinai da al'adu a faɗin duniya na gudanar da taruka daban-daban, inda miliyoyin mabiya addini ko wata mazhaba ko kuma wata al'ada ke haɗuwa a wuri guda domin bikin.

    Mafiya lokuta ana irin waɗannan tarukan ne shekara-shekara wani abu da ke bai wa masu son halartar taron yin tanadi walau dai na kuɗin tafiya ko guzuri.

    A yanzu haka akwai taruka manya guda biyar da suka fi kowanne samun taron jama'a a duniya inda kuma uku daga cikinsu na mabiya addinin Musulunci ne sai kuma guda biyu na mabiya addinin Hindu da Yahudanci.

  2. Muhammad ya sake zama sunan da aka fi sanya wa jarirai a Ingila da Wales

    Jarirai

    Asalin hoton, Getty Images

    Sunan Muhammad ya sake zama sunan da mahaifa suka fi saka wa ƴaƴansu maza a Ingila da Wales a shekarar 2025.

    Hukumar ƙididdiga ta Ingila ce ta sanar da hakan a wani rahoto da ta fitar ranar Alhamis dangane da sunayen da aka fi sanya wa yara a shekarar da ta gabata.

    Wannan dai shi ne karo na uku a jere da sunan na Muhamamd ke zama wanda aka fi sanya wa yara a Ingila da Wales - sunan ne ja-gaba a shekarun 2023 da 2024 da kuma 2025.

  3. Nicaragua ta soke lasisin lauyoyi 2,000

    Lauya

    Asalin hoton, Bloomberg Creative/ Getty Images

    Hukumomi a Nicaragua sun soke lasisin lauyoyi 2,000 ba tare da bayyana dalilin yin hakan ba.

    Kafafen yaɗa labarai na Nicaragua sun ruwaito cewa an cire sunayen lauyoyin daga rajistar Kotun Koli, matakin da ya hana su ci gaba da gudanar da aikinsu na lauya.

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce wannan mataki zai rufe hanya ta ƙarshe da ta rage ga mutanen da ke neman kariyar shari'a daga gwamnatin da ake zargi da mulkin kama-karya ƙarƙashin Daniel Ortega da matarsa, Rosario Murillo.

    Ma'auratan sun shafe kusan shekara 20 suna mulkin Nicaragua da cikakken iko, tare da riƙe madafun iko

  4. Gobarar daji ta yi ajalin aƙalla mutum 12 a Spain

    Spain

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomi a kudancin Sifaniya sun ce aƙalla mutum 12 ne suka mutu sakamakon wata gobarar daji a lardin Almería.

    An samu gawar wasu daga cikin waɗanda suka mutu ne a cikin motoci da wutar ta rutsa da su.

    Wakilin BBC ya ce Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne bayan wani layin wutar lantarki ya faɗi, lamarin da yasa wutar ta bazu cikin sauri zuwa wani yanki mai cike da bishiyoyi .

    Matsanancin zafi mai maki digiri 40 na ma'aunin Celsius da ake ci gaba da samu, ya haddasa gobarar daji a sassa daban-daban na kudancin Turai.

  5. Me ya sa aka jinkirta jana'izar Khamenei duk da tanadin Musulunci na gaggauta binne mamaci?

    HAMSHAHRI

    Asalin hoton, HAMSHAHRI

    Tun ranar Juma'ar makon da ya gabata ne aka fara gudanar da tarukan jana'izar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, har zuwa ranar Alhamis, inda za a binne shi a harabar hubbaren Imam Reza da ke birnin Mashhad.

    An ajiye akwatunan gawar Khamenei da wasu mutum huɗu daga cikin iyalansa a wani wuri na musamman a Tehran a safiyar Asabar 4 ga Yulin 2026. An lulluɓe akwatunan da tutar Iran, inda aka sanya su cikin gilashi kuma makarar sun fi yadda aka saba yi tsawo.

    Mahukuntan Iran sun ce ba don dalilan tsaro kaɗai aka sanya gawarwakin cikin gilashin ba, har ma domin amfani da tsarin sanyaya yanayi da zai taimaka wajen kiyaye su.

  6. Sojojin Najeriya sun kama ƴar Chadi bisa zargin kai wa Boko Haram giya da ƙwayoyi

    Soja

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na sashi na 3 na rundunar haɗin gwiwa ta arewa maso gabas sun samu nasara kama wata ƴar ƙasar waje da uke zargi da kai wa mayaƙan Boko Haram ƙwayoyi da giya.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun sojojin Mohammed Goni ya fitar, ya ce sun yi amfani ne da bayanan sirri wajen bibiyarta, inda a ranar Alhamis 9 ga Yuli suka kamata ɗauke da tarin miyagun ƙwayoyi da giya da sauran haramtattun kayayyaki da ake kyautata zaton za ta kai wa ƴan Boko Haram ne.

    "An kama wadda ake zargin, Misis Rachael Samuel mai shekara 48, wadda ƴar garin Kelo da ke lardin Chari-Baguirmi na Jamhuriyar Chadi ce. Binciken farko ya nuna cewa tana kai kayan ne zuwa wurare da ke cikin tsibiran Tafkin Chadi, inda aka san zama mafakar 'yan ta'adda ne."

    Daga cikin ƙwayoyin da sauran kayayyakin da aka kama matar da su akwai buhu bakwai na tabar wiwi da giya da sauransu.

  7. Da gaske an daina karɓar takardar naira 100 a Najeriya?

    Naira

    Asalin hoton, CBN

    A baya-bayan nan ƴan Najeriya sun shiga ruɗani game da sahihancin takardar kuɗi ta naira 100.

    Rahotonni daga wasu yankunan ƙasar sun nuna cewa wasu a ƙasar sun daina karɓar tsohuwar takardar kuɗi ta naira 100.

    Najeriya na amfani da nau'uka biyu na takardar kuɗi ta naira 100, waɗanda duk hukumomin sun amince da su.

    Tun asali akwai takardar naira 100 da ake amfani da ita, sai dai a shekara ta 2014 babban bankin Najeriya ya fitar da wata sabuwar takardar naira 100 wadda aka yi wa sauye-sauye, a wani ɓangare na murnar cikar ƙasar shekara 100 da samuwa.

  8. Yadda aka binne tsohon jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei

    Iran

    Asalin hoton, Reuters

    Kafafen yaɗa labaran gwamnati a Iran sun ce an binne jagoran addini na ƙasar da aka kashe, Ayatollah Ali Khamenei, a hubbaren Imam Reza da ke Mashhad, wuri mafi tsarki a Iran, bayan taron jana'iza da ya jawo dubban mutane.

    An gudanar da jana'izar a Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran bayan mako guda na jerin gwanon jana'iza da tarukan alhini da kuma zaman makoki, a daidai lokacin da rikici ya sake ɓarkewa tsakanin Iran da Amurka bayan wani lokaci na tsagaita wuta a yaƙin da ya shafe wata huɗu ana yi.

  9. Amurka za ta tattauna da ministocin ƙasashe 60 kan masu tsattsauran ra'ayi

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya gayyaci ministoci daga ƙasashe sama da 60 zuwa wani taron koli da za a yi a birnin Washington, a mako mai zuwa domin tattauna abin da ma’aikatarsa ta kira ‘sake farfadowar masu tsattsauran ra'ayin kawo sauyi na kasa da kasa ’.

    Ana dai sa ran taron zai haɗa ministoci da manyan jami’ai daga yankuna daban-daban na duniya, ciki har da turai da Asiya.

    Sai dai kafafen yaɗa labarai na Amurka sun bayar da rahoton cewa abu ne mai wuya a sami shugabannin turai masu yawa a taron, saboda ba sa kallon masu matsanancin ra'ayi kawo sauyi a fagen siyasa a matsayin babbar barazana

    Masu sukar wannan mataki dai na cewa Amurka na zuzuta girman barazanar da ake dangantawa da masu matsananincin ra'ayin kawo sauyi.

  10. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Laraba.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai kan jana'izar Ali Khamenei da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.