An sauya Salisbury mai kula da VAR a wasan Liverpool da Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
An canja Michael Salisbury a matakin wanda zai kula da VAR a wasan Premier League mako na uku tsakanin Liverpool da Arsenal a Anfield ranar Lahadi.
Hakan ya biyu bayan da mahukuntan wasannin Premier League suka ce ya yi kuskure da ya hana ƙwallon da Fulham ta fara cin Chelsea ranar Asabar, wanda yana cikin masu kula da VAR.
Josh King ne ya ci ƙwallon a minti na 22 da fara tamaula, amma bayan da aka duba VAR, sai aka yanke hukuncin cewar an yi wa Rodrigo Muniz ƙeta tun kan a ci ƙwallon.
Daga baya shugaban alkalan Premier League, Howard Webb ya kira Fulham da cewar an yi kuskure da aka hana su ƙwallon da suka ci Chelsea.




