Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Labarin wasanni daga 30 zuwa 5 ga watan Satumbar 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 30 zuwa 5 ga watan Satumbar 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An sauya Salisbury mai kula da VAR a wasan Liverpool da Arsenal

    An canja Michael Salisbury a matakin wanda zai kula da VAR a wasan Premier League mako na uku tsakanin Liverpool da Arsenal a Anfield ranar Lahadi.

    Hakan ya biyu bayan da mahukuntan wasannin Premier League suka ce ya yi kuskure da ya hana ƙwallon da Fulham ta fara cin Chelsea ranar Asabar, wanda yana cikin masu kula da VAR.

    Josh King ne ya ci ƙwallon a minti na 22 da fara tamaula, amma bayan da aka duba VAR, sai aka yanke hukuncin cewar an yi wa Rodrigo Muniz ƙeta tun kan a ci ƙwallon.

    Daga baya shugaban alkalan Premier League, Howard Webb ya kira Fulham da cewar an yi kuskure da aka hana su ƙwallon da suka ci Chelsea.

  2. Ana sa ran Liverpool za ta gabatar da fan miliyan 130 don siyan dan wasa mai kai hari na Newcastle da Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, tare da Karin alawus-alawus da zai sa ya zama cinikin da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin Ingila. (Telegraph - subscription required, external)

    Manchester United ta amince ta tura Rasmus Hojlund, mai shekara 22, aro na tsawon kakar wasa zuwa Napoli, tare da wani sharadi na siyansa kan fan miliyan 38.(Athletic - subscription required, external)

    Brentford ta yi tayin kusan fan miliyan 45 kan dan wasan amus Maximilian Beier mai shekaru 22 da Borussia Dortmund ta ki amincewa da shi.(Athletic - subscription required, external)

    Dan wasan tsakiyar RB Leipzig da Austria Christoph Baumgartner, mai shekara 26, na cikin 'yan wasa da Crystal Palace ke sha'awa. (Sky Sports, external)

  3. Jackson bai ji daɗi ba da batun komawarsa Bayern Munich ya bi ruwa

    Chelsea ta sanar da Bayern Munich cewar ta soke yarjejeniyar bayar da aron Nicolas Jackson, har ta umarci ɗan wasan ya koma Jamus, bayan da ya je can don kammala ƙulla yarjejeniya.

    Wasu majiya sun sanar da BBC cewar ɗan wasan mai shekara 24 bai ji daɗin lamarin ba, bayan da aka cimma cewar zai buga wasannin aro a Bayern Munich kan fam miliyan 13 a kakar nan.

    Chelsea ta ɗauki wannan matakin bayan da Liam Delap ya ji rauni a wasan da ta ci Fulham 2-0 ranar Asabar a Premier League, wanda aka ce zai yi jinyar mako shida zuwa takwas.

    Kenan Chelsea, wadda take da ƴan wasa huɗu masu buga gurbin cin ƙwallaye saura ɗaya mai lafiya.

    Tuni Christopher Nkunku ya koma AC Milan kan fam miliyan 36 an kuma tura Jackson Jamus, domin buga wasannin aro ga Delap ya ji rauni.

    Kenan Joao Pedro ne keda lafiya, wanda ya ci ƙwallo biyar daga wasa biyar.

  4. Newcastle ta ɗauki Woltemade a matakin mafi tsada a ƙungiyar

    Newcastle United ta kammala sayen Nick Woltemade daga Stuttgart kan yarjejeniyar kaka shida.

    Ɗan wasan tawagar Jamus, mai shekara 23 ya koma Newcastle kan fam miliyan 69.

    Kenan ya zama ɗan wasan ƙungiyar da ta saya mafi tsada a tarihin Newcastle United.

    Woltemade, wanda zai saka riga mai lamba 27, ba a kammala yi masa rigista da wuri ba, kenan ba zai buga wasan da Newcastle za ta je Leeds United ba ranar Lahadi a Premier League.

  5. Labarai da dumi-dumi, Chelsea ta kammala sayen Garnacho daga Manchester United

    Chelsea ta kammala sayen ɗan wasan tawagar Argentina, Alejandro Garnacho daga Manchester United.

    Tuni ɗan wasan, mai shekara 21 ya saka hannu kan yarjejeniyar da ƙungiyar Stamford Bridge zuwa karshen kakar 2032.

    Garnacho, wanda ya ci ƙwallo 11 da bayar da 10 aka zura a raga a United a kakar da ta wuce, ya yi mata karawa 144 a dukkan fafatawa da cin ƙwallo 26.

    Ɗan wasan Argentina yana daga cikin ƴan wasa biyar da suka nemi izinin barin United har da Marcus Rashford da Antony da Tyrell Malacia da kuma Jadon Sancho.

  6. Manchester United ta kusan sayar da Hujlund ga Napoli

    Ɗan wasan Manchester United, Rasmus Hojlund na daf da komawa buga gasar Serie A a ƙungiyar Napoli.

    Tuni Hojlund, mai shekara 22 ya je Italiya ranar Asabar, domin a auna koshin lafiyarsa ranar Lahadi.

    United da Napoli sun cimma yarjejeniyar da ɗan wasan tawagar Denmark zai koma Italiya kan fam miliyan 38 da zarar an cika wasu ka'idoji.

    Ɗaya daga ciki shi ne ƙungiyar da Antonio Conte ke jan ragama ta samu gurbin shiga Champions League, wadda ta cika hakan.

    Hojlund ya ci ƙwallo huɗu a lik a United a kakar da ta wuce.

  7. Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni

    Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.

    Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.